Sunnonin Manzon Allah (ﷺ) yayin Kwanciya Bacci

Sunnonin Manzon Allah (ﷺ) yayin Kwanciya Bacci

Sunnonin Annabi Kafin Kwanciya Bacci Wasu Ayyuka ne da Yake Aikatawa Kafin Ya Kwanta Bacci. Waɗannan Abubuwan Kodai Na Aiki ne Ko Kuma Na Furuci Kamar Azkar da Makamantansu.


Sunnonin Da Suka Tabbata a Hadisai Ingantattu Waɗanda Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Ya Dawwama Yana Aikatasu Yayin Kwanciya Bacci Sun Haɗa Da:


1. KWANCIYA BACCI DA ALWALA: Sunnah Ta Farko da Manzon Allah (ﷺ) Ya Kasance Yayin Kwanciya Bacci Shine Yin Alwala. Ya Kasance Baya Kwanciya Bacci Ba Tare da Alwala ba. Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah (ﷺ) Yace da Barra'u bn Ãzib:


فقد قـال النبي صلى الله عليه وسلم للبراء بن عازب رضي الله عنه: (إذا أتيت مضجعك ، فتوضأ وضوءك للصلاة ، .....)

[البخاري: ٦٣١١]


Haƙiƙa Annabi (ﷺ) Yace Da Barra'u bn Azib (ra): “Idan Zaka Tafi Makwancinka, To Kayi Alwala Irin Alwalar da Kakeyi Idan Zakayi Sallah,.......”.

(Bukhari: 6311)


2. KAKKAƁE SHIMFIƊA: Abu Na Biyu Shine Share Shimfiɗa Koda Kuwa Bakaga Ƙura Akanta ba. Annabi (ﷺ) Yana Cewa:


(إذا أوى أحدكم إلى فراشه فلينفض فراشه … فإنه لا يعلم ما خلفه بعده … )

(رواه البخاري ومسلم)


“Idan Ɗayanku Yazo Ga Shimfiɗarsa, To kakkaɓe Shimfiɗarsa. Domin Besan Abinda Ya Hau Kanta a Bayansa ba”.

(Bukhari da Muslim)


3. KWANCIYA TA GEFEN DAMA: Yayin da Mutum Zai Kwanta, Saiya Kwanta ta Gefen Jikinsa Na Dama. Saboda Faɗar Annabi (ﷺ):


(ثم اضطجع على شقك الأيمن … ) 

[رواه مسلم]


Annabi (ﷺ) Yana Cewa: “...... Sannan Ka Kwanta ta Gefen Jikinka Na Dama.....”.

(Muslim Ya Ruwaitoshi)


4. SANYA TAFIN HANNUNSA NA DAMA A ƘARƘASHIN KUMATUNSA NA DAMA: Annabi (ﷺ) Ya Kasance Yana Sanya Tafin Hannunsa Na Dama Ƙasan Kumatunsa Na Dama Yayin da Zai Fara Bacci.


( كـان النبي ﷺ إذا رقـد وضع يده اليمنى تحت خـده) 

[رواه أبو داود]


“Annabi (ﷺ) Ya Kasance Idan Ya Kwanta Bacci Yana Sanya Tafin Hannunsa Na Dama a Ƙasan Kuncinsa Na Dama”.

(Abu-Daud Ya Ruwaitoshi)


5. KARANTA SURATUL KAFIRIN:


عن فروة بن نوفل عن أبيه أن النبي صلى الله عليه وسلم قال لنوفل: (اقرأ ”قُلْ يَا أَيُّهَا الْكَافِرُونَ“ ثم نم على خاتمتها، فإنها براءة من الشرك)

[أبو داود: ٥٠٥٥]


An Karɓo Daga Farwah bn Naufal (ra) Daga Babansa Yace: Lallai Annabi (ﷺ) Yace da Naufal: “Ka Karanta (ƘUL YA AYYUHAL KAFIRUN), Sannan Kayi Bacci A Ƙarshenta; Domin Bara'ace Daga Shirka”.

(Abu-Daud: 5055)


6. KARANTA ƘUL HUWALLAHU, FALAQI DA NASI: Bayan Karanta Suratul Kafirun Kuma, Ya Kasance Yana Karanta Suratul Ikhlas, Suratul Falaq da Kuma Suratun Nas:


عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها، (أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ إِذَا أَوَى إِلَى فِرَاشِهِ كُلَّ لَيْلَةٍ جَمَعَ كَفَّيْهِ ، ثُمَّ نَفَثَ فِيهِمَا فَقَرَأَ فِيهِمَا : قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ وَقُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الفَلَقِ وَقُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ، ثُمَّ يَمْسَحُ بِهِمَا مَا اسْتَطَاعَ مِنْ جَسَدِهِ ، يَبْدَأُ بِهِمَا عَلَى رَأْسِهِ وَوَجْهِهِ وَمَا أَقْبَلَ مِنْ جَسَدِهِ يَفْعَلُ ذَلِكَ ثَلاَثَ مَرَّاتٍ)

[البخاري: ٥٠١٧]


An Karɓo Daga Aisha (ra), “Lallai Annabi (ﷺ) Ya Kasance Idan Ya Iso Shimfiɗarsa Kowane Dare Yana Haɗa Tafukan Hannunsa, Sannan Ya Karanta (ƘUL HUWALLAHU AHAD, ƘUL A'UZU BI RABBIL FALAQ DA ƘUL A'UZU BI RABBIN NAS) Sai Ya Tofa A Tafukan Hannunsa Sannan Ya Shafa A Inda Ya Samu a Jikinsa. Yana Fara Shafan Kansa da  Fuskarsa Dasu da Sauran Jikinsa Har Sau Uku”.

