Ana siyan galan na man fetur aƙalla Naira 3000 a ƙasar Amurka

 Masu motoci da ababen hawa da ke amfani da man fetur a kasar Amurka na shan baƙar wuya a faɗin ƙasar a inda suke biya dala biyar kimanin naira dubu uku domin sayan galan ɗaya na man fetur.



A wasu jihohi na ƙasar kamar irin su California, farashin ya ɗara haka.Wannan ne karon farko da irin wannan lamari ke faruwa a Amurka.

Shugaban ƙasar Amurka Joe Biden ya yi ƙoƙarin bayar da umarnin amfani da man fetur ɗin Amurka da aka tanada domin ko ta kwana don rage farashin man fetur a ƙasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar Amurka ke ƙoƙarin shawo kan matsalar tashin farashin kayayyaki a ƙasar wanda rabon da a samu irin haka kusan shekara 40 kenan.

Ƙarin farashin man fetur ya samo asali ne sakamakon rage adadin man da ake tacewa sakamakon annobar korona da kuma takunkumin da aka saka wa Rasha, wadda tana daya daga cikin manyan ƙasashen da suka fi samar da man fetur a duniya.


Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post