Zafin Kai page 16 & 17 complete by Mamuhgee

 

Zafin Kai page 16 & 17 complete by Mamuhgee

_ArewaBooks@Mamuhgee_

16

Annensu yanayin manyanci da wahala ga kunnenta da bataji yanzu sosai yanda ya kamata yasa jikinta da lafiya suka fara yimata qaranci yau da gobe wasu ayyukan bata iya yinsu da kyau dan haka sune suka karbe mata duk wani aiki saidai idan suna makaranta a bata wani aikin shima suna dawowa zasu karban mata hande tayi ta fada amma karba sukeyi saidai wata ran susha marika gurin Ababa akan sun fara Rena hande.


Sbd Anne yasa Benazir takoma gaggawa takewa karantunta ana tashi take dawowa bata batar da lokaci ko qanqani Shiyasa basa dawowa tare da sumayyah kusan tafiyarsu yanzu tare ta rage sosai,


Sumayyah tafara IT dinta a wata makarantar kusa da anguwarsu dan haka Ababa ya dena bata kudin mashin ita da qafa take zuwa ta dawo da qafa dan haka take rigan Benazir fita tinda safe.


Bilal ne da kansa yake kaita lokuta da dama kuma ya daukota ita kuma Benazir Sulaiman ne yaci gaba da kaita kuma abincinta babu wanda aka fasa kawo mata makaranta kaman yanda itama sumayyah acan ake kai mata nata.


IT din sumayyah ya sake kusancinta da Bilal kwatsam saiga maganar aurenta da wanda yayi alqawarin bawa yana karban kudinsa akan karatunta ta taso sbd karatun nata yazo karshe dan haka maganar aure ta taso take gadan gadan ba daukan lokaci.


Maganar auren ta rusa duk wani kwanciyar hankalin Bilal ita kuma dukkanin hope din data samu ya wargaje sbd tasan maganar Ababa bamai fasuwa bace ko gardamawa,ko mahaukacin kare ya cijeta bazata iya ko dagowa ta kalli Hukuncin Ababan ba bare gardamawa.


Abinda ya dagawa bilal hankali kenan wato sarewarta da kasa iya cewa komai akan hakan sbd shi anasa bangaren yaso ta basa hadin kai da goyan baya ya sakewa Ababan Nera ba yar kadan ba dan ya hanawa kowa aurenta ya basa ita sbd a hankali ya fahimci irin asalin rayuwar rashin gata da yancin dasukeyi hannunsa dan hakan ne ma yakejin idan bai karbesu su dakan daga hannun Ababan ba kaman zai iya shiga wani halin sbd zai iya komai dan ya rabasu da gidan dan haka auren Sumayyah din yake jin tabbas ba fashi garesa da yardar Allah.


Benazir tayi nisa a karatunta batasan tashin hankalin da suke cikiba saida Yaje daukanta da kansa ranar yake sanar da ita irin yanda yakeson daukesu daga gidan suyi rayuwarsu kaman kowa.

Haka kuma a shirye yake da auren Sumayyah ta roketa tabarsa yaje gurin Ababan dan yana qin zuwan ne sbd baisan kalan azabar da zai janyo musu ba shiyasa yaketa kiyayewa.


Ita kanta Benazir jin hakan saida takusa shidewar mintina sbd firgitaccen tashin hankalin wucin gadin data shiga sbd zuwansa gurin Ababa koda motar kudi zai ake masa wlh saiya kusa aikasu lahira kafin ya amsa kudin sbd sun take qaqqarfan doka da sharadinsa akansu na kula kowane irin namiji.


Cikin rashin boye masa tashin hankali da tsoronta taqi amincewa zuwansa itama,


Anne ma dataji da sauri ta hanasu qarasa zancen sbd kusan da hannu suka kwatanta mata rabin zancen tinda bataji sosai sai an dan daga murya gashi zancen bana a daga murya bane wani yaji Alqiyamarsu ta tsaya.


