Hukuncin Sallah Da Qafafuwa Waje Ga Mace

Hukuncin Sallah Da Qafafuwa Waje Ga Mace

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

:

Assalamu aAaikum

Malam barka da yau Allah ya qara rufa asiri. Malam shin menene hukuncin sallah da qafafuwa waje ga mace, inajin malamai na cewa babu banbanci ga sallar macce da ta namiji da Manzon Allah (S A W) yace kuyi sallah kamar yanda kukaga inayi, ban saniba ko nayi kuskure toh naga maza basa rufe qafafuwan su, don Allah malam ina son sanin hukuncin sallah da safa shin dole ne ko mustahabbi?? Nagode

:

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

:

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،

An shar'anta wa mace baliga wacce ba baiwa ba, ta rufe jikin ta baki dayan sa idan zatayi sallah, sai fuskar ta da tafukan hannayen ta ne kadai bazata rufe ba. Saboda ita mace 'ya gaba dayanta al'aurah ce.

Idan tayi sallah alhali bata rufe wani sashen jikinta ba kamar qwaurin ta ko kafarta ko dukan su ko kuma wani sashen kanta a bude, toh sallar ta bata yi ba. *Manzon Allah ﷺ  Yace:

"لا يقبل الله صلاة حائض إلا بخمار"  رواه أحمد وأهل السنن إلا النسائي بإسناد صحيح.

"Allah baya karbar sallar mace wacce ta fara al'ada har saida khimaar (mayafin rufe kai)"

Ahmad da Abu Dawud da Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito shi da isnaadi ingantacce.

و لما روى أبو داود عن أم سلمة عن النبي صلى الله عليه و سلم أنها سألت النبي عن المرأة تصلي في درع و خمار بغير إزار فقال: " المرأة عورة"

Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallah anha) cewa ta tambayi Manzon Allah ﷺ gameda matar da tayi sallah tana sanye da dir'a (kamar riga) da khimaar (mayafin rufe kai) amma bata sanya Izaar (kamar wando na mata mai rufe tafukan kafar su) ba? Sai Manzon Allah ﷺ  Yace "Ita Mace Al'aurah ce"

Amma ita fuskar mace, abinda yake sunnah shine baza'a rufe ta ba a lokacin yin sallah matuqar babu maza wadanda ba muharraman ta ba a gurin.

Mafiya yawan malamai sunce wajibi ne a rufe tafukan kafa, wasu malaman kuma sunce ba wajibi bane rufe su, amma dai mafiya yawan malamai sun tafi akan wajibcin rufe kafafu gaba dayan su a yayin sallah.

Abu Dawuda ya ruwaito daga Ummu Salamah (radiyallahu anha) cewa an tambaye ta akan matar da tayi sallah tana sanye da khimaar (mayafin rufe kai ko kuma karamin hijabin da bai wuce kwankwaso ba) da kuma qamees (Riga)? Sai Ummu Salamah tace: babu laifi a hakan idan dir'a (wando ko doguwar riga) din nata ya rufe tafukan kafafun ta. 

Amma yafi kyau a kowane irin yanayi ta rufe tafukan kafafun ta domin tsallake siradin kokwanto. Saboda haka idan mace zata yi sallah ta sanya safa (socks) yin hakan yafi dacewa.

والله أعلم،

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa Da Tunatarwa a Sunnah. 

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BD0aB20SWTB9hgHahFHb9M


ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post