Ko wanne irin atisaye ne ke maganin ciwon baya?

Sau da yawa idan mutum ya ce "ina fama da ciwon baya", sai ka ji wani ya ce "ba ka motsa jiki ne", ko kuma ya ce "ka riƙa motsa jiki akai-akai". To amma abin tambaya a nan shi ne: wanne irin atisaye ko motsa jiki ne ke taimaka wa mai ciwon baya? 

Lower Back Pain

Da farko dai, ya kamata mu bambance tsakanin "motsa jiki" da kuma "atisaye".

Motsa jiki na nufin duk wani yunƙuri da ya haifar da motsin jiki ko gaɓoɓi saɓanin hutu. Wato hutu shi ne lokacin da mutum ke kwance ko zaune ba tare da yana yin wani aiki ba.  Misalan motsa jiki sun haɗar da: ayyukan gida, aikin gona/lambu, tafiya, sassarfa, gudu, tuƙa keke da sauran ayyukan yau da kullum.

Amma atisaye, kamar yadda Bahaushe ya aro kalmar daga turanci, wato "exercise", sannan ya yi mata kwaskwarima zuwa "atisaye". Atisaye na nufin tsararre, aunanne, ƙayyadajje, kuma keɓaɓɓen motsa jiki domin magance wata matsala ko bunƙasa aikin wani sashin jiki ko gaɓa ko kuma bunƙasa karsashin jiki gaba ɗaya.

Saboda haka, kamar yadda nau'o'in ƙwayar magani ke da yawa, kuma kowacce ƙwaya ke da keɓaɓɓen aiki domin ciwuka daban-daban, haka ma atisaye ke da nau'o'i daban-daban kuma domin ciwukan jiki ko gaɓoɓi daban-daban. Har ila yau, nau'in atisayen mai ciwon gwiwa ba zai zama iri ɗaya da na mai ciwon baya ko wuya ba.

Bugu da ƙari, shi kansa ciwon bayan yana da sabuba daban-daban. Wani ciwon bayan ya faru ne sakamakon tsinkewa/cirar nama, targaɗe, fashewa, bulli ko zaizayewar faifan tsakankanin ƙasusuwan gadon baya, gocewa ko karayar ƙashin gadon baya da dai sauransu. To yanzu mene ne sababin ciwon bayanka?

Saboda haka, kamar yadda sabuban ciwon baya suka sha bamban, tilas ma nau'o'in atisayen da za su magance nau'o'in ciwon bayan su bambanta.

Abu mafi ban tsoro a kasadar fara atisaye ga masu ciwon baya ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba shi ne; sau da yawa, wasu ire-iren motsa jiki ko atisayen da mutane ke yi sune ke ƙara ta'azzara ciwon bayan. Ko kuma a shafe tsawon lokaci ana yi amma babu sauƙi.

Daga ƙarshe, ya zama wajibi ga duk mai wani nau'in ciwo: ciwon baya, ciwon wuya, ciwon ƙafaɗa, ko ciwon baya da ya guji fara yin duk wani irin motsa jiki ko atisaye da zimmar magance wani ciwo ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba.

Saboda kafin a samar da wani nau'in atisaye ga mai wani nau'in ciwon baya, sai an nazarci sababin ciwo, sannan a ɗora mutum a kan ƙeɓaɓɓen atisaye da shawarwarin da za su taimaka wajen sauƙaƙa ko magance ciwon.

Har wa yau, akwai kayan aiki da nau'rori na musamman da likitocin fisiyo ke amfani da su wajen rage raɗaɗin ciwon baya. Wannan hanya ce da ake magance ciwo ba tare da dogaro da shan ƙwayar maganin rage ciwo kullum ba.

Don haka, yin atisaye ko motsa jiki ga mai ciwon baya, ciwon gwiwa da sauransu, ba tare da tuntuɓar likitan fisiyo ba tamkar shan magani ne ba tare da tuntuɓar likita ba.

Physiotherapy Hausa

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post