Wanna maganar tasa ta sanya kwata kwata suka fara qaurace masa ga tsananin Ababa akansu ta qaru dan kusan yanzu dabiar kai musu ziyarar ba zata ya dauko dan haka suka shiga taitayinsu ba shiri 

Ko hanya suke tafiya basa dagowa.


Kusan sati biyu Bilal yayi bai saka daga Sumayyah har benazir a idanuwansa ba dan haka ya shiga damuwa da tashin hankali sosai sbd kar Ababa fa yayiwa Sumayyah aure bai saniba.


Ita kanta sumayyah tana cikin damuwa da qunci ga dukan da yanzu kusan kullum sai tasha sbd tinani ya hanata nutsuwa ta aikin data saba kullum saita qona manyan kayan mutane gurin guga dan haka a cikin qanqanin lokaci ciwonta yafara kokarin dawowa na kai,

Benazir na ganin haka tafara kokarin kada Ababan ya gane ciwon Sumayyah saidai kuma kusan abin gaba gaba yafara sbd da asarar datake ja masa tayi yawa sai ya hanata fita kwata kwata makarantar datake IT din bayan wahala da duka babu abinda take samu kullum a gurinsa.


Ganin lamarin yafara yawa tsoron Benazir sai qaruwa yakeyi ga Anne itama yau lafiya gobe ciwo sai abin yawa Benazir yawa tafara skipping lectures itama sbd lalura da ayyukan da karatun.


Daqyar da Addua Ababan yabar sumayyah tafara fita takoma makaranta bayan ta share kusan sati uku ko kofar gida bata isa ta leqa ba.


Koda tafara fita batada lafiya sosai dan haka suna isa makaranta Ms aysha ta dauketa da kanta a motarta sukai asibiti ita kuma Benazir tanada test a ranar dan haka ms aysha tace tayi zamanta.


A asibitin ba bata lokaci Bilal da ms aysha ta kira ya iso cikin mummunar damuwar halinda sumayyah din take ciki ta rame sosai ta sauya gabaki daya kaman wadda tai jinyar shekara guda kwance.


Ruwa da magani aka hau dara mata 

Ko minti uku basuyi da fara shiga ba ta hau zubo amai mai qarfi.

Sosai ta bata jikinta dan haka ms Aysha ta kamata bayan ta gama suka shiga toilet tayo wanka akai mata ordern kayan ba jimawa mai delivery ya kawo Bilal dinne ya karba ya miqa mata ta kofar toilet din sbd Ms aysha ta wuce ankirata da gaggawa Mijinta ya dan samu accident.


Sauya kayan tayi jiki ba qwari ta fito jiri na dibanta daqyar ta dawo da kanta gadon ta zube take aka sake maida mata ruwan wani wahalallan bacci ya dauketa.


Baccin awa hudu tayi ta farka,

Abinci yafara bata taci ba laifi kafin taje toilet da qyar tayo fitsari da Alwala ta dawo tayi sallar a zaune sbd bazata iya tsayuwaba,


Tana idarwa ya karban musu sauran maganinta yace gida zasu sbd kayanta dayakeson suje a wanke a shanya su bushe in time ta mayar dan yasan ko tsautsayi bazaisa sumayyahn taje gida da wasu kayan ba wanda ta fito dasu ba kuma gashi doguwar riga ce mara nauyi har qasa amma ta kwanta jikinta tayi mata kyau sosai duk da tana cikin hali na ciwo.


Kai tsaye wata anguwar dake zagaye kaman ta masu qasa ya nufa da ita wadda ta sanyata jin zazzabinta na sakinta sbd kusan duka gidajen anguwar ba tsarin ginin Nigeria bane,

Anguwa ce mai tsarin gine ginen Turawa masu tsada na asalin masu abun Hannu na gasken,

Tin daga babban gate din shigowa anguwar baka shiga saika fada inda kazo ka kuma nuna id card din kowane iri hakama commercial abubuwan hawa basa shiga anguwar kwata kwata,

Manyan samudawan Securities ne wani kamfanin securities mai zaman kansa suke gadin Anguwar da bazaa kirata da estate ba sbd ba estates din bace amma   Tamafi estate tsari.


