Furar Danƙo chapter 11 by Billyn Abdul

Furar Danƙo chapter 11 by Billyn Abdul

 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣

........Nagartaccen likita nutsatstse da ya san makamar aikinsa. Cikin girmamawa ya gaida Mommy da Daddy, Uncle Yousuf kuma ya bashi hannu sukai musabaha dan zasu iya zama sa'anni. Kusan mintuna uku ya nisa yana mai gyara gilashin idanunsa da ɗagowa ya ɗan kallesu. “A ɗazun mun ɗan fara magana da Yousuf wani hanzari ya katseni, shiyyasa na buƙaci ganinku ku duka saboda muhimmancin abinda zan faɗa game da lafiyar Muwaddat”.

        “Doctor ALLAH dai yasa ba wani mummunan ciwo bane, idan kasan akwai matsala dan ALLAH ka barmu mu wuce da ita ƙetare kar sai al'amarin ya ƙwace azo ana wallahi tallahi zuciyarmu bazata iya ɗauka ba”.

          “Ka kwantar da hankalinka Alhaji, bawai matsalar zamanta anan ko fitar da ita zuwa ƙasar waje ne damuwar ba. Sanadin abinda ya haddasa mata ciwon nake son ku sani domin a ɗauki mataki....”

     “Minene likita?”.

  Daddy ya sake faɗa a zabure cikin katse Dr Khalifa Shira. 

            “Kwantar da hankalinka Alhaji”. Khalifa ya faɗa yana sake gyara zama. Cigaba yay da faɗin, “Ina son ku fahimci maganata da idon basira duk da ban sani ba ko kun san halin da take ciki kafin yau ɗin. Bincikemu ya nuna mana ba komai ya haddasa mata matsalar da take ciki ba yanzu sai Shaye-shaye..”

      “What?!!”.

Daddy ya faɗa yana miƙewa zumbur. Jikinsa har rawa yake wajen nuna Dr Khalil Shira. “Yarinyar tawa zakaima sharri, miya haɗa wata Muwaddat da shaye-shaye? Yarinyar da bata san komai ba sai karatunta. Amma kai dai wlhy anyi.......”

      “Yaya Please ka bari ya faɗa mana abinda ke faruwa mana. A wannan zamanin har wani gardama ko shaidar yaranmu za'ai akan hakan”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin damuwa da takaicin Daddy. Mommy ma kallonsa take cikin tashin hankali da ɓacin rai, duk da ba itace ta haifi Muwaddat da cikinta ba bazata so ace yarinyar ta lalace kamar haka ba. Tasha wahala a hannun mijinta akan mahaifiyar Muwaddat matuƙa, bayan rasuwarta kuma tabar baya da ƙura dan Daddy wani sabon shafin wulaƙanci ya buɗe akan al'amarin Muwaddat gareta....

      Bayanin da likita ya fara ne ya katse mata tunaninta. Dr Khalifa Shira ya cigaba da faɗin, “Alhaji a wannan zamanin da muke ciki wannan ba abin mamaki bane. Yara mata da yawa sun shiga wannan mummunar aƙidar abin tashin hankali harda matan aure ma. Iya gaskiyata na faɗa muku Muwaddat na shaye-shaye, kuma da alama ta jima a cikin wannan al'amarin dan gashi har ya fara taɓa mata lafiyarta. Idan kuma har bata dainaba komai zai iya faruwa ciki harda rasata. Ya dace kusa ido akanta da duk wani motsinta na rayuwa, idan da dama ma a nisantata da komai cikin hikima, sannan a rabata da duk abokan mu'amalarta akan hakan harma da inda take zuwa ta shawo dan alamu sun nunamin baku san tanayi ba. Iyaye da yawa sunfi maida hankali da damuwa akan kar ƴaƴansu mata su lalace wajen zubar da mutuncinsu akan huɗubar maza (zina), a tunaninsu wannan itace kawai matsalar dake iya tauye mace ko fanɗarar da tarbiyyarta. Shiyyasa sai yaran har suyi nisa a lalacewar da basu jawoma kansu tunaninta ba misali irin wannan ta shaye-shaye daketa ƙara yawaita a cikin al'ummar mu a yau. Hakama mazaje da yawa sakacinsu da son zuciya ya haifarma matansu da yawa shiga irin wannan halin batare da sun fargaba. Yayinda wasu ɓangare na matan kan jefa kansu ne ga ɗabi'ar shaye-shayen saboda son zuciya ko zama da abokai ko ƙawaye ko samari dakan koya musu. Ya kamata ku binciki silar faɗawarta wannan yanayin kuyi kuma gaggawar maganceta duk da abin ya rigada ya mata nisa sosai sai addu'a gaskiya. ALLAH ya bata lafiya ya kuma shiryar damu da zuri'armu baki ɗaya akan tafarki na gaskiya”.

