Zafin Kai page 26 complete by Mamuhgee

 

Zafin Kai page 26 complete by Mamuhgee

*_Arewabooks@Mamuhgee_*

26

Kallan kudin Dake rubuce kan takardar yayi duk da bokonsa bamai zurfi bane Amma sosai yakeda lissafi da ilimin gane lissafi a rubuce a kuma bayyane.


Dubu goma kudin gado" ya sake maimaita karantawa Yana Jin zuwan jikinsa na sake daukan tafasa Dan kuwa Wannan zubin da baisan ko zaiyi kwasa ba dayake yafara cin tsakiyar zuciyarsa ba ruwan jikinsa da jini ba kawai.


Benazir yacira kudin yace


"Kije ki biya kuma wlh duk a lissafe nake ko cikin nan yafita saina ballawa kowaccenku qafa daddaya Kuma wlh Suma kaates sai sun ragemun asara tinda dai anyi cikin Kuma wlh Allah ya Isa zan ringa zabga muku duk ku daidaice tinda kune kuka jamun.


Karban kudin tayi da hannu biyu kanta na qasa jikinta na mutuwa tana fatan cikin nan dai ya tsira yazo duniyar da Babu komai cikinta sai qunci da wahala.


Juyawa tayi ta nufi Inda ake biyan ta biya ta dawo jiki mace ta sake rakubewa ta tsaya Inda take tin farko.


Suna gurin zaman jiran har Akai asuba Ababa ya wuce yaje yayi sallah ya dawo 

Yana dawowa ya tadda Babu wani bayani take ransa ya qarasa baci yahau masifar data Saka nurses fitowa dole suka masa bayanin sumayyahn tayi bacci ne na wahala sbd suna Saka ran ba jini jikinta sai anmata Qari pcv dinta suke jiran akawo su gani da B group dinta.


Su kansu likitocin da nurses din sun so Yi masa fadan yanayin da suka samu sumayyahn sbd akwai yunwa da wahala a tare da ita da rashin jini duk ga Mai ciki amma baa kula da ita ba Saida komai yai tsanani tukuna Amma masifarsa da zafinsa yasa suka bige da kokarin fahimtar dashi abinda yake faruwa Dan kuwa kallo daya zakai masa kasan ransa ya gama daukan zafi sai sukai masa uzurin tinanin damuwar ciwon marar lafiyar yasashi ficewa hayyacinsa cikin masifa.


Benazir na gefe rakube duk abinda yake faruwa Bata Isa dago kai ta kalla ba harya gama fadan akace to gaskiar magana jini ake buqata sosai.


Shiru yayi bayan anbasu takardar kawo jinin Yana sake duba takardar zuciyarsa na nauyi Dan kuwa bayajin bayan dukiyarsa zai iya Bada jininsa Dan Shima Yana buqatan jinin 

Kudin daya kashe sun gama Kone jininsa baida na bayarwa,


Bazai iya Bada jininsa ba yaxo Bai fita ba abin ya masa yawa Dan haka gwara dai idan akwai na siyan ya siya duk zai Saka a lissafi.


Dakin da aka kwantar da sumayyahn aka kaisu,


kallan baqin ciki da zafin zuciya ya ringa jifan sumayyahn dashi ransa na tafasa Amma Baice komaiba ya juya ya fice yabar Benazir gurinta.


Yana ficewa dakin Sumayyah ta Bude idanuwanta dasukai jajir ahankali ta saukesu akan benazir wadda itama sumayyahn take kallo idanuwanta na cikowa da hawaye masu zafi da radadi.


A tare hawayensu suka gangaro daga idanuwansu batareda kowannensu ya iya cewa komaiba sbd sun Kai matsayin da basa buqatan Bude Baki su fada quncin ransu saidai hawayensu su isar da sakon.


Ahankali Benazir takai hannu ta dafa na sumayyah suna sauke qaramin numfashi a tare.


Shiru ne ya ratsa dakin tsawon lokaci Babu mai iya magana acikinsu suna jiran tsammanin Ababa jikin sumayyahn Babu qwari ko kadan.****A gida Tin bayan fitarsu hande taga Anne na Neman shidewa ta debo ruwa Kofi daya ta hau yayyafa mata ba Ji ba gani tana cewa


"Benazir bazaki mace ba ki barni da Renan jikan gaban fatiha bayan na gama naki Renan nayi na 'yayanki,

Maza tashi kece Zaki Rena jikanki tinda kune kukasan ya Akai kuka somosa."


