Alhaji Isma'il Yusuf Ashafa, Sardaunan Ikulu wanda fan asalin yakin Kudancin Kaduna ne ya lashe lambar yabon ne bisa kokarinsa na taimakawa cigaban matada da samar da ingantaccen shugabanci a tsakanin Al'umma.
A cewar shugaban kungiyar Matasa Yan jarida ta jihar Kaduna Nuhu Basheer Masa wanda kuma sune suka bada lambar yabon, yace Sardaunan ya sami nasara ne bayan dokke Sanata Sulaiman Abdu Kwari da yayi a zaben da aka gudanar a internet da yakai tsawon awa arba'in da takwas.
A nashi jawabin, Alh. Yusuf Ashafa yace lamabar yabon da aka bashi zata kara karfafa masa guiwa akan ayyukansa da yake yiwa Al'umma.
Tags
NEWS