Mun mayar da ikon gudanarwar NNPC hannun yan Kasuwa - Buhari

 Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar sabon kamfanin mai na kasar wanda aka canza wa fasali, wanda a yanzu haka kamfanin na NNPC ya koma wani kamfanin kasuwanci mai zaman kansa.

Buhari (Presidency - Photo credit)


An gudanar da wani kwarya-kwaryar biki a Abuja babban birnin kasar yayin kaddamarwar .

Shugaba Buhari ya godewa mahartar taron, wanda ya kira shi da ''mai dimbin tarihi''.

A jawabin da ya gabatar a wajen taron, ya ce an mayar da ikon gudanar da kamfanin ga 'yan kasuwa ne, saboda inganta shi, don samar wa kasar makamashin da take bukata.

Ya kara da cewa ''daga yanzu kamfanin NNPC ya koma karkashin gudanarwar 'yan kasuwa, inda zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa na fadin duniya, domin cigaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan dari biyu (200) tare da habaka fannin makashi a fadin duniya''.

''A yanzu haka an dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen makashin da take bukata domin samun habakar tattalin arzikin ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar makashin''. in ji Shugaban Buhari.


Kuna ganin wannan zai haifar da d'a mai ido?

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post