Numfashi da ajiyar zuciya Anne ta hau jerowa tana Bude idanuwanta da Dan qarfi sbd ita kanta bazata so ta mutu a yanzun ba tabar 'yayanta Harma da jikan idan yazo cikin wanna masifar su kadai tanason kayanta,jikan ma na gaba da fatihar tana sonsa ahakan tinda Allah ne ya qaddaro musu hakan Kuma sun karba.


Hande wurgi tai da kofin hannunta tana wucewa cikin masifa da cewa


"Tinda kukayo cikin nan kuka hanamu samun zaman lafiya a gida Nan,

Duk Kun zautar mun da 'da ya haukace ba dare ba Rana magana yake shi kadai da Kansa duk akan cikin nan,

Gashi yanzu Yana musu Barazanar yunwar da Babu ranar dawowa daidai idan aka rasa cikin,

Benazir aurenki dai ba Alkhairi bane ga Ababa tin kuruciya har girma Bai ganewa komai akanki ba".


Sai alokacin wasu hawaye masu dumi da zafi suka gangarowa Anne ta dafe zuciyarta Dake Neman fashewa sbd abinda takeji cikinta na tsananin qunci da damuwa.


Kasa komawa daki tayi ta rarrafa ta miqe tsaye ta Isa Inda kujerar tsakar gidan take ta zauna tana dafe kirjinta dake Dan mata nauyi da radadi ta dasa zaman jiransu har Akai asuba tana gurin zaune.


Sai da gari yafara haske ta iya daurewa ta tashi taje tayi sallah ta sake fitowa tana kokarin sake zaunawa zaman jira hande ta fito tana cewa kasheni zakiyi da yunwa kenan bazakiyi abinci ba tinda 'yarki Rai na hannun Allah.


Fasa zaunawa tayi ta nufi kicin tafara kokarin sharewa kafin tafara hura wutan aikin.*****Ababa har qarfe goman safe Yana yawon Asibiti Neman jinin da zaa sakawa sumayyahn Amma Sam baa samu na siya ba hakama shi bazai iya qanqantar da Kansa rokan kowa jini ba.


Ransa ba qaramin baci yai ba,fushinsa sai qara Hawa yakeyi sbd ko ciwo Bai taba hanasa fita nemansa ba sai yau gashi tin asuba Yana gantalin nemawa jikan da a yanzu yafi kowa son zuwansa duniya.


Yunwa ma bayaji sbd a yau ida Bai samu jini ba dole ya Isa KAANTES su Dd babba Aturo Mai Bada jini wlh,

Yaso ya bari sai Alh Bilal ya dawo qasar ya tinkaresa Amma idan har baa samu ba gwara yaje tin wuri kar yayi biyu babu 

Koda Babu me Bada jinin dai su San da cikin ta yanda ko cikin ya matu shikam zai samu abinda zai Maida dukiyar daya rasa.


Koda yadawo dakin daga benazir har sumayyahn idanuwansu a kumbure da kukan dasuka Sha sosai suna ganinsa benazir tai qasa da Kai sumayyah kuwa Dake kwace rufe idanuwanta tayi ahankali tana Jan numfashinta Dake fita daqyar.


Kallan da yayi musu yana Jin inama jinin uwarsu zaiyi da daukota zaiyi a kwashe duka jininta a sakawa sumayyahn da akeda buqatan lafiyanta yanxu.


Kokarin zama yakeyi nurse ta shigo tana fadan baa kawo jininba ana fa buqatansa da gaggawa gaskia.


Cikin takacin rashin sanin abin Yi yace


"Baa samu ba ni nawa Babu yawa bazan iya badawa ba Idan akwai Inda zaa samu na siyan bayan Nan ku fadan nawa ne Kuma nawa ne.


Da mamaki nurse dn ke kallansa Jin wai bazai Bada nasa ba bayan shine mahaifin sumayyahn kaman yanda ya fada.

Ganin kaman zata ma batawa kanta lokaci ne yasata juyawa tana cewa Leda biyu mukeso Kuma ko wanne ka tanadi kudinsa muje Akira aji idan akwai Inda muke saka ran zaa samu.


Miqewa yayi Yana take kafar benazir cikin zafi ya fice daga dakin Yana bin bayan nurse din ransa a bace Jin har Leda biyu bayan yasan jinin mutum sai yayi tsada sosai Kila.


Bayan fitarsa Babu Wanda ya iya motsawa har tsawon mintina kafin sumayyah datasan ba jinin da Ababan zai iya siya a Saka mata bare ma ta rayu,

Hawaye ne suka cika idonta tana kallan benazir data kasa kallanta sbd karyawar zuciyarta yayi yawa.


