Tinubu da Atiku sun fara neman waɗanda za su mu su mataimaka yayinda INEC ta bada wa'adin bada Sunayen yan takara

 Ɗan takarar Shugaban kasa jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, sun shiga neman mutanen da za su yi musu mataimaka a babbar zaben 2023 me zuwa.



Kakakin ganganmin yakin neman zaben Tinubu, Mr Bayo Onanuga, ya shaidawa manema labarai cewa, ɗan takarar a jam'iyyar APC zai gana da gwamnoni domin tantace mutumin da zai masa mataimaki.

Yayinda Tinubu ke neman mataimaki, shi ma Atiku dan takarar jam'iyyar adawa ya gudanar da tattaunawar sirri da gwamnonin PDP a Abuja a kokarin neman wanda zai masa mataimaki.

Sannan kuma zuwa karshen mako ana saran, Tinubu zai gana da shugabanni jam'iyya, ciki harda sanata Abdullahi Adamu.

A wani cigaba kuma, Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bai wa jam'iyyu wa'adi na karshe da su gabatar da sunayen mutanen da za su yi musu takarar shugaban kasa da mataimakansu.



INEC ta tsayar da 17 ga watan Yuni a matsayin ranar karshe na masu takarar shugaban kasa da mataimaka, da kuma sanatoci da 'yan majalisar tarayya.

Hukumar ta gargadi cewa da misalin 6 na yammacin Juma'a 17 ga watan Yunin, 2022 shafin da ake cike sunayen 'yan takara zai rufe.

Sai dai na 'yan takarar gwamna da 'yan majalisar jihohi, a ranar 15 ga watan Yuli wa'adin zai cika


Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post