Id card dinsa ya fiddar suka duba suka scanning motarsa yafada gidan wanda zashi saida ya fada private security code na gidan da zashi din wanda kowane gida akwai private security code da ake basa duk wanda zaizo gidanka sai fada masa code din ya fada a gate abarsa ya shigo.


Wangale masa manyan kofofin gari guda akai ya shigo da motarsa tareda miqewa kai tsaye zuwa gidan DD kaante wanda kaf gidan shine ya zabi zama wata anguwar daban ba acikin babban kaantes ba,


Shi kadai ya zabi rayuwarsa daban sbd yinta yanda yake so da buqata,ba damuwa,ba hayaniya,ba takura haka zalika rayuwarsa da zafin kansa dake hanasa jituwa da Mutane musamman Dad kaante wato mahaifinsa daya kasa gane haka Allah yayisa.


Duk matsi da takura tareda fadan Dad kaante da dd babba wato kakansu sunyi sun hakura amma bazai iya zama a can cikin family ba,

Baya son kusanci da gidane sbd rayuwarsa bayason duk abinda yake amfani dasu na daily life dinsa ya zama mutane na kusanta,

Idan har yana gida yasan umminsa da sister dinsa da brothern nasa da dad kaante harma da wasu baqin wata rana duk zasu ringa shigar masa ana muamalantar abubuwansa dan haka ya zabi zama a gidansa a anguwar datake da iya tsaro,tsafta,tsari da dokikin dayake so na rashin hayadan ko horn baayi aciki idan ka shigo.


Isarsu kofar gidan yasa Jikin sumayyah sake daukan rawa sbd kusan ko a hanya dasuke wucewa a anguwanni hanyarsu zuwa makaranta bata ganin irin wainnan gidajen dan haka jikinta yayi sanyi ta qara rasa kuzarinta.


Codes na bude kofar qaramin gate din gidan ya saka gidan ya bude suka shige ya sake saka na kofar shiga asalin cikin gidan kofar ta bude ya saka kai ciki kai tsaye yana janye da hannunta sbd batada karfin tsayuwa da kyau.


Dummm kirjinta yayi na kokarin rage jan numfashi sbd wani Ni'imtaccen qamshi daya shiga hancinta duk da gidan tsawon lokaci sosai ba kowa amma qamshinsa daya gama kama komai da koina na gidan ya kasa fita hakama komai na gidan tamkar kullum ana shigowa ana gyarawa komai nasa daban ne.


A rayuwar DD kaante daga black sai fari iya sune kalolinsa sai ta kama cancan ga gansa da wasu kalolin da bazasu wuce milk,ash,navy blue shikenan suma dan suna yanayi da kalolin nasa ne wato black and white,dan haka gidan nasa ya zama kusan komai na cikinsa iya wainnan kalolin ne dan haka komai yake unique na masu dala,

Luxuries kawai ta ko ina daga dala sai dala babu abinda bana Waje waje ba.


Zaunar da ita Bilal yayi yaje ya kunno switch na wutar gidan take ta kawo koina ya dauki wani irin Haske su Ac daman duk a kunne suke switch dinne aka kashe na wutar gidan kai tsaye dan haka take suka fara aiki.


Dayake harda bra dinta ne a kayan shiyasa bai bawa wani ya wanke ba yazo yayi da kansa tinda Benazir na makaranta gashi ko sumayyah bazataso a hanata test dinta ba haka shima a yanzu dayake jin Benazir din tamkar Aleeya qanwarsa ta jini bayajin zai taba bari karatunta ya ringa samun tangarda.


