Muna Kira ga Magadanmu su Ninka Kokarin Su Akan Namu - Tsohon Shugaban NAZAS, Ahmad Aliyu Awai.

Muna Kira ga Magadanmu su Ninka Kokarin Su Akan Namu - Tsohon Shugaban NAZAS, Ahmad Aliyu Awai.

Jawabin Manema Labarai

28/10/2022


Assalam Alaikum 


MUNA MIƘA GODIYA GA ALLAH, KUMA MUNA KIRA GA MAGADAN MU SU NUNKA ƘOƘARIN SU AKAN NAMU - TSOHON SHUGABAN NAZAS, AHMAD ALIYU AWAI .  


A matsayina na Tsohon Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Na Lardin Zazzau (NATIONAL ASSOCIATION OF ZAZZAU STUDENT NAZAS) wadda keda ƙananan hukumomi Sha ɗaya na Jihar Kaduna, Haƙiƙa yau mun bar ofishin mu inda wa'adin mu ya ƙare wannan babbar nasara ce agaremu muna roƙon duk wanda muka ɓata masa rai a tsawon wa'adin da mukayi su yafe mana muma mun yafe wa kowa, Haƙiƙa mulki nauyi ne babba munga jarabawa kuma mun koyi darasin rayuwa, muna fatan hakan zai buɗe mana sabon babi na ci gaban rayuwa,da shiga duniyar Ilimi. Domin "Ilimi shine fitilar rayuwa"


SAƘON MU GA MAGADAN MU

Muna kira ga wadda suka gaje mu su tabbata sunyi ƙoƙari wajen shafe kura-kuran mu da inda muka gaza su kawo sabon Tsari mai ɗorewa wadda zai kawo cigaba ga ɗaliban Lardin Zazzau, wannan damace agareku daku kyautatawa rayuwar Ɗalibai masu tasowa, kada kuyi kwaɗayi kada ku ci mutuncin kowa kuyi aiki tuƙuru don ɗaga Darajar Masarautar Zazzau da Al'ummar Jihar Kaduna da Najeriya, kusani Ilimi shine gatan kowa kuma da Ilimi ne ake samun Ƴanci da sanin Yakamata, mu Tarbiyyantar da kanmu kyawawan halaye da girmama nagaba da tausayin na ƙasa, damace kuka samu a lokacin wa'adin ku, kusani mulke yanada wa'adi lokaci baya jira muyi amfani da damar mu kafin ta kurce mana. Zaɓen 2023 yana tafe wajibi kuwayar kan ɗaliban lardin Zazzau su tabbata sun zaɓi shugaba mai manufa aƙida da sanin Yakamata wadda zai kare mutuncin Ilimi da gina rayuwar matasa da Samar da ayyukan yi da inganta tattalin arziki a ƙasa. 


GODIYA 

Muna miƙawa Allah godiya bisa damar da ya bamu na kammala wa'adin mu na shugabancin Ɗalibai na lardin Zazzau (NAZAS) , bayan haka muna miƙa godiyar ga Masarautar Zazzau bisa gudunmowar su da goyon baya da suka nuna mana a tsawon lokacin wa'adin mu. Godiya ta musamman ga Mai Martaba Alhaji Ambasa Ahmad Nuhu Bamali Sarkin Zazzau haƙi mun sami nasarori ɗinbi saboda goyon bayan da kuka bamu a tsawon lokacin wa'adin mu. 

Bayan haka muna miƙa godiya ga majalisar zartarwa ta NAZAS da Majalisar Dokokin NAZAS da iyayen ƙungiyar Ƴan Jaridu da Tsofaffin Shugawagabannin Ƙungiyar. 

Godiya ta musamman ga:

Injiniya Musa Muhammad 

Mal. Ahmad Maiyaƙi 

Mal. Umar Yahaya 

Kwamared Usman Hayatu Mazadu

Da sauran wanda sauran wadda bamu ambata ba Allah yasaka wa kowa da Alheri. 


NASARORI DA ƘALUBALE

Haƙiƙa kowace nasara tana tare da ƙalubale wannan babbar ƙalubalen da muka fuskanta a lokacin wa'adin mu shine na samar da Kuɗin shiga da gudanar da ayyukan ci gaban Ɗalibai da sauran su. 

Mun samu kuma nasarori inda muka gabatar da Koyar da Sana'o'i a watan Agusta  a Fadar Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Jakada Ahmad Nuhu Bammali ya jagoranci horon. Bayan haka a cikin Wa'adin mu munyi ƙoƙarin samo tallafi domin ɗaliban da basu da Kuɗin zana jarabawar kammala Sakandire dana share fagen shiga Jami'a (NECO, WAEC, JAMB) da sauran abubuwa.

Muna fatan Allah yasawa abinda mukayi Albarka duniya da lahira muna fatan magabatan mu su nunka ƙoƙarinsu akan namu.

Na Gode

Ahmad Aliyu Awai

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post