Zafin Kai page 31 complete by Mamuhgee

Zafin Kai page 31 complete by Mamuhgee

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

31

Dd babba tinda ya dawo hayyacinsa numfashinsa da bugun zuciyarsa Daya dawo daidai ya farka Bai ko Kalli gefen da Bilal yake ba sbd Sam ko ganinsa baya son Yi Dan ciwonsa zai iya dawowa harma fiyeda na farkon,


Duka yayansa da daidaikun jikokinsa da suka samu zuwa babu Wanda baiyi kokarin son sanin meya kawowa dd din samun attack a take bayan kowa yasan lafiya yake,

Hakama dad kaante da ko a yammacin ranar sunyi waya lafiya kalau baisani ba Kuma baiji alamar damuwa ko Wani ciwon a yanayin dd babban a lokacin ba.


Dan haka suketa shiga damuwa da mamakin Abinda ya samesa Amma Sam yamaqi yarda ya bayyanarda ko kafa Daya dazata bayyanarda akwai Wani abin ya sanar dasu zuwan kaddara ne kawai Allah ya Aiko masa da attack din.


Dole kowa ya bar zancen aka Maida hankali gurin kulawa dashi sosai.


Bilal Daya fahimci ko kallansa dd bayayi sai jikinsa ya sake mutuwa yayi sanyi ya sake shiga damuwa da mutuwar jikin yanda zancen zai bayyana ga sauran familyn.Kwana biyi dd yayi a Asibitin ya sa aka sallamosa suka dawo gida a qarasa jinyar a can duk da zuciyarsa ba saukin zata samu sbd shi kadaine yasan tsananin zafi,bacin Rai,baqin ciki da damuwan Dayake ciki akan babu Wanda yasani daga shi sai Bilal sai Allahn su.Bayan dawowa da jinyar dd babban gida sosai kaantes ke karban baquncin manyan mutane masu riqe da qasar dake zuwa duba dd daban daban,

Dan haka har lokacin dd Baiyi lokacin Bilal ba.


Babu Wanda ya fahimci Wani Abu ko rashin kulawan da dd babba kewa Bilal sbd anriga an Saba da sanin babu wata shaquwa Mai zurfi Ra girma tsakaninsu Dan haka babu Wanda ya ankara da rashin kulasan da dd babba kewa Bilal din.
Damuwa tasako Bilal din gaba sbd babu inda a yanzu yakejin saukin rayuwar,

Komai ya lalace masa ya tsaya masa cak,

Mahaifiyarsa da DD ne farin ciki da sanyin idanuwansa sai 'yar qanwarsu

Gashi duk Basa tare dashi.


Sumayyah Kuma Ababa ya hanasa zuwa ganinta yace sai dd babba yaji sauki asan matsayar magana.


Ababa ya Hana Bilal din zuwa ne sbd rashin zuwansa yasa yake aikowa Ababan kudi kaman Bai San zafinsu ba Dan kada sumayyah dasu benazir su nema komai su rasa na kulawa da baby da lafiyan sumayyahn.A bangarensu benazir kuwa a yanzu da babu zabin Daya wuce musu karban ciki su hau renansa su Haifa komai menene yazo duniyar yasa suka Maida hankali gurin kulawa da sumayyah sosai.


A dayan bangaren Kuma a rayuwar da suka Saba suka taso cikinta babu Abinda ya sauya musu.


Wahalarsu,bautarsu,qunci da damuwansu babu Abinda ya ragu ko aka dauke musu.


Aikin a yanzu ma yafi na ko yaushe ga benazir sbd wankin shagunansa duka itace take yi hakama ayyukan gida da kulawa da dabbobi

Ga karatinta Dayake baya sbd rashin lokaci da wahalarta data qaru Dan haka duk ta forgice tafara ficewa hayyacinta itama ta rame Takoma kaman itace me cikin.


Anne ma ciwon tsufa ne yake Neman kamata ya rufeta sbd ayyukan sun mata yawa da nauyi itama Dana haka daga ita har benazir babu Mai hutun zuciya dana gangar jiki.


Sumayyah data ga wahala na Neman illatasu qarfinsu ya fara gazawa dole itama ta sakawa kanta qarfi da jarumta ta koma kan aikin itama kaman yanda suka Saba a baya.
******Dd babba tini ya warke ya sake saidai ciwon dake cin zuciyarsa Bai warke ba ko kadan 

Tin ranar da abin yafaru baya iya bacci kowane dare tinanin yanda zai kashe zancen yayi Rami ya birne ya rufe yake,


Fushinsa da Bilal Yana qaruwa ne a duk lokacinda ya Tina cikin Yana girma ne yana sake kusantar lokacin haihuwa.