"Bena" takira sunanta ahankali da wani irin rauni tana Jin karyewar zuciyan itama dan idan ta mutu ta barsu da wahalar da taci alhakinsu.


"Bena ku yafemun ke da Anne....


Kukan da Benazir tafashe dashi ne yasata maganarta karyewa itama tana sakin kuka.


Kasa sauraranta benazir tai ta miqe tsaye tareda barin bakin gadon ta juya mata baya tana kuka mara sauti sbd harga Allah zuciyarta bazata iya daukan rashin sumayyah ba bare Anne.


Ahakan suka ringa kuka har sumayyahn ta dawo tana rarrashin Benazir a hakan sukai shiru dole 

ta dawo kusa da ita ta zauna tana Bata tabbacin zaa Sami jinin da yardar Allah.


******

Ababa kuwa Inda aka Saka ran samun jinin baa samu ba take tashin hankalinsa ya Qaru Dan haka Kai tsaye ya yanke shawarar gwara ayita gaba daya bazai haukace ba a hanya gwara Suma su shigo lamarin.


Securityn Dake masa duk wani mugun bincike da boyayyan aikinsa ne ya kirasa a waya daidai lokacin da ya shiga dakinda sumayyahn take ya rufo kofa.


Wayar yakalla cikin zafi da masifar daya rasa yanda zaiyi da ita tana cinsa,

Ganin Mai Kiran yasashi furzar da numfashin bacin Rai Mai zafi ya dauka zaiyi magana aka rigasa da fadin


"Sir Bilal Kaante ya Sauka kasar yau dinnan A Lagos,

Komin dare yau zai biyo wani girjin ya iso gida".


Tinda aka fara wannan masifar sai wannan lokacin yaji wani sanyi ya Sauka cikin zuciyarsa Yana sanyaya wutar Dake cin zuciyarsa da gangan jikinsa.


Ajiyar zuciya ya sauke a Fili Yana cewa


"Ayau Nima zanga Manyan kaates din da yardar Allah,

Komai na aikina ya zama shirye Ina awa biyar bakajini ba kasan abinda na fada Maka dai."


Kashe wayar yayi Yana juyowa yakalli su benazir Dake jinsa Yace


"Alh Bilal kaante ya dawo

Ayau zanje musan matsayar gaskiar wannan maganar,

Kuyi adduar komai ya tafi daidai idan ba haka nadawo kisan ku zanyi naje gidan yari Nima ba huta da masifarku data isheni.


Juyawa yayi yafice dakin batareda ya waiwayosu ba bare tinanin suna buqatan abinda zasu Dan sakawa cikinsu.


Yana fita Kai tsaye gida ya nufa Dan yin wanka ya sauya kaya zuwa shigar alfarma Dan koba komai ta yanda zasu San lafiyarsa kalau ba mahaukaci bane yaxo Yana karanta musu hauka.*****Barinsa asibiti da kusan awa daya suna zaune jigum jigum cikin fargabar abinda zai biyo baya idan aka samu matsalar da Alh Bilal ya gaddada cikin,

Faduwan gaba da tashin hankalin dasuke ciki ya hanasu Jin yunwa,

Musamman sumayyah datafi shiga tashin hankalin me Bilal din nata zaice.


Kofar dakin nasu Akai knocking ahankali tareda budewa aka shigo cikin sanyi da nutsuwa

Take atmosphere din dakin ya sauya gabaki daya da wani irin qamshin luxury turaran _CARON POIVRE_ na DD dayake amfani dashi kwana biyu yayi tare dashi akan zasu dawo qasar tare Amma wayar sulaiman daya saka bibiyan motsin su Benazir yasashi dawowa Bai jira DD ba dazai dawo tareda su umminsu.


Qamshin yasa sumayyahn kasa gane shi dinne Kai tsaye sbd wannan ba qamshinsa bane kwata kwata da Suka saba Ji.


Ganinsa a tsaye Yana kallansu zuciyarsa na karyewa yasa daga sumayyah har benazir fara hawayen da suka kasa tantance na farin cikin ganinsa ne kokuwa na murnar sumayyahn tasamu Mai Nemo mata jinin da ake Neman.

#MAMUH#

#LOVE#LOVE#ROMANCE#DD#BENAZIR

#LITTLE AMNAH KAANTE

#ZAFIN KAI#MAMUHGEE

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post