A daren ranar Talatar nan ne wasu mahara da ba a san ko su wanene ba suka kai farmaki gidan yarin Kuje da ke babban birnin Najerya Abuja, inda bayanai ke cewa daga cikin fursunonin sun tsere.
A zantawar da BBC tayi da wani mutum ya bayyana cewa maharan sun yi ta kabbara tare da harba rokoki a cikin gidan yarin.
A cewar wani da lamarin ya faru a gabansa, 'yan bindigar sun ci karfin jami'an tsaro inda aka yi ta musayar wuta.