Danne zuciyarsa dd babba yayi ya sake Neman Ababa wannan Karan da Kansa ya gayyatosa Dan suyi magana.


Da qarfe 7 na bayan magrib ya iso Dayake Abbakar ya San da izinin da dd babba ya bayar na ganin Ababa yasa yana babban gate din farkon har Ababa ya iso da Kansa yayi masa barka da zuwa yayi masa iso.


Wannan Karan ma Ababa gidan sake shiga ransa da qwaqwalwansa yake Amma Dayake yafara hangowa Kansa dahir na zamowa Shima Dan haka ya Maida hankali kan dd babba da zai Gani.


Har cikin palon baqin dd babba Abbakar ya rako Ababa ya nuna masa gurin zama ya juya ya fice Dan tsare kofa sbd duk tsananin babu Wanda zaiji me dd babba zai tattauna da Ababan ko ganinsa dd babba yace kada ko Daya a ahalin suyi,

Magana ce zaiyi dashi sukai karshe a rufeta batareda kowa yaji ko yasan komaiba Koda tsautsayi.Numfashi Mai sanyi da nutsuwa dd babba yayi kafin ya amsa gaisuwar da Ababan ke masa tareda ya karfin jiki.


Bayan ya amsa dagowa yayi ya Kalli Ababa da nutsuwa tareda son nufar maganarsa Kai tsaye,

A natse yafara da cewa


"Malam Ababa daga Kai har mu bama buqatan maimaita zancen baya mara Dadi da bacin zuciya Dan haka Ina Mai baka hakuri da Abinda ya samu yarka,

Allah ya tsare gaba ya yafe musu damu gabaki Daya,

Maganar ciki Dayake jikinta Kuma aikin kaddara ne data Riga fata Dan haka dai Ina sake baka hakuri.


Shigowar Bilal ne Daya saka Abbakar kira masa yasan ya shi dagowa a Karan farko yayi masa Wani Kallo ya Basa izinin zaunawa Shima.


Cikin sanyi da girmamawa Bilal ya gaida Ababa da tini ya fara Jin Kansa Wani ya amsa cikin yar kamewa.


Kallansu su biyun dd babba yayi kafin ya sake Dan yin shiru zuciyarsa cikeda nazari da Abinda ya Yanke akan lamarin Dan haka ya kallesu Kai tsaye ya sake fara da tambayar watannin cikin zuciyarsa na daci.


Ababa ne ya amsa Shima Kai tsaye da fiddo takardar scanning din dake aljihunsa ta cikin ya miqawa dd babban.


Kallan takardar yayi batareda ya amsa ba mamakin Ababa na fara shiga ransa sbd zuwa yanzu babu Wani ciwo ko baqin cikin lamarin a tattare da uban da 'yarsa ke dauke da cikin da bana aure ba.


Bai karbi takardar ba ya buqaci sanin watannin cikin kawai.


Bilal ne ya amsa masa Kai tsaye cikin sanyin jiki sbd sanin dd din baya son tambayar da yayi Maka dabam amsar da zaka Basa daban.


"Wata shida cikin yanzu Inshallah"


Shiru palon ya sake dauka Dan kuwa dai ta tabbata cikin haihuwarsa zaayi.


Ababa dd ya kalla yace


"A yanzu tinda qaddara ce ta shigo babu Abinda zamu iya Yi face zamu Bada muhalli,kudi da rayuwa me kyau da uwar da Abinda zata haifa inshallah bazamu gasa ba har lokacin da uwar zata samu miji tayi aurenta Amma bazamu karbi Abinda zaa haifa ba,

Komai ake buqata har Wanda baa buqatan ma zaa Baku.


Maganar dangantakar ciki da kaantes kuwa Sam babu maganar,

Ba'a ma yita ba,Bata taba yinta ba zancen anrufesa anan karya taba fita har abada...


Daga Ababa har Bilal cikin rashin hankali da firgici suke kallan dd babban sbd babu Wanda ya taba tinanin zaice a rufe maganar 'dan mutum har abada kar a sake tayarwa hakama shi Bilal tayaya ake tinanin yayi rayuwa ya binne zancen har abada bayan Yana sane da Yana 'da ko 'ya?

Tayaya ma zai iya rayuwa ba sumayyahn da Abinda take dauke dashi nasa?


