____________________Boss Bature✍️
Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakanin su ta zaƙe sai zuba take yi masa kamar aku
"Kin fara period ne❓Kamar daga sama Taji Ya furta, wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruɗe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon juna.
har na tsawon mintuna ba tare da sun kyafta ba, gabanta ya soma faɗuwa, gaba ɗaya ta rasa sukuninta, la66anta sai kerma suke.
Sexy voice dinsa ce ta sake ratsa kunnanta"tambayarki nakeyi, ko ba ki ji me nace ba"? Yawu ta haɗiya kutt kafin tayi ƙarfin halin furta"meyasa ka tambayeni"?
Lumshe idanunshi yayi kafin ya ware su akan fuskarta"naga canji a tare da ke....." ɗan zaro ido tayi da tsantsar mamaki take kallon sa, girgiza mashi kai tay ba tare da ta iya furta wani abu ba
"Tell me the truth, have you started menstruating? I want to know. It's something I've been waiting for a long time." rass Taji gabanta Ya ƙara faɗuwa muryarta na rawa ta furta"ni.. Ni ban..ma san kan me kake magana ba..." cikin dabara ta tafara zame jikin ta daga kan gadon, kwatsam Taji Ya damƙi hannunta, Idanu zare ta kalle sa.
"Ki bani amsar tambayar da nayi maki" wani irin ƙwarjini yayi mata kamar ba man dinta ba, kamar mai jin tsoronsa ta furta"na fara, tun ranar da mukaje dinner din prime minister, amma ya ɗauke, a washe garin ranar.. " daƙyar ta ƙara maganar, ganin wani kayataccen murmushi gefen fuska daya bayyana akan kyakkyawar fuskarshi, hatta dimple dinsa sai da ya lotsa...
"Amma tayaya akai kasan alamomin mace idan tafara period? Sannan meyasa naji kace abu ne da ka daɗe kana jira"! Aruɗe ta jefa masa tambayar saboda abun ya ɗaure mata kai.
Matsawa yayi kusa da ita da sauri ta zame hannunta daga ruƙon da yayi mata, taja da baya kamar taga wani mugun abu.
"Kamar yadda na faɗa maki, naga sauyi atare dake..." abun da ya sanyata aruɗani yanayi da tagani atattare da shi, ga wani annurin farin ciki daya wanke fuskarsa.
"My man, Ya kamata na tafi tun da na kawo maka abincin, su aunty ummi suna jirana" adabarbarce tayi maganar jiki na 6ari ta sauko daga kan gadon daƙyar ta saci kallon shi suka haɗa ido"pls kada ka zauna da yunwa, idan ka kammala cin abincin ka yi wanka, ka sanya sutura a jikin ka, sannan pls ka daina kaɗaita kanka aɗaki ka dinga fitowa wurin su Haris...." tana magana tana ja da baya, tana kaiwa bakin kofar da sauri ta buɗe ta fuce daga gudu.
Sai da ta 6ace ma ganin sa, kafin ya kau da idonsa daga kallon ta, kasa cin abincin yayi saboda bashi Yake buƙata ba, akwai wani abu da zuciyarsa take muradi, sai dai yasan ba abune mai sauƙi Ya same shi ba, wata irin kasala ce ta baibaiyeshi cikin sanyin jiki ya kwantar da bayansa kan mattress din, haɗi da lumshe idanunsa.
Nannauyar Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke bayan ta sauka downstairs, Hannun ta ɗaya dafe da saifin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face kalamansa da suka tsaya mata arai, yayi matuƙar bata mamaki bata ta6a tsammanin Danish Yana da wayau har haka ba, ko tayaya akai yasan alamomin mace idan ta balaga"!? Ta jefa wa kanta tambayar da bata da amsarta..wucewa dinning tayi zuciyarta cike fal da tunanin sa...
_____________________________✍️
Da marece Hajiya saratu tana a gym room na gidan, cikin shiga ta activewear black colour riga da short dai dai gwiwarta, A hankali take running kan threadmill, ta haɗa uban gumi kan fuskarta da jikin ta.