(Bukhari: 5017)


7. KARANTA AYATUL KURSIYYU:


عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ ، قَالَ: وَكَّلَنِي رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِحِفْظِ زَكَاةِ رَمَضَانَ فَأَتَانِي آتٍ فَجَعَلَ يَحْثُو مِنَ الطَّعَامِ فَأَخَذْتُهُ ، فَقُلْتُ لَأَرْفَعَنَّكَ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - فَذَكَرَ الحَدِيثَ - ، فَقَالَ : إِذَا أَوَيْتَ إِلَى فِرَاشِكَ فَاقْرَأْ آيَةَ الكُرْسِيِّ ، لَنْ يَزَالَ عَلَيْكَ مِنَ اللَّهِ حَافِظٌ ، وَلاَ يَقْرَبُكَ شَيْطَانٌ حَتَّى تُصْبِحَ ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : (صَدَقَكَ وَهُوَ كَذُوبٌ ذَاكَ شَيْطَانٌ)

[البخاري: ٣٢٧٥]


An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Ya Wakiltani Tsare Zakkar Ramadan, Sai Wani Mai Zuwa Yazomin Yana Ƙoƙarin Satan Abinci Sai Na Kamashi. Nace Sai Nakaika Wurin Manzon Allah (ﷺ)........ Sai Yace Dani: “Idan Ka Isa Shimfiɗarka, Ka Karanta AYATUL KURSIYYU, Wani tsaro Daga Allah Bazai Gushe Tare Dakai ba, Kuma Shaiɗan Bazai Iya Kusantarka ba Har Gari Ya Waye. Sai Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Gaskiya Ya Faɗi Maka Amma Maƙaryaci Ne”.

(Bukhari: 3270)


8. KARANTA AYOYIN BIYUN ƘARSHEN SURATUL BAQARA:


 عَنْ أَبِي مَسْعُودٍ البَدْرِيِّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: (الآيَتَانِ مِنْ آخِرِ سُورَةِ البَقَرَةِ ، مَنْ قَرَأَهُمَا فِي لَيْلَةٍ كَفَتَاهُ)

[ومسلم: ٨٠٧]


An Karɓo Daga Abi-Mas'ud Al-Badary (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Ayoyi Biyun Ƙarshen Suratul Baƙara, Duk Wanda Ya Karantasu Cikin Dare, Sun Isan Masa”.

(Muslim: 807)


9. YIN ADDU'A YAYIN DA YA FARKA CIKIN DARE: Annabi Ya Kasance Yanayin Addu'a Yayin da Ya Farka Cikin Bacci:


 عن عبادة بن الصامت رضي الله عنه، عن النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قال: (من تعارَّ من الليل فقال: لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شيء قدير، الحمد لله، وسبحان الله، والله أكبر، ولا حول ولا قوة إلا بالله، ثم قال: اللهم اغفر لي، أو دعا، استُجيب له، فإنْ توضأ وصلى قُبِلت صلاته)

[البخاري: ١١٥٤]


An Karɓo Daga Ubadah bn Thamit (ra) Yace: Manzon Allah (ﷺ) Yace: “Duk Wanda Ya Farka Cikin Dare Yace: (LA'ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKALAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU, WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR, ALHAMDULILLAH, WA SUBHANALLAH, WALLAHU AKBAR, WA LA HAULA WALA QUWWATA ILLAH BILLAH), Sannan Yace: (ALLAHUMMAG FIRLI), Ko Yayi Wata Addu'a, Za'a Amsa Masa. Idan Yayi Alwala Yayi Sallah, Za'a Amshi Sallarsa”.

(Bukhari: 1154)


10. ADDU'A BAYAN YA TASHI DAGA BACCI:


عن حذيفة بن اليمان رضي الله عنه، قال: أن النبي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كان يقول إذا استيقظي من النوم: (الحمد لله الذي أحيانا بعدما أماتنا، وإليه النشور)

[البخاري: ٦٣١٢] 


An Karɓo Daga Huzaifah bn Yaman (ra) Yace: Lallai Annabi (ﷺ) Ya Kasance Idan Ya Tashi Daga Bacci Yana Faɗin: “ALHAMDULILLÃHIL LAZI AHYÃNÃ, BA'ADA MÃ AMÃTANÃ, WA ILAIHIN NUSHUR”.

(Bukhari: 6312)


ALLAH KA BAMU IKON KOYI DA ANNABIN MU A CIKIN DUKKAN RAYUWAR MU


✍🏽Abu Aysha Al-Maliky

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post