Abinci da magani ya bata tanasha bacci mai qarfi ya dauketa ya kaita dayan dakin dake gidan bayan na DD sbd yasan ko DD bayanan wani ya hau masa gado zai gane sbd hancinsa dayake daukan qamshi ko sabaninsa nan take koman qanqantarsa yasan halinsa dan haka baiko kwatanta kaita dakik DD dinba wanda babu ma wanda ya taba shigar masa harshi Bilal din da baida tamkarsa.


Gyara mata kwanciya yayi ya rufeta ya rage Ac dayayi mata yawa sbd yanda ta dan takure duk da sanyi na wahala sun saba dashi.


Toilet yaje ya nade kayansa ya wanke mata kayan fes duk da bai wani iyaba sbd rayuwarsa kaf bai taba wanki ba sai ranar sbd undies dinsama a machine yake sakawa bawai wankin hannu ba suma mafi yawan lokuta mai aikinsa jamil ke wanke masa.

Bayan ya gama duk ya jiqa kayansa sbd rashin iyawar toilet dinma duk ya jiqa koina,

#MAMUH#

#DD KAANTE#

#BENAZIR ABABA#

#LOVER#ROMANCE#MARRIAGE#Sisters#Little Benazir Amnah kaante

#BillonaireromancePage 17

Kallan kansa yayi a bathroom din yaga yanda ya lalata kansa da kayansa sai a lokacin ya tina da a washing machine ya wanke amma sai tinanin bai zo masa ba sbd kusan haka yake komai nasa na wautan 'yayan fari wani lokacin duk da ya zama babban mutum hakan ne yasa kusan ko yaushe dd babba a gurinsa koyaushe DD ne a gaba sbd shima yanada zafi da rashin wasa dan haka komai na DD ya masa duk da zafin kan DDn ya wuce gaban nasa sbd shi harda lokacinsa dayake kai na young billionaire sbd dukiyarsa bata Familyn kaantes bace shine ya tara abarsa da businesses nasa wainda ke qara saka dd babba dukan kirji da DD kaante jininsa ne baibar komaiba a halinsaba sak,

Yayi kudi bada kudin familynsa ko iyayensa ba.


Sake kallan kansa yakeyi yaga ko fita bazai iya daga bathroom din a hakan ba ruwa ne sosai a jikinsa dan haka ya zare kayansa kawai ya sakarwa kansa ruwan zafi ya danyi wanka sbd jin kaman yana qarnin wankin ma.


Yana gamawa ya fito ya sanye da Bathrobe mai kauri da girma datai masa yawa sbd Baiyi jikin DD ba,

Shi jikin fulani ne dashi ba girna sosai,shi kuwa DD qaqqarfan jiki ne dashi daya bude sosai sbd Geamin dayake dan haka yanayin jikinsu sam ba daya ba.


Bacci takeyi sosai dan haka ya fice dakin ya nufi bedroom din DD amma a rufe yake kuma baisan codes ne ko key ba ya hana kofan budewa sai kawai ya hakura ya dawo ya koma bathroom ya jefa kayansa a Machine dan wankewa sbd idan yayi ordern sabbin kafin kafin su iso garesa time ya tafi sosai sbd a first gate ma zaa karba delivery din tukuna shima ayo masa aikesensu daga first gate duk taruwa zaayi a qara bata time dinsu.

Yana gama wankewa ya fito ya zauna kan lafiyayyar sofa din dakin yana amsa wayoyinsa a Ahankali.******qarfe 6 na yamma Benazir ta kammala komai ta fito makarantar ta rasa yanda zatayi tasan Sumayyah na school kokuma ta wuce gida ko tana Asibiti har lokacin.

Batada wayar kira bare ta sani dan haka ta yankara kanta da sumayyah din tikitin Qaddara ta nufi gida tana fatan sumayyar na gida idan ba hakan ba yau suna cikin lissafin kwanan wahala.


