Taskar Nasaba za ta shirya taro a kan Ɓunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Sana'o'i da kuma Fasahar Ƙirƙira karo na farko.

Taskar Nasaba za ta shirya taro a kan Ɓunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Sana'o'i da kuma Fasahar Ƙirƙira karo na farko.

Taskar Nasaba za ta shirya taro a kan Ɓunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Sana'o'i da kuma Fasahar Ƙirƙira karo na farko. 

Kafar Taskar Nasaba da haɗin guiwar Muryar Ƴanci mallakin gidan Rediyo da Talabijin na Liberty da Ma'aikatar Cinikayya Ƙirƙira da ƙere-ƙere ta jihar Kaduna (MBIT) da sauran abokan hulɗarmu, za mu gabatar da babban taron ƙara wa juna sani a kan bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i da fasahar ƙirƙira karo na farko 2022 (TN SME's Arts & Innovation 1.0 2022), cikin harshen Hausa zalla. 


GAME DA TARON

Bunƙasa Tattalin arziki ta hanyar amfani da fasahar zamani na ɗaya daga cikin ƙudurorin Taskar Nasaba domin hakan zai rage masu zaman kashe wando kuma zai samar da dubban ayyukan yi a tsakanin matasa, hakan tasa sashen Tattalin arziki na Taskar Nasaba da abokan haɗin guiwa muke son gabatar da horo na musamman domin inganta sana'o'i da kuma masu baiwar fasaha da ƙirƙira domin ba su horo na musamman domin tafiya daidai da zamani. Ƙanana da matsakaitan sana'o'i da fannin ƙirƙira na samar da kashi sittin da Ɗaya da ɗigo Biyar (61.5%) na ayyukan yi a Najeriya. 

Manufar hakan ita ce, taimaka wa wajen samar da Ilimi a kan duk wata sana'a ko baiwa ta ƙirƙira domin ka fahimci yadda za ka ci moriyar baiwar da Allah Ya yassare maka don kai ma ka ba wa al'umma gudunmowa wajen rage marasa ayyukan yi a ƙasa.  

Ƙarni na Ashirin da Ɗaya (21st century) lokaci ne da kimiyya da fasaha ke da tasiri, hakan ya taimaka wajen samar da dubban ayyukan yi a cikin al'umma musamman a ƙasashen masu tasowa, in da ake da ƙaranci guraben ayyukan yi. 


Taken Taro : Himma Ba Ta Ga Rago 

ƘARIN BAYANI

Taron zai gudana a jihar Kaduna, kowa na da damar halarta a Arewacin Najeriya in da zai gudana a watan Nuwamba 2022, in da masana daga fannoni daban-daban a ɓangaren tattalin arziki za su bajekolin su wajen gabatar da maƙala, daga cikin su akwai; Bankuna da Malamai da masana da hukumomi na Gwamnati da masu zaman kan su.

Dama ce a gare ku domin haɗin guiwa ko bada tallafi ko ɗaukar nauyi don ganin an sami nasara, ku tuntuɓe mu a 09131227413 ,07063387335, 08030977378 ko a Taskarnasaba001@gmail.com


Basira Sabo Nadabo 

Jami'ar Hulɗa Da Jama'a II 

Taskar Nasaba

28/10/2022

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post