Kungiyar ma’aikatan sufurin jiragen sama ta Najeriya (ANAP), ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi ko kuma za su rufe bangaren sufurin jiragen sama tare da hadin kan malaman jami’o’in.
A wata sanarwa da babban sakataren kungiyar ANAP, Kwamared Abdulrasaq Saidu ya fitar, ya bukaci shugaban kasa Mohammadu Buhari ya kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba.
ANAP ta lura cewa ci gaba da zama a gida da daliban manyan makarantu ke yi ya kara haifar da munanan dabi’u a kasar nan yayin da dalibai ke yin wasu abubuwa marasa dadi da ke iya lalata makomarsu.
ANAP ta yi barazanar cewa za su shiga yajin aikin na hadin gwiwa ta hanyar rufe bangaren sufurin jiragen sama idan gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa na magance bukatun ASUU ba.
Kungiyar ta lura cewa yajin aikin na sama da watanni hudu ya sa harkar ilimi ba’a ta kuma maida shi abin dariya a gaban duniya.
Kungiyar ta ANAP bayyana cewa ASUU, NASU, SAUTHRIAI, NAAT sun shafe sama da watanni hudu suna yajin aikin saboda gazawar gwamnati na sake kulla yarjejeniyar 2009 da ASUU, rashin cika sharuddan da aka cimma a watan Mayun 2022. tare da ASUU, da gazawar gwamnati ta saba mutunta yarjejeniyoyin ciniki na gama gari da son ransu da kungiyoyin kwadago.
ANAP ta bayyana cewa ba wai daliban ne kawai ke shan wahala ba, har ma iyaye da sauran al’umma, inda ta kara da cewa tabarbarewar tattalin arziki ya kuma shafi kowane gida a kasar nan.