Maganganun da suka tattauna da su zahra ne suka fara dawo mata akanta, Abun Ya tsaya mata aranta, tun bayan tafiyarsu take ta tufka da warwara, tana matuƙar son taimaka masu, but how? Tasan owais mai biyayyane agare ta, komai takeso zaiyi mata, sai dai bata jin girman kanta zai bari ta nemi alfarma agurinsa Kuma bata jin zata iya taka kafarta zuwa gidansa.
"Me ya kamata nayi"? Ta jefa ma kanta tambayar, Farat ɗaya ta tuna da hajiya laurat! Ita kadai ce zata Iya bata shawarar daya dace.
Fitowa tayi daga gym room din ta nufi part din su.
Tana shiga daki, ta nufi toilet ta shiga, within 15 mins, ta fito sanye da bathrobe, ta zauna kan mirror chair, phone dinta ta dauka ta danna ma hajiya laura kira
Sai da kiran ya kusa katsewa kafin hajiya laura tay picking
"Matar yaya barka da marece?ya kike"? Ta faɗa da murmushi akan fuskarta
On the other hand Hajiya laurat tace"Amarya kuma uwargida a wurin praving, lafiya lou, fatan kema haka..."
jinjina kai ta ɗanyi kamar tana agabanta
"naji kinyi shiru? Faɗamin meke damun ki? Don tunda naga kiranki a irin wannan lokacin raina Ya bani wani abu na damunki"
"Shawara nakeso Ki bani...." ta faɗa kamar bata son furta maganar, A hankali ta zayyana mata komai dangane da zuwansu zahra...
"Bansan Ya zanyi ba! Nayi masu alkawarin zuwa gobe zasu ji kirana, nasan sun kwallafa rai, ni kuma Allah bana son in nemi alfarma awurinsa, nasan owais yana da biyayya zaiyi min abun da nakeso amma ina jin nauyin zubda ma kaina mutunci..."
Sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya cika kunnanta, nan take ta haɗe rai"bana son iya shege, Oh dariya ma na baki? tun da bazaki bani shawara ba, zan kashe kiran"
Da sauri Hajiya laura tace"Am sorry hajiya, kin bani mamaki ne! Kamar kina jin shakkar tunkararsa, Ki aje wani jin kai gefe ɗaya, Yaron nan ɗan yayanki ne, kuma ɗanki, kina da iko da shi, ba alfarma zaki nema a gurin sa ba! abun da yakamata shine Ki bashi Umarni, kiransa zakiyi awaya kice mashi yazo inda kike Ya same ki, Idan Yazo ki zauna ki faɗa masa komai sannan kice mashi gobe zasu zo ganin yarinyar, baki bukatar wani abu da zai sa girmanki ya zube a idon su...."
tiryan tiryan hajiya laura ta tsara mata komai, tunkafin ta karasa maganar, Hajiya saratu ta fara sakin murmushin gefen fuska, saboda shawarar tayi mata 100% shiyasa take ji da hajiya laurat, matar karshe ce wurin Iya bada shawara..
"I can't thank You enough, Hajiya ta, nagode da shawararki, shiyasa yayana Yake ji dake saboda kin Iya tsara kalami ga iya bada shawara...." sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya karade kunnanta
Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"nima naji dadi da kika dauki shawarata, Yanzu faɗa min Ya ake ciki game da hajjaty? Har yanzu baki gano komai ba"?
Ta6e baki hajiya saratu tayi"Hmm Matar wayon tsiya gareta kamar dila, yarinyar dana sanya tana yi mata leƙen asiri, har yanzu bata gano komai ba, amma tace min tabbas akwai wani abu da take kullawa adakinta, saboda bata son kowa Ya shiga...."
Hajiya laurat tace"munafuka, ay daga ganin ta zatai wayau, kuma wallahi ba wayanta bane akwai wanda ke ɗaurata akan hanya,..."!
"Kamar ya bangane me kike nufi ba.."?
"Ina nufin ba ita kadai take shirya plan ba, akwai wani dake taimaka mata..." da tsantsar mamaki hajiya saratu take sauraronta, tabbas Ta yarda da kalaman hajiya laurat saboda matar tana da kaifin basira...
