✨KYALKYALIN KAUNA✨
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣8️⃣
For your original Egypt Abayas,home decor, Gold (new and used), shoes that are qualitative and unique at affordable price , siyen daya ko sari (wholesale and retail) contact +201123302418
Instagram @Shopper_topia
WhatsApp group *Maryam’s Egypt abaya *
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Ita bama tagane inda akai da itaba kokawa take sosai tana tutturjewa tana kokarin kwace hannunta tana kuka sosai tana waigawa tana kiran Farida da duka muryanta da Nana, batasan ta ina akabi da itaba wani babban mahaukacin falo suka shigo da ita akai wani corridor da ita sai chan aka bude wani kofa daganan bakin kofa aka jefata cikin dakin saida ta buge dan kwalin data rufa dashi ma fita yayi daga kanta bata damu da bamata bi ta dankwali ba tashi tayi da gudu tai kofan tana kuka sosai tashiga kiciniyar bude kofan amman arufe hakan yasa tafashe da kuka sosai tana bubbuga kofan tace “dan dan Allah, dan Allah ku budemini kofan, wlh Nanah da Farida zasuyita Kuka please please dan Allah kuji tausayina dasu Nana kubude mini” gajiya tayi da bubbuga kofan ahankali ta tsugunna jikin kofan tareda kife kanta akofan tana wani kalan kuka mai tsuma rai ashe tun jiya batai kuka bane sabida tana taredasu Farida tana ganinsu, yanzu da aka rabasu sai taji duniyan gabaki daya yamata zafi kawai Nanah kefadowa ranta da Farida ga tausayinsu da yanda zasuyi yanda batanan din nan takeji, tai kuka tai kuka harta godema Allah, takai kusan awa biyu awajen kofan kuka take once in a while tana roko abudeta, chan same kamshin turaren nan dataji dazun ne yadaki hancinta hakan yasa tamike tsaye dasauri tana wani kalan bubbuga kofan tana jijjiga kofan tana kuka. “Dan Allah kace su bude ni dan Allah, kayakuri please please please, Nanahhhhhh, Faridaaaa, Ammiiiii……. Dan Allah kayakuri baran karaba” bude kofan dataji anayi yasa tai shiru tashiga kallon kofan da sauri takoma baya, shigowa Maheer yayi dakin yana sanye dawani 3quater navy blue na Fendi sai off white t-shirt mai gajeren hannu dayamai wani kalan mahaukacin kyau dan kunnen diamond dake makale a kunnenshi yana wani kalan shinning yana sheki hannunshi rikeda wayanshi, kafafunshi sanye dawasu fararen crocs designers, yana zuba wani kalan kamshi kaman wanda yafito daga kogin turare, wavy gashin kanshi na kyalli da sajenshi, lips nashi sunyi pink sosai looking so moist and succulent, wannan karan baisaka bakin glasses ba hada idanu sukayi wani kalan faduwa gabanta yayi dasauri ta sauke kanta kasa ganin yanda yakeda dogayen gashin idanu kaman mace, takai bayan hannunta tana share fuskanta, dauke kai yayi yawuce cikin office din shikuma Dan dayake tsaye ata waje yarufo kofan dasauri tai wajen kofan tashiga bugawa tanajan kofan ganin ba’a budeba yasa takife kanta jikin kofan tafashe da kuka sosai kaman wata marainiya da aka kulle adaki tanaso tafita.
