Ko ka san me ke jujjuya ƙwayar idonka?

 Kafin ka iya gane me ka gani ko ka hanga sai ƙwayar ido ta ɗauki hoton abin da ka gani sannan ta tura shi zuwa ƙwaƙwalwa domin ta fassara maka me ka gani. 



Kuma ƙwayar ido ita kaɗai ba za ta iya jujjuyawa gefe zuwa gefe ko sama zuwa ƙasa da kanta ba domin ɗauko hoto sai da taimakon wasu tsokoki guda shida (6).

Waɗannan tsokoki shida sune ke riƙe da ƙwayar ido a cikin gurbin / kwarmin ido kuma sune ke jujjuya ƙwayar idon yayin da kake ƙoƙarin gani ko hangen wani abu.

Haka nan, waɗannan tsokoki na karɓar umarni ne daga jijiyar maganaɗisu ta 3, 4, da 6. Waɗannan jijiyoyin maganaɗisu sun samo asali ne yayin da ƙwaƙwalwa ta fitar da rassan jijiyoyi 12 da ke bai wa sassan kai umarni.

Matsaloli ga waɗannan tsokoki ko jijiyoyi zai haifar da matsalolin gani kamar: hararagarke, gani biyu-biyu, faɗowar murfin ido da sauransu.

Irin matsalolin da ke haddasa hakan sun haɗa da: rauni ga jijiyoyi ko tsokokin sakamakon bugu ko haɗuran ababen hawa, danne ko shaƙe ɗaya daga cikin jijiyoyin saboda bullin jijiyar jini a cikin ƙoƙon kai, ciwon siga, hawan jini, daji/kansar ƙwaƙwalwa, matsalolin da kan biyo bayan tiyatar ƙwaƙwalwa da dai sauransu.


Source: Physiotherapy Hausa

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post