Gwamnatin Burtaniya ta kulla yarjejeniya da Najeriya kan batun bakin haure

 Gwamnatin Birtaniya ta sanar cewa ta kulla yarjejeniya a tsakaninta da Najeriya kan kamawa da mayar da bakin haure gida.A wani sako da ta sanya a a kafan sada zumuntar ta na tuwita,  Sakatariyar harkokin cikin gida na Birtaniya, Priti Patel ta ce yarjejeniyar tana matukar muhimmanci da Najeriya za ta sa a samu damar kara fitar da miyagun masu laifi daga kasar.

Ta bayar da sanarwar ne ranar wannan Alhamis din bayan Birtaniyar ta mayar da wasau ‘yan Najeriyar guda 10 gida bisa laifukan da suka danganci shige da fice.

Ba a bar mmutanen sun gana da kowa ba ko ma ‘yan jarida a filin jirgin saman na Lagos a lokacin aka dawo da su.

A farkon watan jiya ne, Kotun kare hakkin dan Adam ta Turai ta haramta tashin jirgin farko da zai kai masu neman mafaka daga Birtaniya zuwa Rwanda.

Shirin da gwamnatin Birtniyar ta ce zai hana masu bi ta tekun Ingila suna shiga kasar.

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post