        Uncle Yousuf da Mommy ne suka iya amsawa da Amin. Daddy kam da alama ma hankalinsa sam baya jikinsa. Dr Khalifa Shira ya ɗan ƙara musu da shawarwarin yanda zasu fuskanci rayuwar Muwaddat ɗin. Kafin ya sallamesu. Har lokacin Daddy bai iya sake furta komai ba. Dan da zasu tafi ma sai da Uncle Yousuf ya taɓashi, sai dai yana yunƙurawa zai tashi juwa ta kwasheshi ya tafi zai zube ƙasa sai da suka taro shi. Hankali tashe shima aka bashi gado. Nanfa Jiƙamshi family suka sake shiga maɗaukakin tashin hankali mara misali.


       Haka suka yini ranar zubir a asibitin. Shi kansa bai samu kansa ba sai wajen goma na dare bayan ya maida Aunty Saliha matar Uncle Yousuf gida da yaransa yace ya dawo masa da motar ya wuce kawai shi dole zai kwana anan saboda Daddy shima dole an bashi gado. Dr Khalifa kuma yace bazasu sallamesa ba har sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai. Godiya yay masa da hakan dan harga ALLAH ya matuƙar gajiya dama ga yunwa dake cin hanjinsa kasancewar bai wani samu abincin kirki yaci a yinin ba sai wata ƴar gurasa. Sai dai babu yanda zai yi tunda hanyar neman abincinsa ce. Koda ya shiga gidan bai nema kowa ba ya shige ɗakinsa. Sai da ya kammala komai na al'adar rayuwarsa sannan yay zaman cin indomie ɗin daya saya wajen Haladu mai shayi. Tare da shayinsa daya sabarma kansa sha yaci, dan ya samu an dafa masa sabo a flaks. Yasan aikin ƙannensa ne dan basa gajiya da hidimarsa. Hatta ɗakinsa ƙal yake da gyara, dan ko kayansa ƙananu basa ƙyashin zama su wanke masa fes su goge, manyan kayanne dai irinsu shadda sai dai ya kai wanki. Badan kuma bazasu iyaba yake kaiwar, sai dan rage musu aiki ne. Ya jima baiyi barcin ba yana ƙullawa da kwancewa akan al'amuran rayuwa da suka haye masa badan ya tsara su a cikin rayuwarsa ba. Tun yana yaro a kullum burinsa shine buga ƙwallon ƙafa da yin kasuwanci, sai gashi yau ya tsinta kansa a wani matsayin ɓoyayyen aiki da ya zame masa haye. Dan lamarin wannan ɗan taran da bai san miye manufarsa ba yana sake kutso rayuwarsa cikin rayuwar mutanen da har yanzu ya kasa samun amsa ko dalilin dangantakar da ALLAH ya ƙulla a tsakaninsa da su batare da su sun san ma'anar hakan ba suma na cimasa rai. Su dai kawai kallon driver a ƙarƙashinsu suke masa kamar yanda Uncle Yousuf ɗin ya ɗakkosa tun farko yi. Sai kusan ɗaya da wani abu ya samu barcin ya ɗauke sa mai cike da mafarkai marasa daɗi da suka shafi Jiƙamshi family, kodan ya kwanta da tunanunsu ne a rai oho. Ai ko sai gashi ya kusa makara da asuba. Da ƙyar ya iya tashi yay alwala ya wuce massalaci...


      Sashen Abba ya fara shiga kamar yanda ya saba a kowace safiya duk da sunga juna a massalaci. Gaishesa yayi cikin girmamawa da ƙanƙan da kai tare da masa bayanin komawarsa aiki jiya. Karan farko Abba yay ɗan murmushi irin na manya. Tare da faɗin, “Naji daɗin haka sosai, ina kuma maka addu'ar fatan alkairin ALLAH ya baka ikon jurewa. Aliy ba sonka bane banayi da kaga ina maka faɗa. Zaman nan naka ne bana so a hakan. Kai ba aiki ba, ba aure ba, ba wani sana'a ƙwaƙwƙwara ba. Ka duba ƙannen bayanka kusan huɗu sunyi aure har ma ana batun yima wasu ukun. Ba maganar mata nake ba dan su dama dan hakan ta faru ba komai bane ba ai tunda matane”.

