Taskar Nasaba Ta Ƙulla Dangantaka Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Taskar Nasaba Ta Ƙulla Dangantaka Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Kafar Taskar Nasaba ta kai ziyarar ƙulla dangantaka da gwamnatin jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Cinikayya Ƙirƙira da Ƙere-Ƙere na jihar (MBIT) Farfesa. Kabir Muhammad Mato.

A jawabin nasa Mato ya yaba da ayyukan da Kafar Taskar Nasaba take aiwatarwa na farfaɗo da tarihi da haɓaka al'adu. Ya kuma yi kira ga shugabanni da ƴan kasuwa da hukumomi da ƙungiyoyi da su bada tasu gudunmowar bisa ayyukan da wannan kafa take gudanarwa. 

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a cikin wata ziyara da Taskar Nasaba ta kai masa a ranar Talatar da ta gabata. 

Taskar Nasaba Ta Ƙulla Dangantaka Da Gwamnatin Jihar Kaduna


Har ila yau, Farfesa Mato ya ƙara da cewa, "Ƙofar mu a buɗe take domin tallafawa manufofin ku. Kuma a shirye muke mu yi haɗin guiwa tare domin wanzar da ci gaba."

A nasa jawabin, Jami’an Hulɗa Da Jama'a na Taskar Nasaba, Sani Musa Daitu ya ce, sun kawo ziyarar ne domin ƙulla alaƙa don tabbatar da amfani da fasahar zamani wajen bunƙasa Tarihi da Al'adu da kuma Yawon Buɗe Ido gaba ɗaya.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post