Bikin karramawar wadda aka yi wa laƙabi da “Arewa Stars 30 Under 30,” wadda ya shafi matasa ƴan shekara Talatin zuwa ƙasa, wadda jaridar Arewa Agenda, da PR Nigeria tare da haɗin guiwar Daily Nigeria suka haɗu wurin shiryawa tare da tallafin Gidauniyar A.A Gwarzo, wadda Dr. Musa Abdullahi Sufi ya ke jagoranta.
Matasa 30 daga arewacin Najeriya waɗanda shekarunsu ba su kai 30 ba ne jaridun Arewa Agenda da PR Nigeria tare da haɗin guiwar Daily Nigeria ta karrama su bisa irin gudunmowa da suke bayar wa a fannoni daban-daban a cikin al'umma.
Bikin wadda aka gudanar a jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar, a ranar Asabar (3/14/22) domin nuna farin ciki da ƙwazo daga matasa na Arewa suke yi da kuma yin tasiri da zaburar da al'umma kai-tsaye.
Tawagar alƙalan da Dr. Kabir Sufi, ya jagoranta sun zaɓo mutane 30 daga cikin sama da 300 da suka fafata, waɗanda suka haɗa da malamai, manyan ƴan jarida, shugabannin ƴan kasuwa, marubuta, jami'an aikin jin ƙai, wasanni, gwagwarmaya, da kuma fasahar ƙere-ƙere da sauran ɓangarori na rayuwa.
Har ila yau, Kafar Taskar Nasaba ita ce ta zamo gagarabadau a wannan taro da ya gudana, wadda Ma'aikatan ta guda Shida ciki har da shugaban ta Salahuddeen Muhammad, suka samu lambar yabo duba da irin gudunmowar da suke bayar wa a fannonin daban-daban.
Da yake jawabi a wajen bikin, shugaban jaridar Arewa Agenda kuma shugaban kwamitin shirya taron, Mohammed Ɗahiru Lawal, ya shaida wa mahalarta taron cewa, "Jigon bikin ba wai kawai don bayar da lambar yabo ba ne, har ma da samar da wata hanyar da za a bi domin isar da saƙo zuwa ga masu ba da shawara da masu faɗa a ji daga yankin arewa domin matasa su sami hanyar cimma muradansu."
Bugu da ƙari, ba ya ga karrama matasa 30 na Arewa ƴan ƙasa da shekaru 30 da lambobin yabo daban-daban, an kuma gudanar da kaɗe-kaɗe da na barkwanci, da muhawarar ƙarawa juna sani, da tattaunawa mai ma’ana wadda ta mayar da hankali kan yadda za a faɗaɗa tunani da makomar rayuwar matasan Arewa.