Ababa Wani zazzafan zufa ne ya yanko masa ya Bude baki cikin maqoqon baqin ciki zaiyi magana dd babba ya katsesa da cewa


"Miliyan nawa?"

"In nairas ko in dollars?

"Cash ko wiring?


Rikicewa Ababa yayi Wani zufan na keto masa Tako ina

Take bayanin yake Neman qwace masa Jin bayanin ddn.


Hankali tashe Bilal yake kallan Ababa Yana jiran bayanin amsar da Ababa zai Bada Dan kuwa idan har shi din Uba ne bazai zabi kudin banza akan farin ciki da kare martabar yarsa ba harma da rayuwarta ta gaba sbd Yana karban kudin ya yarda da har abada bazai alaqanta cikin ko babyn da sunan kaantes ba.


Nazari Ababa ya shiga zuciyarsa na tsalle tana rikicewa,

Saidai Kuma duk son kudinsa a lissafe yake Shima,

A yanda yasani Kuma a yanda Alh dd babba da Kansa ya Basa zabin nawa yakeso da Kansa ya tabbatarda ko miliyan nawa ya fada Basa zaayi,


To Amma idan ya karbi miliyoyan kudin qarewa zasuyi komai daran dadewa sabanin idan ya tsaya tsayin Dakan da 'yarsa da jininsu ta shiga ahalin to famfon arzikin samun kudinsa bamai yankewa bane har sai inda arzkin kaantes ya tsaya.


Dan haka take ya fizgo hankalinsa ya dawo hayyacinsa daidai ya Hana Kansa zaban kudin dayasan ko agurin Bilal zai ringa yagarsu gwara dai ya shiga kaantes tsundum ayi dashi Shima.


Dagowa yayi ya Kalli dd babba dake kallansa tini Yana sake nazartarsa take ya gano akwai kwadayin arziki a tattare da Ababan Amma bari ya tabbatarda halinsa ta hanyar zabinsa tukuna.


Zufa Ababa ya share da handkerchief dinsa sbd a rayuwa bai taba shiga tsaka me wuyar zabi ba irin wannan ranar,

Dollars fa akace zaa sallamesa dasu

Amma Kuma akace idan zaka Sha giya ka Sha ta dubu,

Gwara ya shigo daga ciki saiyafi samun manyan dololin akan wainda zaa qirga yanzu a Basa.Numfashi ya sake ya Kalli dd babba yace


"Ranka ya Dade kudi bazasu Hana bayyabar zancan Nan ba har abada sbd mutum zaa haifa Kuma dole wataran sai Anso sani kokuma sanin ma waye asalin Ubansa duk da kasancewarsa Dan kaddara".


Me zai Hana idan adalci zaa mun Nima Amin yadda akaiwa iyayen mahaifiyar shi Alh Bilal din...........


Cikin Wani mummunan tashin hankali da bugawar zuciya Bilal da dd Daya kasa gasgata Abinda kunnuwansa suka ji masa suke kallansa cikeda mamakin Da hankalinsu duka ya kasa dauka.Ababa kuwa ganin ya buga daidai kan ga'ba yasa ya sake Jin karfin zuciya dana hali Dan kuwa gwara suyi su gama a rufe babin su fada babin gaba.


Ganin duk sun dauke wuta yasashi sake Dan gyara zama yaci gaba da cewa


"Ayi hakuri ranka ya Dade Nima a bani adalcin daya kamaci 'yata da ni Nima,wlh Banda inda zan saka kaina idan aka barmu da wannan Abinda zaa haifa din.


Ni kaina bazanzo a sani ko aji haihuwar kaddarar da zaayi a cikin gidana ba Amma idan aka haihun babu Wani lullubi da zaayiwa zancen dazai hanasa fita har abada,


Kaddara ce hakuri zamuyi mu dauka a rufawa juna asiri kaman yanda babu Wanda yasan waye Alh Bilal haka Nima idan aka rufa aka karba 'yata har abada wlh nayi alqawarin babu Mai ji.


Yana Kaiwa karshen zancen ya sauke nannauyan boyayyan numfashin karfin zuciyar Daya maqalawa Kansa ya iya furta kalaman a gaban dd babba sbd yasan ba qaramin ganganci Mai hade da ban mamaki yayi ba saidai wannan sarar kawai zai aikawa dd babba a karbi yarsa ba wahala.

#MAMUH#

#KAANTES

#ABABAS

#FAMILIES

#MARRIAGE

#CONTRACT

#CRAZY IN LOVE

#LTRIANGLE

#ZAFIN KAI

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post