Sun jima suna tattaunawa akan hajjaty kafin daga bisani su ka yi sallama.
______________________________✍️
Kusan atare motocin su suka kunno kai cikin estate din,
Bayan sunyi parking, Pravin Ya fito cikin shiga, ta suit, Ya jingina bayan shi jikin motar, Idanunsa akan motarsu twins dinsa, fitowa sukayi kowannansu Ya dauki wankan suit, sun kwaso gajiyar aiki sai faman lumshe idanu sukeyi
Tunkarar shi sukayi da sauri shima Ya nufe su, gaba ɗaya ya hadesu Ya rungumesu, tare da daura hannayensa abayansu.
"Yau mun dawo gida atare, ya gajiyar aiki" dagowa sukayi atare suka dube shi
"Daddy Ba dadi, wallahi, na gaji, ni fa kasan bana son wahala.." zayn ne yayi maganar,
Zaid Yace"Alhamdulillah daddy, kaima ya gajiyar naka aikin"?
Murmushi yayi kafin yace"ay ni bana aiki, ina da masu yi min komai, illa Iyaka in karshen wata yayi in kwashi Albashina...." kallon juna sukayi da mamaki akan fuskokin su,
Ko ajikinsa Yaci gaba da fadin"tuntuni naso In wayar maku da kai amma kuka ƙi yarda, Kunfi so ku yi ta wahala akan albashin da bai taka kara ya karya ba, har atm dina na baku don kuyi irin rayuwar da kukeso amma kuka ki kar6a saboda baku yarda dani ba ko.."
Shiru sukayi suna kallonshi, kafin Zayn yai kafin halin cewa"daddy ta yaya zamu kar6i kudinka? Bayan ba halal dinka bane!! Baka aiki kuma kana kwasar albashi, hakan na nufin haramun kake ci, daddy kaji tsoron Allah, ka riga da kasan hukuncin wanda Ya gina kansa haram..." bai ƙare maganar ba, Pravin yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga mashi hannu, da kakkausar murya ya furta"Enough! Don't you dare repeat what you just said to me!! Gidan ubanwa nake cin haram? duk wani kuɗi da nake da su, Hakkina ne ina da goyan bayan waɗanda suka ɗaura ni akan muƙamin da nake da shi. ..." Yana faɗin hakan rai a6ace Ya nufi cikin gidan, da sauri zaid yabi bayanshi tare da shan gaban shi.
"Daddy ka yi hakuri, naga ranka ya 6aci, Dan Allah ka yi hakuri da abun da zayn yace maka! ka yafe masa kada ka ruke sa a zuciyarka..."
Murmushin gefen fuska pravin yayi"kada ka damu my son, komai Ya wuce"
Ajiyar zuciya zaid Ya sauke, Tare da ruko hannun daddyn nasu suka shiga parlour.
Zayn dake kallon su har sai da suka 6ace ma ganin shi, kafin ya jingina bayan shi jikin motarsu, kalaman zahra ya fara tariyowa, a lokacin da ta kira shi Yana a office, ya gama watsewarsa tare da abokiyar aikinsa yana akan network shiyasa Ya zazzaga mata masifa son ranshi aranshi ya ayyana ko sun samu shiga estate din? Ta6e la66ansa Yayi irin bai damu din nan ba, Ya wuce Ya nufi cikin gidan
"CHIEF OWAIS💪💋*
Yana a cikin Katafaren Office dinsa dake a isod Headquater, office ɗin Ya haɗu, an ƙawata shi da high-end supplies komai na cikinsa launin blue sky ne kalar da yafi so, office din Yana da mugun tsaro gaba daya na'urori ne ke sarrafa komai na cikin sa.."
