Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya zata shiga yajin aikin hadin gwuwa don tallafawa ASUU.

 Kungiyar ma’aikatan lafiya da lafiya ta Najeriya MHWUN ta ce za ta shiga yajin aikin hadin gwiwa domin tallafawa kungiyar malaman jami’o’i ASUU da sauran kungiyoyin kwadago.



 Shugaban kungiyar na kasa Mista Biobelemoye Josiah ya fitar da wannansanarwar  barazanar a cikin wata sanarwa, tare da sanya hannu da mukaddashin babban sakataren kungiyar, Auwalu Kiyawa.

Josiah ya ce, shugabannin kungiyar sun yi tir da kakkausar murya kan halin ko in kula da gwamnati ke nunawa wajen warware batutuwan da ake takaddama a kai.

Ya ce domin kare makomar matasan da rayuwarsu ta tabarbare a fannin ilimi, akwai bukatar gwamnati ta gaggauta aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da kungiyoyin ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kakkausar murya game da matsalar rashin tsaro da tashin farashin kayayyaki da kuma karancin man fetur da iskar gas a kasar.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post