Masana Sun Gargaɗi Gwamnatin Tarayyar Najeriya Kan Daina Karɓo Bashi

Masana Sun Gargaɗi Gwamnatin Tarayyar Najeriya Kan Daina Karɓo Bashi

By: Sami Musa Daitu

Yayin da bashi ya kai N41.6tr, masana tattalin arziki sun ja kunnen Gwamnatin Tarayyar, yayin da ta ke shirin sake karɓar bashi na shekarar 2023. 

Masanan sun gargaɗi Gwamnati da ta daina karɓar rance, kamar yadda Darakta-Janar na ofishin kula da basussuka (DMO), Misis Patience Oniha, a jiya, ta tabbatar da cewa ma’aikatar ta Najeriya ta kasance a watan Maris na 2022 a kan bashi na Naira Tiriliyan 41.60.

Oniha, ta bayyana takaicin ta kan yadda ƙasar ke tafiyar da giɓin kasafin kuɗi tsawon shekaru tare da ƙara yawan rance, musamman tun bayan ɓarkewar annobar COVID-19, in da ta jaddada cewa, mafita ɗaya tilo daga matsalar ita ce inganta samar da kuɗaɗen shiga.

Ko da yake, Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta caccaki Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) a kan ikirarin da kamfanin ke yi na biliyoyin Naira da ake kashewa kan tallafin man fetur duk shekara.

Idan ba a manta ba, Ministar Kuɗi, da Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare ta Ƙasa, Zainab Ahmed, ta gabata a gaban ƴan majalisa a ranar Talata, in da ta bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta ciyo bashin sama da Naira Tiriliyan 11 tare da sayar da kadarorin ƙasa don samar da kuɗaɗen shiga.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post