Binciken masana da aka gudanar a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya yi nuni da cewa muggan ɓirɓishin ƙarafe da ke maƙare a cikin tabar shisha ko lofe sun ɗara na taba sigari.
Sinadaran ƙarafen da ba sa jituwa da jikin ɗan Adam, kuma suke da haɗarin janyo kansar huhu da baki da kuma cutukan zuciya da jijiyoyin jini sun haɗar da ɓirɓishin ƙarafen "nickel", "chromium", "zinc" da "copper".
Binciken ya ce kwarkwaron da mashayan ke zuƙar tabar shisha ba shi da ingantacciyar rariyar da zai iya tace ɓirɓishin muggan ƙarafen. Kuma hakan ne ke sanya ɓirɓishin ƙarafen zarcewa zuwa cikin baki, huhu da jijiyoyin jini.
Jagorar binciken, Ayesha Mohammed, wace masaniyar kimiyyar kemistiri ce a jami'ar Sharjar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa. An kuma buga sakamakon binciken a mujallar "Oxford University Press's Journal of Analytical Toxicology".