Matasa dai sune kashin bayan ko wacce al'umma ko kuma goben al'umma, a karamar hukumar Lere an bar matasa a baya sakamakon rashin wutar lantarki da karamar hukumar ke fama dashi, a dalilin haka ne muka ne mi jin ta baking Shugaban Matasan Karamar Hukumar Lere, Kwamared Mubarak Ibrahim dangane da hakan.



Mubarak ya bayyana mana cewa, "Gaskiya matasa sun samu koma baya sakamakon rashin wutan lantarki na wannan yanki na Karamar Hukumar Lere ya fuskan ta na tsawon lokaci."

 Ya kara da cewa "Tabbas an bar matasa a baya ai bama kamar yanda ka fada ba kusan duk wata sana'a yanzu tana tafiya ne karqashin matasa, koda ace Dattijai ne masu Gidan su a wajen wannan sana'ar, yanzu Allah ya kawo mu zamanin da kusan komai baya yiwuwa yanda akeso sai da sinadarin wutan lantarki 80% na Kasuwanci da akeyi a halin yanzu, kaga kuwa rashin wutan lantarki ya illata tattalin arzikin matasa, abinda zaka yishi akan kudin da be wuce #10 ba yanzu ya kai #20, misali kafin samun matsalar wutan lantarkin masu cajin waya sukan karbi #20 ne, amma yanzu sai ka biya #50 wani lokaci yana fin haka, kuma hanyoyin samun kudin kullun karanci suke karayi" 


Yayi mana Karin haske kan matakin da ake ciki kan gyaran wutar lantarkin "gaskiya kamar yanda kowa ya sani wannan aiki ne na gwamnati, kuma amatsayi na na shugaban matasa ina iyaka bakin koqari na wajen ganin na matsa ma gwamnati lamba akan wannan aiki, kuma nasan irin koqarin da sukeyi a halin yanzu dan ganin wannan aiki ya kammala."


Ya kuma shawarci matasa da su mallaki katin zabe ga wadanda basu dashi, "Zanyi amfani da wannan dama domin kira ga matasa wanda basu da katin zabe suyi koqari su mallaki katin zaben su, domin sai da wannan katin zaku iya canza duk wani shugaba da yayi muku ba daidai ba, ko kuke ganin be taka rawar gani akan kujeran da yake kaiba, idan baka da katin zabe babu abinda zaka iyayi baka da yanci, aikin ka kawai shine hayaniya, dan haka muyi koqari mu mallaki katin zabe. 

"Ina kira ga matasa wanda basu da sana'a suyi koqari wajen neman sana'a komai qanqantar ta domin dogaro dakai, domin rashin Aiki/Sana'a shi yake sa a zama karen farauta, wanda za'a rika amafani daku ana baku 1000 daya kuna bata kaykkawar alakar ku da abokan ku, wanda kuka taso tun kuruciya"

"Ina kira ga gwamnati gyaran wutan lantarki yana daya daga cikin koqarin da zakuyi wajen gyara shi, tare da inganta shi, shine ze baku damar saukaka ma Matasa damar samun matsakaita, da manyan hanyoyin samun abin dogaro dakai lura da cewa kaso 80% na hanyoyin inganta Rayuwar kowace al'uma a Duniya da Gwamnati take bi shine inganta Wutan lantarki.


Kuyi comment da shawarwarin ku ta yadda rayuwar matasa zai inganta..