Ana sallar magriba ta iso gida bata tadda sumayyah ba take jikinta yayi sanyi ta saddaqar da yau din saita Allah su a hannun Ababa.


Sallah sukayi da Anne ta fito tana wanki hankalinta na kan kofa cikin tsautsayi sai ga Ababa ya riga sumayyahn dawowa yana ganin yanda hankalin Benazir da Annensu ya tashi yasan Sumayyah bata gidan,Hande dake jiran dawowarsa tini tafara fesa masa labarin sumayyah bata iso gida ba har lolacin.


Shiru kawai yayi yana gyada kai idanuwansa akan Benazir zaiyi magana sai Sumayyahn ta shigo jiki a matuqar mace ba qwari zazzabi ne a jikinta sosai ga jiri tana gani komai na jikinta bata jinsa da qyar take daga qafafunta dasukai nauyi tana isowa tsakar gidan ta zube Benazir ta tarota tana jin zafin da jikinta yayi sosai.


Kallansu Ababan keyi cikin tsananin zafi da bacin rai da zallan takaici sbd hakurinsa akansu ya kusa qarewa kwata kwata,

Lissafin kudinsa akansu dayake yi yasa yake hana kansa yi musu dukan da zasu kakkarye ya zubar dasu a bola,

Hijab din jikin sumayyah ya cafko ta wuya yana shaqureta a zafafe yake saukar mata da marika yana tambayar uban me ta tsaya a hanya.


Daqyar ta iya bude baki tace masa batada lafiya tin jiyan shine a hanya ta fadi sai da aka kaita wani qaramin asibiti aka bata taimako.


Bakinta ya hau mari yana sake shawe wuyanta data kasa numfashi tana neman macewa.


Sai data kusa rasa ranta ya saketa yana wurgi da ita tareda qarasa sanya qafa ya rufeta da duka.


Daqyar suka sha bayan ya musu laushi itada benazir saidai Benazir din yan marika ne da basu wuce uku ba nata da sauki sosai sumayyahn ce dai taji jiki sosai.


Daki suka koma Annensu ta gasawa sumayyahn dake rawar sanyin zazzabi sosau jiki ta kwantar da ita tareda rufeta bayan sun bata maganin dasuke dasu yanzu suna boyewa batareda sunsan asalin meyake damunta ba take baccin wahala ya dauketa sbd Acanma saida Wata likita mace tazo ta bata magani da Allurar wani babban lamarin daya samesu.


Koda gari ya waye sbd kawai Sumayyahn ta samu ganin likita a asibiti yasa Benazir da Anne lallabata suka fita makaranta amma kam ko tsayuwa bata iyawa abin harya fara basu tsoro matiqa sbd bata taba zazzabin daya hanata ko iya daga qafafuwanta haka ba.


Suna fitowa ga mamakin Benazir Bilal ne yazo daukansu a qage yake kaman wanda yasan Sumayyahn batada lafiya dan kuwa gabaki daya damuwarsa da rashin sukuninsa a bayyane yake.


Da sauri ya fito motar ya budewa Benazir ta sakata baya ta kwantar ita kuma ta shiga gaba suka wuce.


Ba tambayar komai asibiti ya nufa dasu suna isa dayake likatansa ta jiyan ce sunriga sunyi magana karban sumayyan kawai akai aka daura mata ruwa da allurai dakuma sauran abubuwan dasuka bi baya.


Benazir bata taba ganin damuwa ko rashin sukunin Alh Bilal din ba sai yau duk da ba wani kallan mutane sukeyiba bare su tsaya karantar yanayinsu amma na yau din a bayyane damuwarsa take.


