Majalisar Tuntuba da Hadaka ta Arewa ta yi Allah wadai da Matsayar Kungiyar Dattawan Arewa

Majalisar Tuntuba da Hadaka ta Arewa ta yi Allah wadai da Matsayar Kungiyar Dattawan Arewa

Majalisar Tuntuɓa da Haɗaka ta Arewa (ACSC) ta yi Alawadai da matakin da Ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya suka yi na cewa, har yanzu ba su goyon bayan wani ɗantakarar shugaban ƙasa daga Arewa.

Shugaban Majalisar Tuntuɓa da Haɗaka ta Arewa Injiniya Harisu Jibrin ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kaduna.

Shugaban ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu tsiraru suke yanke hukunci gaba-gaɗi ba tare da jin ra’ayoyin sauran jama’a ba.

A cewar sa, “Ƴan takara ne ya kamata su zo su bayyana wa al’umma ƙudirorin su ba wai a gayyace su domin su faɗi ra’ayoyin sa ba, wadda ko yaushe abin da suke cewa ke nan. Kuma har yau ba ta sauyi zani ba ga yankin Arewa duba da yadda yankin ya zama koma baya idan an kwatanta da sauran yankuna a tarayyar Najeriya.”

Har ila yau, Shugaban ya ce, kamata ya yi ƙungiyar ta ji ra’ayoyin al’ummar Arewa kafin su yanke hukuncin kamar yadda sauran ƙungiyoyi ke yi, ba wai kawai a ɗaura ra’ayin wasu ba, wanda ya bayyana hakan kamar ana masu kama karya, in da ya bayyana cewa hakan ba za ta sake faruwa ba domin ba za su lamunta ba.

Daga karshe! injiniya Haris ya yi kira ga al’ummar Arewa da su yi watsi da iƙirarin da wancan ƙungiya ke yi domin kuwa babban kuskure ne a cewarsa.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post