Daddaɗan ƙamshin turarensa Ya gauraya da ni'imtacciyar iskar dake ratsa saƙo da lungu na office din, a yayin da yake azaune kan wata tamfatsetsiyar Excutive chair Ƴar ubansu, Ya ɗaura kafarsa ɗaya bisa ɗaya, daga gaban shi luxury table ne mai ɗauke da High-end computer da sauran kayan amfaninsa dake a baje kan table din
A hankali Ya buɗe idanunsa dake a lumshe, Ya cigaba da operating computer din gabansa,
Adjusting webcam dinsa yayi, kafin ya danna video call Ya dan dakata Yana jira a amsa mashi.
a hankali fuskar commender ta bayyana ta cikin screen din
Murmushi suka sakar ma junansa, Cikin harshen turan ci suka fara magana
"Commander, good to see you, sir," ya faɗa tare da sarah mashi da hannu
"Chief, good to see you too," shima ya sarah mashi.
"What can I do for you?"
Numfasawa chief yai kafin yace"I'm calling to extend an invitation to a high-level meeting in Nigeria, dangane da yaran da kuka damƙa mana case din su" Ya ƙare maganar, Cike da sa ran zai amsa mashi
Jinjina kai commender din Yayi na ɗan wani lokacin Kafin Ya furta" okey, What's the current situation?...bayani ya fara kora masa dangane da halin da ake ciki na binciken prisoners.
Tun da ya fara commender Yake ɗan jinjina kanshi alamar gamsuwa, bayan ya ƙare maganar yace"yanzu wani mataki zaku fara ɗauka"?
Chief yace"That's what we'll discuss during the meeting"
"Tunani mai kyau, zanyi magana da na sama dani, idan har na samu goyan bayan su, zamu halaccin meeting din, yaushe ne kuma a ina za'ayi"?
"Upper week, in Abuja. I'll send over the details. Thank you, Commander..." Ya fada tare da sara ma shi da hannu.. Shima commender din Ya sara mashi
bayan sunyi sallama Ya kwantar da kansa jikin kujerar
"DDG Is coming" Muryar na'ura ce ta ratsa kunnansa, A hankali Yakai idonsa ga duban Glass door ta office dinsa wadda ke kokarin zuge kanta
Big guy ne Ya shigo sanye Cikin kakinsa, Cikin girmamawa Ya sara mashi.
"Sannu da aiki Yalla6ai, Na ji shiru baka fito ba, ko baka lura da time ba ne"? Kallon agogon hannunsa yayi ƙarfe biyar na marece, har time din ta shin sa yayi bai lura ba.
"Have a seat"
Zama big guy yai kan kujerar dake fuskantar chief kamar yadda ya umarce shi
"Munyi waya da commender..." a ƙagare big guy yace"ina fata Ya amsa buƙatarmu"!
Calmly ya zayyana masa tattaunawar da su kai, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar shi"Allah Yasa mu ji alkhairi" Ya amsa mashi da ameen
Shiru sukayi na wani lokaci kowa da abunda Yake saƙawa aranshi
"Ya kamata ka tashi muje in kaika gida, burina ka huta..." murmushi chief yayi"nagode da kulawarka agare ni, Ina boss ko har ya tashi aiki"?
"Tun wuraren huɗu ya koma gida, kasan mutun mai Iyali, ba kamar mu da muke tazurai ba..." da zolaya yayi maganar, harara chief Ya dan watsa masa batare daya furta wata kalma ba
Ya miƙe Ya nufi kofar fita, da sauri big guy yabi bayansa a tare suka fito daga office din.
Tsayawa fasalta haduwar isod headquarter bata baki ne, abun sai wanda Ya gani, lifter suka hau ta sauke su down, ta ko'ina ka kalla Jami'an isod ne sanye cikin kakinsu tun daga senior agents dinsu har izuwa jenior agent, duk inda suka bi cikin girmamawa jami'an suke sara masu, Har suka fito daga headquater din, kaitsaye suka nufi katafaren parking space din su, dankara dankaran motocine makil tare da bikes dinsu killace a harabar.
Da sauri wani agent Ya bude masu backseat na motar da zasu shiga, bayan sun shiga kowan nan su Ya zauna, agent din dake jigilar daukar su Ya yi wa motar key cikin ƙwarewa Ya fara driving dinsu zuwa gida.....
Dai dai lokacin da motar su ta kunno kai cikin gidan, Wayarsa ta fara ringing, lokacin da ya duba sunan mai kiransa yayi mamakin ganin aunt saratu, Cos Ya manta when last Yar tahalikar nan ta kira da sunan tayi magana da shi.
