Azumin Tasu'a da Ashura - Aliyu Bello Jushi


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Allah madaukakin Sarki ya sawwake mana hanyoyin kankaran zunabbai da samun Aljanna cikin sauki. Lokaci bayan lokaci, musulmai kan ci karaba da wasu aiyukan da za su aikata domin kara kusantar Allah da samun ribar duniya da lahira. 

Ranakun Lahadi da Litinin din nan masu zuwa, 7 da 8 ga watan Agustan wannan shekarar ne suka dace da ranakun Tasua da Ashura. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar mana da cewa yin wannan azumin na kankare zunubin shekara guda.

Wannan azumi ya samo asali ne lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo Madina, sai ya tarar da Yahudawa suna azumin ranar Ashura. Ko da ya tambayesu dalilin hakam sai suka bashi amsa da cewa: lallai shi ne yinin da Allah ya tseratar da Annabi Musa -Alaihis Salam- da mutanensa daga Firauna kuma ya nutsar da rundunarsa a cikinsa, a dalilin haka Annabi Musa ya kasance yana azumtarsa domin godiya ga Allah. Sai Manzon Allah ya azumcesa kuma yayi umurni da a azumcesa. Inda yake cewa: kun fisu cancanta (da koyi) da Musa, don haka ku azumceshi. 

Wani abun lura shine, a lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama- ya yi umarni da azumtar Ashura, ba ya yi umurni da koyi da Yahudawa ba ne, sai dai a yi koyi da annabi Musa  Alaihis Salam, saboda shine ya fara yinsa kafin yahudawan su fara.  Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ni ne mafi cancantar Musa fiye da ku, sai ya azumci wannan rana kuma ya yi umarni da azumtarsa”.

Ko da cewa Manzon Allah ya Azumci Tasua ne kadai amma ya yi burin idan Allah ya kai shi shekara mai zuwa zai azumci Ashura domin sabawa yahudawa, amma sai Allah ya karbi rayuwarsa kafin lokacin. 

Wannan ya nuna cewa azumtar kwanakin biyu sunnar Manzon Allah ce mai matukar muhimmanci.

Allah ya bamu ikon cin moriyar wannan falala ta azumtar Tasua da Ashura na wannan shekara a ranakun din nan masu zuwa, 7 da 8 ga watan Agustan 2022.



Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post