Ana yi wa Ciwon Siga take da "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa". Saboda akwai wadataccen siga(gulukos) a cikin jini amma ƙwayoyin halitta, wato "cells", sun gaza samun sigan wanda kuma shi ne makamashin da ƙwayoyin halittar ke ƙonawa domin cigaban rayuwa.
Sinadarin "insulin" wanda matsarmama ke samarwa shi ne ke shigar da sigan daga cikin jini zuwa cikin ƙwayoyin halitta. Wato sinadarin "insulin" shi ne ke daidaita siga a jikin mutum. Idan "insulin" bai yi aikinsa ba, to siga zai hauhawa a cikin jini fiye da ƙima. Wato ga sigan a cikin jini amma "insulin" ya gaza shigar da shi daga cikin jini zuwa cikin ƙwayoyin halitta. Wannan shi ne "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa" kenan!
A taƙaice dai, ciwon siga na afkuwa sakamakon rashi ko ƙarancin "insulin" ko kuma gazawar ƙwayoyin halitta wajen amfani da shi yadda ya kamata a jiki.
Alamomin ciwon siga sun haɗa da:
1. Yawaita fitsari akai-akai, musamman da daddare.
2. Matsananciyar ƙishirwa / shan ruwa fiye da ƙima.
3. Rama / raguwar nauyin jiki
4. Jin matsananciyar yunwa.
5. Ƙan-jiki, wato jinkirin warkewar rauni ko miki a jiki.
6. Saurin harbuwa da ƙwayoyin cutuka, musamman masu haddasa cutukan hanyoyin fitsari.
Tuntuɓi likita da zarar ka fara fuskantar waɗannan alamomi.
SOURCE:
📝 Physiotherapy Hausa