Halin Da Mutane ke Shiga Sanadiyyar Tashin Kayan Abinci

 

FOOD STUFFS

Tsadar yayuwa al’amari ne da ya shafi ƙasar nan da ma duniya baki daya.

Idan aka kwatanta da shekaru goma da suka gabata, tsadar rayuwa a Najeriya a 2023 ya fi yawa.

Abubuwa sun yi tsada fiye da shekaruun bayaa, kuma alumna da daama ba su sami Kari a cikin kuɗin shiga ba.

Adadin kuɗin da mutane ke buƙatar kashewa kan kayan masarufi ko ayyuka ya ƙaru wanda ya bambanta daga wuri zuwa wani.

Anfi samun tsadar rayuwa a birane fiye da yankunan karkara. 

Bayan cutar korona Kasashe da dama suna fuskantar tsadar rayuwa.

Matsakaicin kuɗin da iyali na mutum huɗu ke kashewa a wata shine ₦1,109,034, kuma matsakaicin kuɗin mutum ɗaya a kowane wata kusan ₦310,669.

Tafiyar da gida yana tare da wasu bukatu banda haya.

Adadin kudin haya da ake biya a kasar nan ya karu a 'yan shekarun da suka gabata.

Karin farashin abinci na daya daga cikin batutuwan da suka fi damun al ummar kasar nan a shekarar 2023.

Daga cikin abunda ke kawo tsadar rayuwa a kasar nan shi ne yadda gwamnaticin jihohi dana tarayya ke kashe kudade fiye da kudin shigar su.

Fadduwar darajar Naira ya kara haifar da dagulewar al’amura da tsadar rayuwa saboda kashi hamsin da kayayyakin masatufi da ake amfani dasu yau da kullum a najeriya shigowa dasu ake yi daga kasashen ketare.

 Manufofin tattalin arziki da gwamnati ta shinfifdaa da kara kudin man fetur suma sun haifar tsundunma alumma cikin tsadar rayuwa da talauci

 manyan basussuka na kasa da kuma karuwar rancen gwamnati, hauhawar haraji a kasar karuwar  rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa.

Tsadar rayuwa yana shafar masu karamin karfi wadanda ba su iya biyan bukatusu na yau da kullum.

Rashin ingantacciyar  rayuwa, Rashin abinci mai gina jiki, da karuwar yunwa da talauci suma manyan kalubale dake addabar alumma a kasar sanadiyar tsadar rayuwa.

Rashin aikin yi yana ƙaruwa sakamakonn kamfanoni sun rage ayyukansu. 

jin daɗin rayuwa yana raguwa sanadiyar rashin iya biyan bukatun yau da kullun, da kiwon lafiya tsakanin talakawa da masu arziki.

Tashin farashin kayan abinci a kasar nan na daya daga cikin batutuwan da suka fi damun yan kasar a wannan shekara ta 2023 da muke ciki.


Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post