Lantarki: Muhimmancin sana'a ga matasa - Mubarak Ibrahim

 Sana'ar hannu dai yana da muhimmanci ga matasa Domin akwai sana'o'in da ba haramun ba ne a Addini, Sana'a ga matasa ta zama wajibi bisa la'akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau.

Mubarak Ibrahim

Hakika ba karamin tashin  hankali ba ne, a ce an wayi gari matashi ba ya da takaimaiman wurin da zai je domin neman na kansa. Rashin  hakan ne ke sa dimbin  matasa fadaawa cikin miyagun ayyuka irin su; shaye-shaye, sace-sace a unguwa da shiga bangar siyasa da sauransu.

A yanzu kashi tamanin cikin dari na sana'o'in mafi yawanci matasa ke yi yana amfani da wutan lantarki ne kamar; Dinki, Saloon, Aski, niqa, walda hatta masu shayi yanzu suna aiki da wutar lantarki domin gudanar da sana'o'insu. Duba da yanzu man fetur yayi tsada, iskar gas da sauransu.

Matasa musamman a karamar hukumar Lere suna bukatar wutar lantarki da abubuwan more rayuwa domin samun ingantacciyar rayuwa a matsayinsu na many an gobe. 

A dalilin haka ne Shugaban matasan karamar hukumar Lere, Mubarak Ibrahim ya sake yin kira ga gwamnati a ko wani mataki da su taimaka don ganin an shawo kan matsalar wutar lantarki da karamar hukumar Lere ke fama da ita na tsawon lokaci.

A cewarsa, idan yau matashi ya wayi gari yana da inda zai je ya gudanar da sana'arsa, tabbas za'a sami raguwar shaye-share, da sace-sace a tsakanin matasa kuma za a rage ma gwamnati nauyi sosai.

"Ba zan gaji da kira da gwamnati ba don ganin an shawo kan matsalar wutar lantarki a Karamar hukumar don jin dadin matasa da sauran jama'a." Inji Mubarak.

Ya kara da cewa, "babban burina shine naga matasan karamar hukumar Lere suna zaune lafiya da jin dadi, kada kasance a cikin a in da zai bata rayuwarsu na gobe. Kada su yarda wani Dan siyasa yayi amfani dasu wajen tayar da hankalin al'umma."

Said yayi kira ga gwamnati da ta taimakawa matasa da abubuwan da zasu gudanar da sana'ar.

Har wa yau yayi kira ga matasa da kada su raina sana'a komai kankantarsa, domin da kadan ake farawa har a zo wani matakin da said kayi mamaki.

Allah ya sa mu dace. 

Me karatu ya kake ganin wannan zai inganta rayuwarka a matsayinka na matashi?

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post