Adadin jihohi 12 da suka ƙuri'arsu a zaben fidda gwani da ke gudana a Abuja.

 Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na da jumillar daliget 69 da su ka kaɗa ƙuri'a a zaben fidda gwani da ke gudana a Eagle Square da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

BBC


Jihar Edo na da adadin masu jefa ƙuri'a 52 da aka tantance daga 57.

Deliget daga Jihar Enugu ne daga kudu maso gabashin Najeriya sun fito sun jefa nasu ƙuri'un.

Deliget ɗin 51 ne za su zaɓa su darje.


Daliget daga Jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya su ma sun kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC mai mulki.


Deliget 73 ne cikin 75 za suka kaɗa ƙuri'u a wannan assalatun.

Masu kaɗa ƙuri'a daga Jihar Cross River da ke kudu maso kudu sun jefa ƙuri'unsu.

BBC


 Deliget 54 ne su ka yi zaɓen daga Cross River, jihar da Gwamna Ben Ayade ya fito - ɗaya daga cikin 'yan takarar.

Wakilai 90 daga Jihar Osun su ma an kirawo sun  kaɗa ƙuri'unsu.

Deliget daga Jihar Ogun ta kudu maso yammacin Najeriya sun himmatu wajen zaɓar nasu 'yan takarar a wannan zaben fidda gwani na jam'iyyar APC mai mulki.


Ogun na da daliget 60 kuma dukkansu ba su yi ƙasa a gwiwa ba a daren jiya wajen yin zaɓen. Domin kuwa tuni sun gama na zaben su.


Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na kaɗa tasu ƙuri'unsu.

Borno na da deliget 81 da aka tantance daga cikin 81 da za su ka yi zaɓe.


Daliget na Jihar Neja sun saka takalmansu don zuwa kan akwatin kaɗ ƙuri'a.

Akwai mutum 75 da aka tantance wadanda sune suka kaɗa ƙuri'a daga Jihar Neja a zaben fidda gwani da ake gudanarwa a Abuja.


Masu zaɓe daga Jihar Binuwai a yankin arewa ta tsakiyar Najeriya sun jefa ƙuri'unsu a zaɓen fid da gwani na jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Binuwai na da daliget 64 da aka tantance daga cikin 66 da za su kaɗa ƙuri'a.

Masu kaɗa ƙuri'a daga Jihar Ekiti a kudu maso yammacin Najeriya sun jefa ƙuri'ar su.

Mutane 48 da aka tantance sun fito ne daga jihar da ɗan takara Gwamna Kayode Fayemi ya fito, kodayake ya janye wa Bola Ahmed Tinubu tun kafin fara kaɗa ƙuri'ar.

'Yan takara 14 ne ke fafatawa a zaɓen don samun wanda zai yi wa APC takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Ku cigaba da bin mu domin cigaba da kawo muku halin da ake ciki

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post