      “Kayi haƙuri Abba in sha ALLAHU zaku cigaba da samuna a yanda kuke fata. Ku gafarceni da duk ɓata muku da nake yi”.

         “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, amma ka dage dai ka nema matar aure zamanka ya isheni haka, kaima ina son ganin jininka kafin ƙasa ta rufe idanuna”.

    Ɗan murmushi kawai yayi kansa a ƙasa. Yau ya ɗan jima a wajen Abban har wasu a cikin ƙanensa suka ɗan shigo gaida Abban. Bayan barinsa nan cikin gida ya shiga. Kowane ɗaki sai da ya leƙa suka gaisa, a ɗakin Ammah ya ɗan sha shayi a tsaitsaye yay mata sallama ya fito ganin yana neman makara. Wanka yayi a gurguje yay shirinsa cikin uniform ɗin aikinsa ya fice a gidan....

         

      ★ Yau ma dai gidan Uncle Yousuf ya nufa kai tsaye, saɓanin jiya ya sameshi a compound zaune tare da baƙo. Bai zauna wajen maigadi ba ya nufesu. Uncle Yousuf dake dubansa da murmushi ya ce, “Uncle Smart na yara”. Murmushi yayi da ɗan shafa kansa suka gaisa cikin girmamawa. Baƙon nasa ma suka gaisa. Yana ƙoƙarin barin wajen Uncle Yousuf ya tsaida shi tare da nuna masa wajen zama. “Kaga zauna muyi magana shima ɗan gida ne. Dama kuma akan abinda ya shafi aikinka muke maganar. Sunansa Tajuddeen, surukina ne kuma ɗan uwana. Yaso Muwaddat da muka kai asibiti jiya kuma yana akan sonta dan har ranar aure an saka musu shekaru uku da suka gabata, sai dai taƙi yarda ai bikin. Abinda yasa nace maka zaman ya shafeka saboda taimakon da muke son kai mana ne tare da sake roƙonka kan ajiye aiki da kai niyyar yi. Aliyu a haɗuwarku ɗaya da Muwaddat kawai na fahimci zaka iya bamu taimako akanta, dan kafin kai mun saka drivers da yawa tun dawowarta ƙasar nan amma tsoronta sukeji saboda azababbiyar yarinya ce da kake ganinta, gashi bata shakkar kowa. Shiyyasa basa iya yin komai kan al'amarin ta. Akan Muwaddat kam nasan aikine mai wahalar gaske zamu baka amma dan ALLAH ka taimakemu kaine kawai hope ɗinmu a yanzu game da yanayin da take ciki.”

        Ganin yanda yakai ƙarshen maganar kamar a yanayin son jin ta bakinsa ya sashi nisawa. Cikin dakewar nan tasa ya ce, “Alhaji zan iya taimaka muku, sai dai fa akwai matsala dan zamanmu inuwa ɗaya da ita bazai yiyu ba. Kayi hakuri bazan iya ɗaukar ƙasƙanci ba, idan tace zata wulaƙantani bana zaton kallonta matsayin wadda nakema aiki zan ɗauki mataki kanta ako ina ne kuma”. 

       “Na baka wannan damar, dan hakan nafi buƙata nima”.

      “Shikenan, wane irin taimako kuke buƙata da ga gareni?”.

     “Sanya mana ido akan al'amuranta, ƙawayenta, abokan mu'amalarta, inda take zuwa bayan wajen aiki. Kai hatta waya da zatayi idan san samune musan dawa take yi. Bayan ka gama sanin waɗan nan sai muje mataki na gaba”.

           “Indai wannan ne babu damuwa in sha ALLAHU”.

     Godiya sukai masa, tare da tabbatar masa zai fara aiki da ita da zarar an sallamota asibiti. Sun kuma ninka masa albashinsa..........✍️



_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



VIP🔥💯

Zafin kai 3k

Furar danko 3k

Tabarmar kashi 3k

Bakon munafuki 3k

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post