Orubebe ya fice daga jam’iyyar PDP yayin da Buhari zai karbe shi a APC

 Tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godsday Orubebe, ya koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, shekaru bakwai bayan da ya yi yunkurin dakile fitowar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Najeriya.



Jaridar LEADERSHIP ta samu cewa Buhari na shirin karbar Orubebe cikin jam’iyya mai mulki nan da ‘yan kwanaki masu zuwa. A ranar 31 ga Maris, 2015, Orubebe ya yi biyayya ga jam’iyyar PDP da kuma shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya kawo cikas a wurin tattara sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta gudanar a Abuja.

Ya yi hakan ne domin hana shigar da sakamakon zabe daga jihohin da suka dace da fitowar Buhari a matsayin zababben shugaban kasa. An nada Orubebe a matsayin minista mai mahimmanci a ranar 6 ga Afrilu, 2010, lokacin da Jonathan ya kafa sabuwar majalisarsa a matsayin mukaddashin shugaban kasa.


A matsayinsa na wakilin Jonathan a wurin tattara kuri’u, ya zargi shugaban Hukumar Zabe Mai zaman kanta na kasa a lokacin, Farfesa Attahiru Jega, da hada baki da babbar jam’iyyar adawa ta APC a wancan lokacin. Amma daga baya ya nemi gafarar al’ummar kasar kan halin da ya yi, inda ya kara da cewa ya yi nadamar matakin.

Sai dai kuma a wani sabon salo, Orubebe a ranar Litinin ya fice daga jam’iyyar PDP a matsayin share fage na sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki. An tattaro cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege da shugaban jam’iyyar APC na jihar Delta, Injiniya Omeni Sobotie ne suka kammala sauya shekar Orubebe.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post