2023: Za Mu wayar da kan Masu Zabe a kalla miliyan daya Ga Tinubu A jihar Ribas – Abe

Fitaccen dan jam’iyyar APC a jihar Ribas, Sanata Magnus Ngei Abe, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta tattara masu kada kuri’a miliyan daya a jihar domin marawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Ahmed Bola Tinubu baya a zaben 2023.Abe ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da yake jawabi ga dubban ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayansa a filin jirgin sama na Fatakwal, bayan isowarsa daga Abuja.


Jigon na APC ya taka rawar gani a yakin neman zaben da ya kai ga fitowar Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki a babban taron kasa da aka kammala a Abuja.


Ya yi kira ga al’ummar jihar da su hada kai wajen yin rajista domin tallafa wa shirin ‘Project SMA 2023’, da nufin baiwa jama’a damar zabar wanda zai zama gwamnan su a 2023.


Abe ya ce: “Zan je kauyenmu kai tsaye domin yin rajista a matsayin mai goyon bayan Sanata Magnus Ngei Abe. Za mu yi rijistar masu kada kuri’a miliyan daya da za su zabi Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da Sanata Magnus Ngei Abe.


“Zan je kauye ne domin gudanar da aikin SMA 2023. A yayin da zan yi rajista, ina kira ga duk wadanda suka yi rajista a Jihar Ribas, wadanda ke son su samu zabin sanya Gwamnan nasu a Jihar Ribas su yi rajista da ni. ”

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post