An karawa tsohon Shugaban EFCC Magu Matsayin zuwa matsayi mataimakin Babban Sifetan 'Yan Yanda

Hukumar ‘yan sanda ta sanar da karin girma ga tsohon shugaban riko na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu zuwa mukamin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda.



A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin PSC Ikechukwu Ani ta ce Kwamishinonin ‘yan sanda takwas da aka karawa jami’an AIG sune; CP Mustafa Magu Ibrahim wanda shi ne babba a CP cadre kuma wanda bai samu karin girma biyu na karshe bayan ya koma dan sanda; Abraham Egong Ayim; Okunlola Kola Kamaldeen; Andrew Amieengheme; Akeera Mohammed Yous; Celestine Amechi Elumelu; Ngozi Vivian Onadeko da Danladi Bitrus Lalas (Airwing).

Magu ya rike mukaddashin shugaban EFCC daga 2015 zuwa 2020.

Sau biyu majalisar dattawa ta ki tabbatar da nadin nasa.

Daga baya an dakatar da Magu tare da wasu da dama bisa zargin karkatar da kudaden hukumar, zargin da ya sha musantawa.

Kwamitin bincike na shari'a karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara, Mai shari'a Ayo Salami ya shafe sama da watanni uku yana bincike.


Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post