Picking call din yayi tare da kara phone din a kunne, Cikin ladabi Ya yi mata sallah tare da gaishe da ita
Ko sallamar shi bata amsa ba ta furta"Owais, bayan sallar magbrib, Ka same ni a pool yard, Ina son yin magana dakai"! Cike da bada umarni ta furta, bata jira amsar shi ba, Ta katse kiran.
Kurawa screen din wayar ido yayi ba tare da ƙyaftawa ba..."
"Yalla6ai, Mun ƙaraso"! Big guy ne Ya fargar da shi, sam bai lura sun karaso ba, Fitowa yayi da sauri Ya nufi Cikin main falo din gidan
Yana shiga bedroom dinsa, Ya rage kayan jikin shi, Ya shiga toilet domin Yin wanka,
*HAJJATY*
Safa da marwa Take Yi atsakar dakinta, tun safe take sa ran zuwan pravin shuru bai leko ba, Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, saboda abun da ya faru jiya yayi matuƙar daga mata hankali.
Yanke shawarar fita neman shi tayi, da sauri ta dauko mayafi ta yafa akanta, Tana kokarin fita suka ci karo da juna har saida ta bangaji kirjin shi, da sauri taja da baya tare da dafe gefen kanta da hannu daya
"I'm sorry wifey, Ina zaki je ne"? yayi maganar yayin da yake nufar cikin dakin idanunsa akan fuskarsa
From head to toe Ya kalle ta, farat ɗaya ya gane akwai wani abu dake damunta, da alama ko wanka batayi ba.
"Baki da lafiya ne" ya yi maganar tare da ruƙo hannunta suka zauna gefen gadon ta
"Baki ji ina magana ba? Fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan kafadarshi
Hankalin shi yayi matuƙar tashi jin kukan hajjaty, yana daga cikin abunda Ya tsana arayuwarshi.....
Cikin shesshekar kuka tace"pravin ina cikin tashin hankali, Saboda akwai mai bibiyar rayuwata, daren jiya bana acikin kwanciyar hankalina, a tsorace na kwana, ko baccin kirki banyi ba, ina ta jira ka dawo shiru baka zo ba..."
Tuni yanayin fuskarshi Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai,
"Fada min meya faru dake a daren jiya? Wani ya shigo ne"?....ɗagowa tayi da kanta hawaye na sintiri kan kuncinta ta kwashe komai ta sanar da shi...
Tafukan hannayensa ya daura kan fuskarta,A hankali Ya fara share mata hawayen ta
"Ki yi hakuri, in sha Allah koma wanene ke naman ki da sharri kan shi zai koma, Allah Yana atare dake wani bai isa Ya cutar min dake ba! ...." bai kare maganar ba, tace"bansan ya zanyi ba, wallahi ina jin tsoron ranar da asirinmu zai tonu, pravin bana son abunda zaija mu rasa kimarmu da darajarmu a idon mutanan gidan nan, saboda ina ji araina akwai wanda ke son ya tona mana asiri shiyasa aka fara bibiyana.." ta faɗa tana jan numfashi kafin taci gaba da cewa"saboda fargaban abunda Ya faru daren jiya, ko abinci banci ba tun safe har yau kamar mai azumi, wanka ma nakasa yin shi...."
Ta ƙare maganar, tana kallon cikin idanunshi
"Tuntuni saida naso In siya maki gida daban inda zakiyi rayuwarki cikin kwanciyar hankali, amma sai kika nuna bakison rabuwa da su....abunda nake jiye mana kenan...
"Duk laifinka ne, Abunda kayi min awurin dinner din hateem shine Yaja har wasu suka fara zarginmu, kuma ni gaskiya bazan bar gidan nan ba, kawai ka nema min mafita ..."
Jinjina kanshi yayi tare da ruko hannayenta acikin nashi"zan tambaye ki wani abu" daga mashi kai tai alamar toh
"Idan kika kama 6era adakin ki Yana yi maki 6arna, kuma kinsan zai iya haifar maki da gagarumar matsala wani hukunci zaki masa"?
"Meyasa kayi min wannan tambayar"?
