Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, na ganawa da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu da gwamnoni biyar na jam’iyyar a daren ranar Alhamis.
Taron dai yana gudana ne a fadar shugaban kasa dake Abuja.
A bayanan da Jaridar LEADERSHIP ta hada yana cewa taron ba zai rasa nasaba da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da za a yi ranar Litinin mai zuwa ba.
Ku tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin a ranar Talata kafin ya tafi kasar Spain domin ziyarar aiki.
Ana kuma sa ran shugaban kasar zai gana da gwamnonin jam’iyyar APC da suka dawo daga tafiyar a ranar Juma’a domin cimma matsaya daya gabanin babban taron jam’iyyar na kasa na musamman.