By Sani Musa Daitu
A ranar 28/08/2022 ne shugabannin kungiyoyin yan kasuwar jahar yobe na kananan hukumomin 17 dake Jihar suka ziyarci gwamnan a ofishinsa dake birnin Damaturu.
Ziyarar ta gudana ne karkashin jagorancin Alh Mu'azu state Chairman tareda jagorancin Alh Nasiru Mato Algon Chairman na kananun hukumomi 17 dake jahar kuma Shugaban yan kasuwar birnin potiskum.
Inda sukayi tattaunawa na musamman tareda kira ga gwamnaty akan ninka tallafin da takeyiwa yan kasuwa da kasuwanci a jahar yobe.
Alhaji Nasiru Mato ya nuna jindadinsa na musamman bisa dama tareda abubbuwan cigaba da gwamnatyn nan take bawa yan kasuwa, inda yayi ƙira ga gwamnaty da ta cigaba da karfafawa yan kasuwa gwuiwa a jahar.
Mai Girma Gwamna jahar yobe hon. Mai Mala Buni yaji dadin karramawar da yan kasuwar suka masa inda daga karshe yayiwa yan kasuwan godiya tareda alkawarin damawa dasu a dukkan harkokin gwamnaty ninkin wamda akeyi a baya.