"Kedai ki bani amsa"!
Shiru tayi jim kafin tace"hannayen da yake yin amfani da su wurin yin 6arnar su zan naƙasa, sannan in murje bakin shi ta yadda bazai iya daukar komai da shi ba...." murmushi pravin ya sakar mata"kin kawo shawara mai kyau.." arude tace"bangane me kake nufi ba"
Bai bata amsar tambayarta ba, sai cewa yai muje bathroom In taimaka maki kiyi wankan da kika kasa"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da mikewa suka nufi toilet atare almost 18 mins Ya fito dauke da ita a hannunshi, dukansu sun daura towel a waist dinsu,
Taimaka mata yayi ta sanya kaya, shima ya maida nashi
"Tashi ki je kitchen ki shirya mana abinci mu ci atare" amsa mashi tayi da toh,
Bayan fitarta da yan mintuna ta dawo hannunta ruke da try na kayan abinci, ta ajiye masu kan rug, saukowa yayi daga kan gadon suka zauna atare suna ci.....
___________________________✍️
Bayan kammala sallar Magbrib, Owais Ya nufo pool yard din gidan baba obie, Jikin shi sanye da farar jallabiya, tunkafin Ya ƙarasa Ya hango Hajiya saratu zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Hankalin ta na akan wayar hannunta da take dannawa
Cikin kunnanta ta tsinkayi muryarsa"Assalamau alaikum" ba tare da ta kalle shi ba tace"wa'alaikum salam,"
Zukunnawa yayi daga gaban kujerar da take Cikin girmamawa Ya gaishe da ita, Har cikin ranta taji daɗin hakan da yayi mata sai dai bata nuna a fuska ba, wai don kada ya raina ta
"Lafiyalou My son, ina fata Ka wuni lafiya? Ya aiki"?
"Alhamdulillah.."
"Bismilla ka zauna" ta fada tare da nuna masa chair din dake facing dinta, miƙewa yayi bayan ya zauna ya ɗago da ido ya kalle ta, babu alamun zata kalle shi
"Mommy, kince kina son ganin na, zamu yi magana" sai da ta mula ta sha iska kafin tace"eh, magana ce mai mahimmanci, Ina fata zaka bani aron hankalin ka.."
Amsa mata yayi da toh, tsawon mintuna biyar ta shanya shi, kafin ta fara kora mashi jawabi dangane da zuwan su Zahra, da alfarmar da suka nema a wurin ta...." tun da ta fara maganar, Yake dubanta da alamun rudani akan fuskarshi.
"Ita zahran da ta kawo min maganar, tana ɗaya daga cikin interior designers din da suka yi mana aiki aranar dinner din hateem a hall dinne taga yarinyar, sunan yarinyar ta wurinsu Angel amma asalin sunan ta Unaisah, har hotonta sun nuna min, sunyi kama sosai da yarinyar wurin ka,"
Cike da son jin ƙarin bayani yace"ko ta fada maki sunan Baban Yarinyar da sunan mahaifiyar ta"? Shiru tayi tana kokarin tariyo sunan su ....can tace"na tuna, sunan mahaifin yarinyar zaheer tajudeen, mommynta kuma sunanta benazir"
." Bari na kira Daddyn nata, naji idan Ya san su" da mamaki hajiya saratu tace"oh dama mahaifin yarinyar yana atare da ku"?
"Eh," ya bata amsa atakaice, har cikin ranta taji dadin jin hakan....
Phone dinsa Ya curo daga aljihu Ya danna ma Taj Kira, Tana fara ringing Ya saka wayar a handsfree don taji abunda zasu ce
"Yalla6ai barka da marece, Na shigo gidan na taras baka nan.."
"Ina agidan grandpa, zuwa anjima zan shigo"
"Allah ya dawo kai lafiya"
Am so nake na tambaye ka, Wa cece Aneelerh! Kamar na ta6a jin sunan abakin ka"
"Yalla6ai ka kamanta ne halan, matar aminina ce uzair, kamar mahaifiya take awurin Angel ɗina..." murmushi hajiya saratu tasaki jin abun yazo mata cikin sauki
"Zamuyi magana idan na shigo gidan" amsa mashi yayi da toh, bayan yayi rejecting call din Ya ɗago Ya kalli hajiya saratu dake kallon shi
"Yarinyarsa ce..."