Wani irin tattali da kulawa tareda kauna mai tsananin gaske yake nunawa Sumayyah yana asibitin har ta dan farfado guraren 12 na rana,


Lafiyayyun abinci kala kusan uku aka kawo daga Kaante H&S 

Benazir ce ta bawa Sumayyah abincin tasamu taci kadan dr zulfa tasaka wata nurse ta shiga da Sumayyahn toilet ta taimaka tayo mata wasu yan dubarun sai gashi sumayyar ta dan samu qwarin jikinta daga nan tayi sallah tana idarwa Wani baccin ya sake daukanta lokacin jikinta ya dan warware ba laifi.


Anan suka wuni daga ita har Bilal din wanda ya kasa ya tsare bai matsa koina ba saida yamma tayi ya dawo dasu gida kaman ya cinye Sumayyan da idanuwansa masu haske da kaunarta 

Ita kuma takasa koda dagowa ta kallesa sbd Halinda zuciyarta da gangar jikinta sike ciki.


A gidan ma haka ta daure tana nuna kuzari da samuwar dan sauki sbd hankalin Anne da sumayyah ya kwanta.


Washe gari Benazir nada wata test dinma dan haka Bilal dake neman dama ya samu shi kadaine yayi jinyarta cikeda so mai tsanani da kauna tareda kulawa kaman ya mayar da ciwon jikinsa.


Dayake iya su biyu ne ranar kuka ta ringa masa zuciyarta cike da qunci saidai shima zuciyar tasa bata cikin dadi sai damuwar amma haka ya ringa lallabata harta dan warware sukai wunin cikin kulawa suka gama da yamma ya biya ya dauki Benazir suka koma gida.


Cikin kwanaki kusan bakwai shine yake jinyarta a sirrance harta warke sosai ta koma lafiya kalau hakama a daidai wannan gabar ya riga ya tabbatarwa da kansa aurenta koda zai dauketa ne subar qasar bada sanin kowa ba amma tabbas sumayyah tasa ce wlh babu me aurar masa ita.


Ita kanta sumayyahn a yanzu da qaddara ta kaisu wani matakin zuciyarta ta sake jarabtuwa dashi,

Yanda suke jin junansu fiyeda tinani cikin ransu. 


Kulawarsa akansu ta qaru fiyeda koyaushe hakama yafara shirye shiryen yimusu passports dukkaninsu su ukun.


Sumayyah da benazir aka fara yiwa sbd zuwa lokacin ya sanar musu da manufarsa ta daukesu daga hannun Ababa zasu bar qasar zai kaisu inda zasuyi rayuwa kuma kafin su bar qasar yanason a daura aurensa da sumayyah din dan tini ya tanadi masu daura musu auren manyan malamai na mutunci.


Hoton Annensu akeso da thumbprint amma an rasa mafita saidai daga baya ya bawa Benazir camera a boye cikin dakinsu suka shirya Annen da Hande ta fita da rana sukai mata hoton sai bayan azahar suka tafi makaranta ranar sbd hoton kawai suna fita suka basa kuma cikin saa hotunan sunyi amma sam bazasuyi abinda akeson ba dan haka dole sai anyi dabarar fiddo Anne a gidan.


Anata wannan process din Tafiya ta kamasa dan haka yabar komai ga aje saiya dawo sbd case din DD ne da Dad dinsu sam yaqi dawowa gashi bayan zamansa 'dan Kaantes business partner dinsu ne sbd ya zuba hannun jarinsa sosai a kamfanoninsu dan haka shares dinsa a kaantes suna dan da kauri kadan duk da suma akwai tarin abar.*_PHYDOORS FOOD AND MORE_*💯🔥


*_Ina masoya Abincin gayu dana gargajiya da Sea foods? Ga ingantattu kuma tsaftattun kayan Phydoors Sea foods and more da muka tabbatar da dadi, kyau, inganci da tsaftarsu tareda saukinsu._*

*_Uwar gida, Amarya shin kun taba aikin Abinci da kayan Phydoors sea foods and more kuwa?_*

