Shiba Tayi Kira Ga Matasa Su Tashi Sunemi Na Kansu.

Shiba Tayi Kira Ga Matasa Su Tashi Sunemi Na Kansu.

Ƙungiyar Ɗaliban Kiwon Lafiya ta Ƙasa Baki ɗaya (National Association of Health Information Management Students NAHIMS) Tare da Haɗin Guiwar Ƙungiyar Matasan Nijeriya Masu Nazari da Tantance Kyakykyawan Shugabanci. (Nigerian Youth Good Governance and Development Initiative NAGGDI) sun karrama Hajiya Bilkisu Shiba Zailani da lambar yabo a Kaduna. 


A Jawabinta Hajiya Shiba tace "bazata iya nuna farin cikin ta ba da wannan karramawar da akayi mata tace hakan yazo lokacin daya dace, ta ƙare da cewa tana Alfahari da asalin ta wato Najeriya duk da tanada Izinin zama a Amurka, tayi kira ga matasa da su tashi su nemi na kansu su kauce wa shiga miyagun laifuka".


Shiba tace a shirye take data tallafawa matasa a duk lokacin da buƙatar hakan ya taso, shiyasa ta buɗe Gidauniyar ta domin faɗaɗa ayyukan ta na jinƙai da tallafawa Marayu da marasa galihu.


Shima a nasa Jawabin Shugaban Ƙungiyar NAHIMS Kwamared Jibril Salihi "yace sunga da cewa da cancantar ne yasa suka zaɓota don karramawa yace hakan abune da ya kamata saboda ƙara mata ƙwarin guiwa akan ayyukan ta na Alheri kuma bazamu gajiya ba wajen tallafawa don cinma burin ta".


Taron ya gudana ranar 01/11/2022 a Kaduna inda shugaban ya sami rakiyar Membobin ƙungiyar na jihohi.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post