Kyalkyalin Kauna page 9 Hausa Novels

 

Kyalkyalin Kauna page 9 Hausa Novels

✨ KYALKYALIN KAUNA✨
      ✍🏻M SHAKUR
EPISODE 9️⃣


ZAKU IYA SAMIN EPISODE 10 only on my IG page;

8, 9 dakuma 10 under kowani post I will be picking 2 winners to join my paid group free💃 go and drop your comment, zanyi selecting comments dayay sweeting belly na, da wayanda sukai tagging mutane I don’t mind kukai taggin duka mutanen IG ma😂 dakuma wayanda naga sunada likes dayawa under comment nasu💃

https://www.instagram.com/p/CtENyNPIpNs/?igshid=MTc4MmM1YmI2Ng==
Baba da team nashi kowanne na road din da Baba yamusu assigning, Baba da su Aliyu sune suka tsaya kan daidai Dikko junction, sun rarraba kansu sunsa kayan gida normal kaya da bazaka taba dauka polisawa bane, wasu na wajen yan shayi wasu na wajen yan saida tsire, wasu kuma na wajen masu saida ayaba, Baba kuma dayasai ledan kankara da minerals keciki gabaki daya nawani yaro ya karba yadaura aka yana yawo akan titin yana saidawa masu motoci da passenger, dan junction din ba dare ba rana is always active saidai wani zubin da daddare babu motoci sosai kaman rana, Baba hakanan yaji zuciyanshi yafi bashi tanan zasu bullo sabida titin minna criminals nason titin, kaman daga sama Baba yahango wasu manyan trailer na container guda uku suna tahowa ruwan na kanshi yana tafiya akan titin yace “team stay alert, stay alert ga containers guda uku na tahowa let’s get them, I will give you the signal” daidai dayan team nachan hanyan gwagwalada na fadin suma ga wasu containers biyu na tahowa, hakan yasa Baba yace “get them is them, sune” baiji tsoroba ko shakka ba tundaga nesa ya tsaya akan titin ta yanda babban motan idan tazo dole saita tsaya ta rage gudu, aiko kaman yasan hakan zai faru daidai yazo dab da Baba babban motan dake gaba ya tsaya tareda jan glass kasa ya leko da kanshi yace “so kake yan uwanka suyi bidiri da kudin diyyan ka kome dan kaman ka kusan shekawa, dole ne sainasayi ruwan ka bakaga dare bane” kaman begger Baba yataho ta side na kofan direban yace “yallabai kataimakamini kasaya iyalaina zan bawa abinci da kudin” ko kaine kaga yanda Baba yayi saiya baka tausayi, komawa cikin motan direban yayi yace “hayo kabani lakasera da ruwan paro, dasauri Baba yasauke jakan ruwan akasa yaciro lakasera da paro ya dane sama yanama yaranshi signal da fingers daidai direban yadauko kudi yajuyo zaibama Baba da kanshi keta window kawai yaga Baba yanuna mishi bindiga anatse yace “ko motsi kayi balle kai kokarin jan motan nan zan bindigeka billahillazi” Daidai sauran yaranshi suma sunma motoci biyun na baya haka, hannu Baba yakai ciki still bindigar na kan direban yabude kofan sannan yawani kalan fizgo direban Ya sauko dashi kasa sauran ma haka, Aliyu yakawoma Baba handcuff dasauri ganin dai da gaske ne yasa direban yace “dama yan fashi na sama mutane ankwa to Kodai ku kidnappers ne dan Allah kuyakuri kada ku kamamu kome kukeso kubari nakira Ogan mu za’abiyaku wlh” wani kalan murmushi Baba yayi yace “kana magana da Commissioner na police Ibrahim Ibrahim” Baba yakalli Aliyu yamai alamu daya duba motocin, bude container sukayi dasauri suka fito suna maidawa suka rufe, Baba yace “zubasu a mota Aliyu, zanja mota daya kace Kamal da Balarabe sun iya babban mota ko”? Dasauri Aliyu yace “yes sir” Baba yace “tafi dasu muna biyedaku abaya” daidai sauran team din suna waya sukace sun kamashi sun kama package din, murmushi Baba yayi yashiga babban  motan yaja motan zuwa police station, parking trailer uku akayi achan asalin garage da ake parking motoci da machines na mutane da aka kwace, Baba yace “awuce dasu interrogation room bari yafara magana da IG” dan yasan IG baitafi gida ba sauran suma sun kusan zuwa da sauran trailer biyun.

****Agogon hannunshi yakalla this is 4:25AM amman har yanzu direbobin nan basu iso ba kuma hakan baitaba faruwa ba yawanci 1 ko 2 nadare highest sunkawo shipment din, ijiyan zuciya Nas yasauke feeling so uneasy, Wike dake gefenshi yana zukan wiwi yakalla yakai hannunshi ya fizge wiwin yace “I need this” dan dariya Wike yayi yace “kacika damuwa Oga Nas maybe dan delay aka samu sabida traffic but zaka gansu try calling them muji bari nashiga ciki naga sun gama gyara vans din dazai transporting kayan to basement” yay maganan yana wucewa yashiga cikin babban building na wajen na wani supermarket, waya Nas yaciro yana shan wiwi yay dialing number dayay saving da Head Driver amman akashe, tsaki yaja yace “why the fuck zai kashe wayanshi at this time of all times haaa” kirrrr sako yashigo wayanshi dasauri yakalli wayan, messege yagani daga head driver 2. “Oga wani dan sanda yakamamu muna headquarter yanzu haka, sun fita sun barmu ne karamin wayan nan na kafana shine namaka sakon nan, nai alkawari bazan taba fadin komi ba amman yarana basu saba da police station ba tsorona kada suyi magana ayi wani abu Oga da gaggawa…..” baya Nas yayi zai fadi dasauri Wike daya fito yatareshi yace “Oga Nas lafiya” wayanshi yamikamai dasauri Wike ya karba ya karanta sakon damuwa karara akan fuskanshi yace “tunda muka fara operation bamu taba samin matsala da yan sanda ba, wani zubin suke taimakon mu ma product dinmu ya iso, yanzu an kama all 5 containers namu da already masu abubuwa na jira yaya zamuyi, who is behind this? Waya isa yataba kayan Pablo Escobar”? Saida akama kira sunan Pablo hankalin Nas yadawo jikinshi dasauri yashiga daddana wayan number Maheer yayi dialing wayan na gab da katsewa aka dauka batare da anyi magana ba.