*_Idan baki taba ba ina shawartarki da gwadawa sbd a take zaki gano bambamci da kuma damar Girki masu dadi da ingancin da suka wuce ki._*


_*Phydoors sea foods and more Suna tare daku a koina sbd suna aika kakansu koina a duk Inda kikeso cikin tsari da packaging mai kyau da kulawa hakama ga sauki da Ragusa,Akace siyan na gari maida kudi gida.*_


*_Phydoors food and more is a food branded based in abuja and offered national wide delivery of her items, available food stuffs are stone free crayfish , egusi, palm oil, plantain powder in kg, prawns 🍤 , fried kpomo, some from as low as 2k._*

*_Contact her through this line 08062181151 or DM me let’s do paired order for minna and suleja. She’s based in abuja._*

_*Or visit her instagram handle*_ @ _Phydoors_Food_
***Bayan tafiyarsa sai sumayyah tayi sanyi sbd wani irin sabo da shaquwar da sukai kusan kullum saiyazo makaranta ya dubata da kulawarsa,


Ms aysha ma zuwa lokacin ta zama kaman wata uwarsu sbd sosai take hana kebawar Sumayyahn da Bilal dan ganin yanda yake tsananin santa kuma gashi akwai 'yar rayuwar turai a tare dashi kada barna ta shiga.


Benazir kuwa karatinta takeyi bil haqqi hakama Nasir itama a nata bangaren tana jinsa cikin zuciyarta amma kuma bata taba jin zata iya tsayawa ta kulasa sbd Ababa da sharadinsa tareda gujewa babban masifar da zata biyo bayan ganewarsa Ababan.


Da wayar ms aysha kullum yake samun magana da ita har dai yayi dan busy ya rage kiran sai dare yake samun time kuma lolacin yasan ba lallai tana tareda ms aysha ba dukda time ba daya ba.


****Acikin sati uku zuwa hudu da tafiyarsa ramar sumayyah ta bayyana sbd yanda bata iya cin abinci sai iya na gidansu da ake basu bata iya cin wanda ake kawo musu daga Kaantes,


Gabaki daya tayi sanyi ta dena kuzari,Annensu data ga hakan ta dan ringa lallabata itada benazir a boye ba halin nunawa,

Makarantar daurewa kawai takeyi tana zuwa sbd kawai samun yin magana dashi a wayar ms aysha amma sam ko fita batason yi.


Aikin wahalarsu na gida kuwa kusan akan Benazir ya dawo sbd sumayyahn data fara yanzu rawa jikinta yake dauka sai jiri.


Tin Benazir da Anne basa lura har suka fahimta sosai take hankalinsu ya tashi sbd tsoron idan wani ciwon ne ya shigeta tinda yanzu ta koma yau lafiya gobe ciwo.


Maganin zazzabi da paracetamol suka ringa bata a boye sbd kada ciwon koma wane iri ne yayi mata karfi gwara ta warware kafin Ababa ya sani ya hadasu ya hukunta sbd ta dena aiki sai yakusa dawowa ta fito dan karya gane.


Tin suna boye ciwon Sumayyahn daya fara qarfi sbd koyaushe a zazzabi da jiri take makarantar ma ta dena zuwa har Hande ta gane tayita masifa tana qarawa daga qarshe dole suka ringa saka sumayyahn warewa tayi yan wasu ayyikan sbd kada Ababa yaji ya tsananta mata aiki.

#MAMUH#

#BENAZIR ABABA#DD KAANTE#LITTLE BENA Amnah#HotHot#marriage#love#romance#DBenaZAFAFA BIYAR🔥


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR 'KASHI

Safiyya Huguma


-FURAR DANKO

Billyn Abdul


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at

1487616276

Access Bank 

Bilkisa Ibrahim


Send your Shedan biya Anan👇

09032345899


MTN VTU/MTN CARD/AIRTIME TRANSFER👇👇

09033181070


Zafafa🫶🔥🔥

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post