Hukuncin taya Murnar Sabuwar Skekarar Muslimci.

 HUKUNCIN TAYA MURNAR SABUWAR SHEKARAR MUSULUNCI

Rubutawar: 

#Sheikh_Basheer_Lawal_Muhammad_Zaria_

27th Zhul-hijjah, 1438.H.

18th September, 2017.M.



SHIMFIDA:

Daga cikin abubuwan da daliban ilimi ke tattaunawa a akai a cikin irin wadannan lokuta da ake fuskantar shigowar sabuwar shekarar musulunci; akwai HUKUNCIN TAYA MURNA don wannan shigowa.Ya halasta ko bai halasta ba?  Bidi'a ne ko Sunnah?. 


BINCIKE:

A gaskiya a abin da na karanta wannan kusan ma'ala ce da magaba can-can ba su tattauna a kanta ba, a kabance, sai dai malamai daga baya su ne suka tattauna akanta, misali: Al-imam Assuyudi - Allah ya jikansa - ya ambace ta a cikin Risalarsa mai suna: {وصول الأماني بأصول التهاني } wacce ke cikin juzu' i na {1} a cikin littafinsa {الحاوي للفتاوي}, ga abin da ya ce:


قال القمولي في الجواهر : لم أر لأصحابنا كلاما في التهنئة بالعيدين، والأعوام، والأشهر كما يفعله الناس، ورأيت فيما نقل من فوائد الشيخ زكي الدين عبد العظيم المنذري أن الحافظ أبا الحسن المقدسي سئل عن التهنئة في أوائل الشهور، والسنين أهو بدعة أم لا ؟ فأجاب بأن الناس لم يزالوا مختلفين في ذلك، قال: والذي أراه إنه مباح ليس بسنة ولا بدعة انتهى، ونقله الغزي في شرح المنهاج ولم يزد عليه.


        الحاوي للفتاوي ج/١ ص ٨٢


MA'ANA:

Al-qamuliy ya ce : Ban ga mutanen mu {Shafi'iyya} Sun yi wata magana ba a kan taya murnar idi, ko shekaru, ko watanni; kamar yarda mutane suke yi ba, amma naga ni a cikin fa'idojin da aka cirato daga Zakiyyud-deeni Abdul'azeem Al-munzhiriy, lallai Babban malami Abul-Hasan Al-maqdisiy an tambaye shi game da taya murna a farkon shigar watanni, da shekeru, shin Sunna ne ko bidi'ah ? Sai ya bada amsa kamar haka:- 

Mutane ba su gushe suna Sabani a kan haka ba, sai dai ni ina ganin HALAS ne kawai, ba sunna ba ne ba bidi'a ba.

Haka ma Sharaf - Algazziy ya cirato a cikin sharhin littafin Al-minhaj, kuma bai kara komai a kai ba. Al-hawi  J/1 Sh:82


An ruwaito Al-imam Ahmad - Allah ya jikansa - yana cewa a game da taya murnar idi ma ba sabuwar shekara ba :

"أنا لا أبتدئ أحدا، فإن ابتدأني أحد؛ أجبته."

Ma'ana: Ni ba na fara taya wani murnar idi, amma idan wani ya fara min, to ina mayar masa.

Sai Sheikhul Islam Ibnu Taymiyya ya ce :- 

"وذلك لأن جواب التحية واجب، وأما الابتداء بالتهنئة، فليس سنة مأمورا بها، ولا هو - أيضا مما نهي عنه، فمن فعله فله قدوة، ومن تركه فله قدوة."

      مجموع الفتاوى ج/.٢٥٣ ص ٣٤

MA'ANA:

Yayi haka ne saboda maida gaisuwa tilas ne, amma fara taya murna ba sunna ce da akai umurni da ita ba, sannan kuma ba a hana yi ba, wanda ya aikata yai koyi, wanda kuma ya ki yi, shima yai koyi."


SAKAMAKO:

A karkashin haka, muna iya cewa: taya murnar shiga sabuwar shekarar musulunci, HALAS ne ba yi da alaqa da ibada, wato al'adace ta mutane su taya junansu murna ba don suna tsammanin wani lada ba.


ABABEN LURA.

1- Cewa halas ne taya murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ba ya halasta taya kafirai murnar shiga sabuwar shekararsu ta miladiyya, kamar yarda Al-imam Ibnul-Qayyim yai bayani a cikin {أحكام أهل الذمة}.


"وأما التهنئة بشعائر الكفر المختصة به فحرام باﻻتفاق، مثل أن يهنئهم بأعيادهم وصومهم، فيقول : عيد مبارك عليك، أو تهنأ بهذا العيد ونحوه ......."

MA'ANA:

Amma taya murna da abubuwan alamomin kafirci, wadanda suka ke banta da shi, to HARAMUN ne babu sabani a kan haka, kamar yace : Barka da idi, ko makamancin haka.


Ahkamu ahliz - zhimma J/1 Sh: 154.


2- Baya cikin sunna tara mutane domin bikin sabuwar shekarar musulunci, har a sauke Qur'ani, ko ai wasu addu'oi.


3- Ba kawai sabuwar shekarar musulunci ba ne abun murna, a'a mai za'a gabatar a cikinta shi ne  abun tambaya, kuma abun ai murna ko kuka.


4- Akwai banbanci tsakanin taya murnar sabuwar shekara, da daukar haka wato: Shiga sabuwar shekarar a matsayin ranar biki, da haduwa, da shagulgula.


KAMMALAWA:

Allah ya taimake mu ya sa ma rayuwarmu albarka, ya sa mu amfana da ita.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post