Cikeda shakka da fargaba akuma rude Nas yace “Pablo ansamu matsala fa” shiru still yaji baice komi ba kuma yasan yanajinshi sarai hakan yasa ahankali kaman Mai tsoron yafada yace “police sun kama kayanmu da direbobin mu duka yanzun nan head driver yamin sako asace daga karamin wayanshi dake kafanshi, Maheer wlh wlh kasanni tunda kai assigning this role to me bantaba mistake ba, tayaya police sukasan shipment namu zai iso yau dakuma time, wani snitch muka samu a empire nan, this has never happened before baitab………” “where are you now”? Maheer yay maganan a mugun natse da sauri kirjin Nas na bugawa sosai yace “muna border” dan shiru yayi nakusan 1min sannan yace “get everyone and everything out of there, wipe every trace na komi awajen makesure bakubar komi dazaisa yan sanda sukara gano wani abu namu from border ba and get back to house zan hadu daku awajen” dasauri Nas yace “t…..toom” juyawa yayi suka koma ciki suka sanar da sauran ma’aikatan ciki suka fara aiki suna kwashe komi da gyara komi ana lodawa a van, kafin 30min dayake hannu dayawa ne bazaka taba sanin wani yataba rayuwa awajen ba, sannan sukaja mota zuwa gida gaban Nas faduwa kawai yake kaman tsinken agogo.Tun bayan wayan yana zaune akan kujeranshi a office Ya lumshe idanu wanda yasanshi ne kadai zai iya gane yanda ranshi ke mugun bace, yakai morethan 30mins ahaka sannan yadanna wani botur, Dan yashigo office din dasauri yace “car is ready Sir” ahankali yatashi tsaye yakalli Dan sannan yasauke idanunshi kan table yashiga kwashe kwashen wayanshi da yan kananun abubuwanshi ahankali yace “who do you think get the nerves to betray me in this empire Dan?” Dasauri Dan yadago kanshi yakalli Maheer daya dauki wayanshi looking confuse dan baigane kan tambayan ba, wani bakin glass yadauka yasaka dan yawanci idan ranshi abace bakin glass yake sawa sabida baimaso kaga idanunshi yace “wakake gani zai iya bama police tip akan kayana dazasu iso yau” adan tsorace Dan yasauke ijiyan zuciya yace “gaskiya banjinba duka mutanen empire nan are people damukai aiki dasu for years basu taba yin abu makamancin haka ba gaskiya brain dinga baiga wanda zai iya yaudara ka haka cikinmu ba” murya chan kasa Maheer yace “kake gani?” Kallon Maheer yayi wani abu yaji ya makalemai awuya sabida yanda yaga yana kallonshi ahankali yace “yes sir anddd…..” yadanyi shiru yana kallon Maheer still yace “maybe coincidence ne” for the first time wani kalan smirking Maheer yayi yace “I don’t believe in coincidence” tafiya yafara saida yazo daidai gab da Dan daya budemai kofa yace “da coincidence ne da CP bazai fita dakanshi ba yaje operation haka da daddaren nan ba” binshi abaya Dan yake harsuka fita daga club din,  mota yashiga Dan yamaida kofar motan yarufe sanan suka wuce zuwa gida.Bude musu gate sojan mai gadinsu yayi mazane kusan 200 a compound din anyi charko charko ana magana ganin motan Maheer yadanno kai cikin gidan kowa yayi tsit, karasawa wajen parking direba yayi yay parking sannan Dan ya sauko yabudemai kofa, kusan 2min yayi sannan yasauko cikin wani kalan izza da Kamala kaman sarki, binsu yayi da kallo one by one kafin anatse yace “what are you all doing here”? Tsit kowa yayi kaman ruwa yacisu, dan murmushi yayi yace “koma wanene yace zai yaudareni trust me his days are numbered not just him har grandkids nashi saina tabbatar na batar da zuri’anshi kakkab adoron kasan nan” idan kaji yanda yake magana kasan tabbas zai iya, shiru yayi yana kallon kowa yace “banbancina da mutane da yawa shine I don’t tell my enemies to stop rather i encourage them yacigaba!” Yasake shiru yace “I don’t hide and I fear no one!” Zokaji tapi pap pap pap ake, saida suka tsagaita yace “I will never shut down my operation and zan muku alkawari guda, nan da 24-48hrs shipments dina da Direbas dina are coming back to me!” Tafi da ihu kawai mutanen suke saida suka tsagaita yace “get back to work, Snitch har address na gidan nan kabayar you will rot!” “Allah yabar mana Pablo, Escobar! Escobar! Escobar!” Ihu kawai suke suna tafi suna shouting sunanshi yawuce ciki Dan yabishi abaya, haka Nas da Wike.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post