Watanni 18 Ba tare da Mahaifinmu ba; Kiraye-kirayen Iyalan Mataimakin Shugaban Miyetti Allah Ga 'Yan sandan Najeriya, DSS da Kungiyoyi masu zaman kansu su taimaka gameda Bacewar Engr. Mannir Atiku Lamido, Mataimakin Shugaban Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN).
Watanni goma sha takwas ke nan da bacewar mahaifinmu abin kaunarmu, Engr. Mannir wanda ya bace, ya bar danginmu cikin rugujewa da rashin tabbas. A ranar Juma’a 23 ga watan Yuni 2023 ya tashi daga Katsina zuwa Kaduna, kuma mun yi imanin cewa an sace shi ne tsakanin Zariya zuwa Kaduna.
Duk da ƙoƙarin da muke yi na neman bayanai, munkasance bama barci, kuma mun kasance cikin duhu game da tunanin irin halinda. Bacin ran rashinsa yana da nauyi a kanmu, kuma muna kewar zafinsa, hikimarsa, matsayina nanjagora, mai kishin Al-umma.
Muna rokon hukumomin gwamnati, jami'an tsaro musamman 'yan sandan Najeriya da DSS da su taimaka mana kan wannan Neman mahaifinmu, da masu tausayin jama'a da su taimaka mana a cikin wannan mawuyacin hali. Duk wani guntun bayanai, ko yayane, a wurinmu yanada mahimmanci, zai iya zama mahimmin jagora na neman mahaifinmu da kuma haɗa shi da iyalinsa.
Idan kuna da kowane bayani ko kuna iya bayar da tallafi ta kowace hanya, da fatan za ku zo. Taimakon ku zai iya taimakawa wajen tona asirin bacewarsa da dawo da farin cikin danginmu.
Mun gode ba bada lokaci don karanta roƙon abunda yake zuciya. Muna fatan cewa tare, zamu iya kawo mahaifinmu gida.
Bayanin wannan za'a tuntuba:
- Suna: Abdullahi Balarabe
- lambar waya: 08065694352
Kwanan Watan Bacewarsa:
- Yuni 23, 2023: Engr. Mannir ya tashi daga Katsina zuwa Kaduna
- Anyimasa gani na karshe tsakanin Zaria da Kaduna
Kutaimaka mana wurin yada wannan labarin akan kafofin watsa labarunku.
Mun gode.
Malam Abdullahi Balarabe