"Alhamdulillah, Yanzu gobe da yaushe zasu zo ganin ta? ta tambaya tana kallon shi
"Duk lokacin da yayi miki, su zo kawai" murmushin gefen fuska tasaki, Taji dadin yadda yake bata girma
"Nagode my son, bari nasa akawo mana abun sha" da sauri yace"ina so zan shiga wurin baba"
"Okey, mu tafi tare" mikewa sukayi atare suka jera suna tafiya, abun ba karamin dadi yayi mashi ba, tsawon lokaci basa jituwa da juna, sai gashi silar neman unaisah da yan uwanta sukazo yi Allah Ya haɗa kan su, Har fira ta fara jan shi da ita, a haka har suka karasa dakin baba obie...
Idan muka koma 6angarensu Hajiya Layla dake a asibiti, wuraren ƙarfe 8 na dare, Hospital staff suka fara sallamar mutanan da ke zuwa dubiya, saboda a dokar asibitin karfe takwas na safe visitors suke zuwa da zarar takwas Na marece Yayi kowa zai tafi za'abar majinyaci karkashin kulawar nurses
Hajiya layla tace ita fa ba inda zataje, dole ta kwana don ta kula da yar ta, dr shureim ma ya goyi bayanta, tunawa da barazanar kashe benazir da ake Yi, Idan suka tafi ba lallai nurses su san lokacin da za'a farmake ta ba, duk da akwai cctv camera a kowani daki na marasa lafiya, bayan hakan asibitin Yana da tsaro sosai, kawai dai bai yarda subar benazir ta kwana ba tare da wani nata akusa ba
Hospital staff din basu Yi masu gardama ba, ganin sanannu ne a idon jama'a, kuma da ma ire irensu sunayi masu alfarma, kodan saboda matsayin dake gare su, musamman hajiya Saratu da takasance former firstlady ta kasar, tun da ta sanya baki a maganar suka amince hajiya layla ta kwana tare da ita.
Gaba dayansu sun hallara a harabar ajiye motocin asibitin, Sun fito domin tafiya gidajen su,
Mami da abie suna atsaye, Ga Aneelerh da Zahra da mahboob, Aneeleeh taso abarta tayi jinyar benazir,
"Mu zamu wuce, Ubangiji Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tashi kafadunta, in sha Allah zamu cigaba da tayata addu"a" abie ne yai maganar tare da miƙa ma Alhaji ubaid hannu suka yi musabaha
"Mungode sosai, Allah yakaiku gida lafiya,"
Mami tace"dan Allah duk halin da ake ciki game da rashin lafiyarta ayi kokarin sanar damu"
Hajiya sarah tace"in sha Allah zamuyi kokarin hakan"
bayan abie da mami sun shiga mota, Hajiya layla ta ruko Hannun Aneelerh acikin nata fuskarta dauke da matsananciyar damu tace
"Dan Allah kiyi kokari Aneelerh, Zuwa gobe, Ku tuntu6i iyayen yarinyar da kikace tana kama da yarta, ku rokar mana alfarma awurinsu, su ara mana ita, idan ma suna bukatar mu biyasu kudi su faɗi nawa suke so, ko nawa ne zamu biya, wallahi bana so na rasa benazir, ina matuƙar jin tausayinta...." la66anta na kerma ta ƙare maganar, tuni taji hawaye sun wanke fuskarta
Wani irin tausayinta ne Ya kama Aneelerh, bata san sa'adda itama ta fara share kwallar ba, Yau dai sun sha kuka bayin Allah
"Mommy in sha Allah zanyi kokarin ganin sun bamu yarinyar, Indai akan benazir ne wallahi sai inda karfi na ya ƙare...."
"Pls kukan Ya isa haka, Ku yi hakuri, mu cigaba dayi mata addu'a Allah Ya bata lafiya..." acewar hajiya sarah
Dakyar sukayi sallah da juna, bayan sun aneelerh sun shiga motarsu, A jere motocin suka fuce daga asibitin,
"Zan tafi ba dan naso ba, amma In sha Allah, gobe da wuri zan shigo asibitin"
Fuskar hajiya layla a yamutse tace"Sai Allah Ya kaimu.."
