Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin ministoci bakwai da Majalisar Dokokin ƙasar ta tatance.
Ya rantsar da su ne gabanin taron Majalisar Zartarwar ƙasar na mako-mako Larabar nan.
Ministocin ta aka rantsar sun hada da Umana Okon Umana daga jihar Akwa-Ibom a matsayin ministan Naija Delta, da Ikoh Henry Ikechukwu daga jihar Abia a matsayin ƙaramin ministan kimiyya da fasaha, da Umar Ibrahim El-Yakubu daga Kano a matsayin ƙaramin ministan ayyuka da gidaje.
Sauran kuma su ne Goodluck Nanah Opiah daga jihar Imo, wanda ya rabauta da kujerar ƙaramin ministan ilimi, da Ekumankama Joseph Nkamah daga Ebonyi, a matsayin ƙaramin ministan lafiya, da Odum Udi daga Rivers a matsayin ƙaramin ministan muhalli, da Ademola Adewole Adegoroye daga Ondo a matsayin ƙaramin ministan suuri.
Shugaban ya taya su murna, tare da buƙatar su yi aiki tuƙuru don ciyar da ƙasar gaba.