Kukan jariri da zarar an haife shi muhimmin abin sauraro ne ga uwa, ungozoma da dangi. Kuka yana nuna cewa jariri a raye ya zo duniya. Kuma hatta a lamarin rabon gado kukan jariri abin lura ne.
Sai dai, gaza yin kuka ko kuma jinkirin kukan jariri zuwa wasu 'yan mintina na nuni da cewa jariri bai fara numfashi nan-take ba bayan haihuwa. Saboda ba a kuka sai da numfashi. A taƙaice, kukan farko na jariri na nufin numfashin farko.
Idan aka lura jariri bai yi kuka ba bayan haihuwa, ungozoma ko likita na amfani da ƙwarewa domin yi wa jariri ƙaimin numfashi domin ceto rayuwa da lafiyarsa.
Ana nasarar ceto dubban jarirai daga wannan matsala, a yayin da wasu kuma ke mutuwa.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, ƙiyasin jarirai 900,000 ke mutuwa duk shekara sanadiyar gaza fara numfashi bayan haihuwa. Kuma matsalar na daga cikin matsalolin da ke lashe rayukan jarirai kai tsaye.
A lokacin da jariri yake cikin uwa, yana karɓar iskar oksijin da sauran sinadaran abinci ta jijiyoyin cibiya. Ana sa ran jariri ya koma shaƙar oksijin da kansa ta hanyar numfashi da zarar ya faɗo duniya.
Saboda haka, gaza fara numfashi ga jariri bayan haihuwa na nufi da rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa. Rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa kuwa na da haɗarin gaske. Domin yana haifar da mummunan lahani ga ƙwaƙwalwa wace ke sarrafa sassan jiki.
Wasu sabuban da ke hana jariri fara numfashi na faruwa ne tun a cikin uwa, inda wasu kuma ke faruwa yayin naƙuɗa ko haihuwa.
Daga cikin sabuban da ke iya janyo gazawa ko jinkirin fara numfashi ga jariri sun haɗa da:
1. Matsalolin jijiyoyin cibiya: Cibiya na iya fuskantar ƙullewa, shaƙewa ko kuma dannewa. Hakan kuma na nufi da katsewar oksijin ga jariri.
2. Girman kan jariri: Idan girman kan jariri ya wuce faɗin mafitar ƙugun uwa, to ana iya samun tangarɗar naƙuda.
3. Juyewar kwanciyar jariri a ciki: Haɗarin samun tangarɗar naƙuda na ƙaruwa da juyewar kwanciyar jariri.
4. Mummunar zuba ko ɓallewa jini kafin ko yayin naƙuda.
5. Toshewar hanyoyin numfashi, ko dai saboda tawayar halitta ko kuma shaƙar ruwan mahaifa.
6. Fashewa ko ɓallewar mahaifa.
7. Matsananciyar ƙamfar jini, da dai sauransu.
To ko mece ce makomar ƙwaƙwalwar jaririn da ya gaza yin kuka bayan haihuwa?
Kamar yadda aka ambata a baya cewa rashin oksijin ga ƙwaƙwalwa mummunan lahani ne. Saboda haka, tsawon lokacin da aka ɗauka jariri bai yi kuka ba, wato shi ne gwargwadon tsananin lahanin da ake zaton ya faru ga ƙwaƙwalwa.
Idan hakan ta faru, jariri na gamuwa da "shanyewar ƙwaƙwalwa", wato "cerebral palsy" a yaren likita, larura ce da ke shafar dukan sassan jiki. Daga cikin inda ta fi shafa akwai gangan jiki.
Jaririn da ya gamu da "shanyewar ƙwaƙwalwa" yana fuskantar jinkirin matakan girma. Misali, idan lafiyayyen jariri zai iya riƙe wuya a wata uku zuwa huɗun farko, to jariri mai "shanyewar ƙwaƙwalwa" zai yi jinkirin watanni kafin ya cimma wannan matakin girma.
Daga ƙarshe, jariran da suka gamu da "shanyewar ƙwaƙwalwa" sanadiyar gaza kuka bayan haihuwa na fuskantar barazanar nakasa idan ba a ɗauki matakan da suka kamata tun da wuri ba.
Daga cikin matakan akwai ganin likitan fisiyo domin kiyaye nakasar sassan jiki da kuma bunƙasa aikin sassan jiki domin su cimma matakan girma kamar riƙe wuya, zama, tsaiwa da tafiya.
📝 Physiotherapy Hausa