"Duk halin da ake ciki, pls ki sanar dani" ta amsa mata da toh,
"Allah Ya bata lafiya" ta amsa mata da ameen, dr shureim ne ya buɗe mata murfin motar, Ta shiga daga ciki, kafin Ya datse mata, akan idonsu motar hajiya sarah ta fuce daga asibitin
Ya rage saura su uku dake atsaye suna kallon juna,
"Shurem muje ko"? Alhaji ubaid ne yayi mashi maganar, Sam baya son tafiya, Gani Yake kamar in ya tafi wani abu zai faru da benazir,
"Toh daddy" Yayi maganar, Tare da ruko hannun hajiya layla
"Mommy, nasan ko ban fada maki ba, zaki kula da ita, amma inaso ki sanya ido sosai, dole sai kin hana idonki bacci in ba haka ba..." bai kare maganar Ba Alhaji ubaid Yace"meyasa kace haka"?
"Daddy akwai wani abu da nake zargi akan benazir, zan sanar daku amma ba yanzu ba, saboda bana son ɗaga maku hankali, kawai abinda nakeso mommy kada kiyi gangancin kula da ita, in ba haka ba za'a iya samun matsala, duk da munsan Allah ke tsare bawansa amma da bukatar muma mu kula"
Hankali atashe Hajiya Layla ke kallon shi, Muryarta na rawa tace"Shureim dan Allah ka fada min meke shirin faruwa da Benazir dina, ni dama najima ina zargin akwai wanda ke bibiyar rayuwarta, so ake akashe min ita, ko faduwar da tayi a toilet sai da raina ya bani wani mugun abunne Ya faru da ita, in ba haka ba taya za'ace ta fita hayyacin ta? Bata gane kowa dake akanta?..." maganganunsu sunso rikita Alhaji ubaid Ya rasa gane inda zancen su Ya dosa
"Dan Allah kuyi min bayani meke faru ne"?
Da ido Hajiya layla tayi ma dr shureim Alamar yayi shiru saboda tana zargin ba hakanan Aka kyale Alhaji ubaid ba, kada su saki baki su sanar da shi zargin da suke Yi Yana iya zuwa ya sanar ma Alhaji musa, tunda Ya zama kamar ubansa komai zaiyi sai ya nemi shawarar shi
Jinjina kai dr shureim yayi alamar Ya fahimce ta,
"Daddy, Muje gida zan sanar da kai komai" Ya faɗa tare da ruko hannun shi, Hajiya layla tayi masu Allah Ya kiyaye hanya, tana atsaye tana kallon motarsu har suka fuce daga hospital din,
Da sauri ta koma ɗakin benazir, tana shiga, ta iske Nurse agaban gadon ga benazir zaune jikin ta sai kerma Yake tana ta sambatu
"Daddy, mommy, ku kira min taj, Ya kawo min babayna dana bar mashi, dan Allah ku bani ƴata, kada na mutu ban ganta ba...." lallashinta hajiya layla ta cigaba da yi sam bata fahimtar komai, sunan ƴarta da mijinta kadai take ambato,
Har abinci nurse ta kawo mata, kwata kwata ta kasa cin shi, duk yadda mami takaiga lallashinta abun Ya faskara, Addu'oi ta koma tana tofa mata, har dare Ya tsala mami tana zaune kan kujera tana kallon ta, Har dr ya shigo ya kara duba jikinta, Ya bata magungunanta dakyar suka samu ta sha, daga bisani bacci Yayi awon gaba da ita, lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar ishai'a, mami ta shiga toilet cike da zullumin kada wani ya shigo dakin Ya cutar da benazir, saboda ta razana da jin kalaman dr shureim, jin motsin mutun adakin yasa tayi wuff ta bangaje kofar toilet din ta fito tana haki, Ko alwalar bata karasa ba..
*Daga alkalamin Boss Bature mu haɗu next page✍️*
*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*