Kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mutane bakwai, ya fitar da sunayen mutane 13 da za su fafata a zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa.
Jaridar LEADERSHIP, ta ruwaito a ranar Alhamis ne kawai cewa kwamitin na shirya jerin sunayen mutane tara domin tantance shugabannin jam’iyyar APC.
Kwamitin karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, John Odigie-Oyegun, ya tabbatar da labarin yayin da yake mika rahotonsa jiya ga shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.
A safiyar Juma’a ne dai aka yi ta cece-kuce game da rashin cancantar wasu ‘yan takarar shugaban kasa biyo bayan gazawar Oyegun, wanda ya yi wa manema labarai karin bayani bayan mika rahoton, ya bayyana sunayen mutane 13 da suka nemi a tantance a cikin jerin sunayen kwamitin nasa.
A cewar daya daga cikin majiyoyin, dukkan masu neman takara 23 da aka tantance an wanke su kuma sun cancanta, amma kwamitin ya ba da shawarar sake fitar da wani jerin sunaye 13.
Wadanda aka ba da shawarar a cikin jerin sun hada da jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan; Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Sauran sun hada da tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu; tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi, da takwaransa na jihar Jigawa, Abubakar Badaru.
Wasu masu neman takarar biyu, tsohon ministan Neja Delta Godswill Akpabio da Mista Tein Jack-Rich, an kuma yi imanin sun shiga jerin sunayen bayan kwamitin ya mika rahotonsa a jiya da yamma