Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari makarantar kididdiga ta tarayya da ke Manchok, karamar hukumar Kaura a Kaduna a daren Talata 2 ga watan Agusta da misalin karfe 9:00 na dare.
‘Yan bindigar sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da mutane biyu; ciki har da shugaban makarantar.
Harin dai ya zo ne makonni uku kacal bayan an kashe wasu ma’aikatan wucin gadi biyu da ke kula da raba gidajen sauro a hanyar Zangang zuwa Zankan a karamar hukumar.
Tags
SECURITY