Abubuwan da ya kamata duk musulmi a goman Farko Na Zhul Hajj

 Kwanaki goma na farkon Zhul-Hijjah sune ranaku mafi falala a cikin shekara, inda Allah madaukakin sarki ya albarkaci al'ummarsa da damar ninka ladarsu ta hanyar rahamarSa mara iyaka.Babban limamin masallacin Sultan Bello Masjid Kaduna, Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam wanda ya bayyana haka a lokacin hudubar Juma’a ta farko a watan karshe na kalandar Musulunci, ya bukaci al’ummar Musulmi da su sake sadaukar da kansu wajen bautar mahaliccinsu ta hanyar kara ayyuka na gari.

Allah madaukakin sarki wanda ya halicci lokaci ya fifita wasu lokuta fiye da wasu, wasu watanni da ranaku da darare, idan aka yawaita lada a matsayin rahama ga bayinsa.

Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam ya ce kwanaki goma na farkon watan Zhul-Hijja lokaci ne na ibada da ke kawo fa'idodi da dama, kamar samun damar gyara kura-kurai da kuma gyara duk wata kasawa ko wani abu da mutum zai iya samu.

Dangane da haka babban limamin ya bukaci al'ummar musulmi da su fahimci kimar rayuwarsu, su kara bautar Allah da kuma ci gaba da ayyukan alheri har zuwa lokacin mutuwa.

A zaben 2023 da ke tafe a kasar nan, Sheikh Dr. Muhammad Sulaiman Adam ya yi kira ga kowa da kowa da ya tabbatar ya samu katin zabe na dindindin domin ya ba su damar zaben shugabannin da za su tafiyar da al’amuransu.

Baya ga gudanar da ayyukan alheri da dama, babban limamin ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su kara himma wajen gudanar da addu’o’i a tsawon wadannan kwanaki goma domin kasar nan ta fita daga halin da take ciki.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post