Ahankali yazauna kan kujeranshi yaja system yabude ya kunna kafin gently yadago kanshi yadaura manyan idanunshi akanta yanabin tundaga gashin kanta dayake abude da kallo wanda wani shuku dayay tsufa ne akanta but baihana kaga silky black long hair nata ba, gashin ma sun zazzaro waje dan tanada tsantsin gashi gasu kuma so coily, ganin duka gidan nan babu mai imani ko tausayin Nanah karama ma dake kuka balle ita babba yasa tawani juyo da sauri karaf suka hada idanu yahade rai tamau ya tsuke fuska, wani kalan wankamai wani uban harara tayi tareda kai bayan hannunta tashare fuskanta tass tass tawuce wajen dan kwalinta datagani akasa ta dauka takai hancinta ta fyato majina, wani kalan yatsine fuska Maheer yayi shi karan kanshi baimasan yayi ba irin ewww din nan dirty girl, kaman taji ajikinta dago manyan idanunta tayi ganin yanda yayi da fuska yasa takara wankamai wani mugun harara kaman zata kasheshi da idanu dayasa ya zaro idanushi cikeda mamaki irin wat! Sake ballamai hararan tayi ciki ciki tace “mara imani kawai” cikin kakkausan murya yace “mekika ce”? Juyowa tayi takalleshi da sauri suka hada ido cikin tsantsan dakewa dan yanzu jitake dukma abinda zai faru yafaru tace “cewa nayi Allah yasa kada Babana ma yabaka abinda kakeso duk abinda zakayi kayi” tsayawa yayi chak yana kallonta abin looks really strange to him, dan tunda yake babu wacce tama isa tamai wani kalan kallo balle tamai rashin kunya haka wato she’s stubborn kaman babanta, kwallin taba yadauka yabude yazaro daya yakai bakinshi yadauki lighter zai kunna saikuma yakalleta anatse yace “idan Babanki bai bani kayan kwayoyi na ba saina kasheshi har lahira” zaro manyan idanunta dasuke jikeda ruwan hawaye tayi ta kalleshi kana ganinta kaga tsoro da fargaba dakuma shakkan shi aranta jin yanda yake kiran kisan kai kai tsaye, hakanan saiyaji yaji mugun dadin hakan, lighter yasa ya kunna taban sannan ya ijiye ya zuki taban ya fuzar ahankali yace “bashi kadai zan kasheba duk wani tsatso da jininshi daya bari aduniya sainabi na kashesu daya bayan daya” yakara zukan taban ya fuzar, yabita da kallo yanda yaga yan dogayen brown skin yatsunta ke rawa masu kyau dabasu da dark knuckles, gently yadauki wayanshi yabude yay dialing number Dan yasa a speaker yace “bari nafara da kannenki” dawani kalan sauri ta kalleshi dan bata gane takamaimen mene ze fara da kannenta ba, daukan wayan Dan yayi yace “yes sir” dan shiru yayi yakalleta yanda take zaro manya manyan idanunta tana kallonshi cikin wani kalan murya na asalin mugunta da isa yace “shoot those children Dan, ka kwashe gawawwakin su ka bama Kikito yaci don’t cut the call, execute the task ina kan wayan” dasauri Dan yace “Yes Sir” wani kalan mikewa tsaye Yasmeen tayi kanta har juyawa yake jikinta wani kalan bari bari yafara kaman wacce takeda farfadiya tana dumfaro shi tace “dan girman Allah, dan girman Allah malam kada ka kashe kannina, kill me, nika kasheni dan Allah let them be, ka kasheni, kayakuri dan Allah kaya kuri” tana tafiya tana hade hannayenta biyu tana rokonshi tana karasowa wajen dayake ta zagayo ta bayan table din kusada shi tafashe da kuka sosai tahade hannayenta biyu tana kallonshi yanda yakeshan katon lukutin taban abinshi ko kallonta bayayi daidai nan taji karan bude kofa tawayan saiga kukan Nanah kaman zai tsaga wayan, Dan yace “Sir gani nan na iso” zaro manyan idanunta tayi kirjinta na bugawa sosai tarushe da kuka tai kneeling gefenshi takai hannunta saman hannun kujeran dayake zauna tana kallonshi tana kallon wayan tace “dan Allah kada ka kashe kannina dan girman Allah dan ya Rasullullahi, bawan Allah kayakuri kada ka kashe min Farida da Nanah su kadai ne kannina dan Allah” daidai lokacin taji kukan Nanah da ihun Farida tana cewa “wayyo me kake nunani da bindiga” Yasmeen batasan lokacin data mike daga kneeling din datayi ba hannunta har rawa yake tawani kalan daukan wayanshi garin haka hannunta ya gogi nashi wani kalan shocking Maheer yaji dasauri yakalleta, bama tasan tayiba dasauri takai wayan kunnenta kaman ba a speaker wayan yake ba tana ihu sosai tace “dan Allah kada ka kashemin kan……” tuss tuss taji sau biyu wani kalan ware idanunta tayi kafin idanunta suwani kalan juye sama tai baya luuuuu zata zube kasa dawani kalan sauri Maheer yatarota hakan yasa tafado jikinshi a sandare.