KADUNA: Za Mu Kammala Aikin Hanyar Shiga Garin Kauru – Uba Sani

KADUNA: Za Mu Kammala Aikin Hanyar Shiga Garin Kauru – Uba Sani

Dantakar Kujerar Gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, da yardar Allah idan ya zama gwamna zasu kammala sauran ayyukan alherin da Malam Nasir Elrufai ya faro, amma lokaci bai bashi damar kammala su ba, ciki har da karasa aikin titin shiga Garin Kauru.

Sanata Uba Sani ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar gaisuwar bangirma da ya kai fadar Mai martaba Sarkin Kauru Alhaji Zakari Ya’u Usman, da kuma ganawa da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kauru, a yayin da tawagar jirgin kamfen din Sanata Uba Sani ta ziyararci karamar hukumar Kauru da Lere.

Uba Sani ya kuma kara da bayyana cewa, “abin da zamu sa a gaba shi ne kammala manya da kananan ayyukan alherin da wannan gwamnatin Malam Nasir Elrufai ta faro domin ci gaban Al’ummar jihar Kaduna baki daya.”

Ya kara da cewa, “Sannan zamuyi kokari wajen ganin mun taimakama manoman rani da damina domin su habaka sana’ar noma. Sannan za mu taimaka wa mata da matasa da jari, domin su kama sana’oin da zasu dogara da kansu.”

Sanata Uba Sani ya ci gaba da cewa, ”Sannan da yardar Allah zamu daura daga inda Malam Nasiru Elrifai ya tsaya akan harkar tsaro, domin ci gaban harkar tsaro abu ne mai muhimmancin gaske.”

A nasa jawabin, Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman, ya bayyana fatan alherinsa da kuma addu’ar samun nasara ga Sanata Uba Sani.

Suma a nasu jawaban daban daban, Wakilan Jama’atul Nasril Islam da kuma na kungiyar CAN, da kuma na Kungiyoyin Mata da Matasa sun bayyana addu’arsu da fatan alherin nasara ga Sanata Uba Sani.

Taron kamfen din ya gudana ne a daukacin kananan hukumomin Kauru da Lere. Inda Sanata Uba Sani ya sami tarbar dimbin mutune daga ko ina.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post