Menene Olsa, Alamominta da hanyoyin kariya daga cutar.

 PEPTIC ULCER DISEASES 

Menene Ciwon ulcer.

Ciwon olsa Ciwo ne da ke tasowa akan rufin makogoro, ciki ko hanji.

Ulcer na faruwa lokacin da acid na ciki ya lalata rufin tsarin narkewar abinci.

Ciwon olsa ciwone wacce ta zama gama gari kuma tana daya daga cikin manyan cututtuka da suke damun al'ummah musamman a kasar Najeriya.

Ulcer


Me yake kawo ciwon Olsa

 Kwayar cutar bakteriya mai suna H- pylori shi yake kawo ciwon Olsa , Haka kuma yawan shan maganin dauke  ciwo kamar su  Aspirin, Shan taba (sigari) da kuma shan Giya suna taimaka sosai wajen kawo ciwon Olsa.


Hanyoyin Daukar olsa

Mutum yakan iya daukan wannan koyar cutar ta hanyar musyar yawu (saliva) ko lokocin kiss.

Mutum yakan iya daukan wannan kwayar bakteriyan  ta hanyar ruwan sha da kuma abinci .

Idan ruwan sha ko abinci ya gurbanta da bayan gida ko fitsarin mai ciwon, wanda hakan yana faruwa ne ta hanyoyi da yawa.


Peptic Ulcer Disease : (Gyembon Ciki) Wannan shine sunan ulcern ciki gabaki daya.

Ita Peptic ulcer ( gyembon ciki ko ciwon ulcer ) ta kasu kashi uku:


1. Gastric Ulcer (Gyenbo wadda take kama Fatar ciki ciki)

2- Duedenal Ulcer (Gyenbo wanda take kama hanji)

3- Esophagus Ulcer  (Gyenbon maqogwaro)


Ciwon Olsa tana zuwa da alamomi dayawa gasu: 

1. Konawar zuciya

2. Ciwon Cikin

3. Rashin cin abinci

4. Tashin Zuciya 

5. Amai

6. Ciwo har a gadon baya

7. Kashi da jini  ko bakin kashi

8. kumburin ciki

9. Daukewar numfashi.


Meyasa ciwon olsa ba'a warkewa da wuri ?

Ba wai Ba'a warkewa bane , ana warkewa daga cutar Olsa ko wacce iri amma abinda yake faruwa shine:


1. Rashin shan magani yadda yakamata, yau anwayi gari shan magani barkatai yazama ruwa dare a najeriya, mafi yawa kwayoyin cutar ansaba musu da wannan maganin har yazama cutar ta saba da maganin ta yadda ko ansha maganin bazai ma cutar komai ba.

2. Za kaga mutum ana bashi maganin wata daya ko sati biyu a ranan da yafara shan maganin daga yaji sauki shikenan ya rabu da maganin sai dai lokocin da alamomin cutar yasake zuwa zaici gaba da shan maganin. 

3. Misali ace kwayar cutar ana samunshi daga gurbaceccen ruwa , To ana shan magani kuma ana cigaba da shanceccen ruwan kaga babu maganar warkewa.

4. Rashin bin ka'idodin likita ya gaba gaba wajen hana warkewan wannan ciwo na Olsa.

5. Shan magunguna barkatai ba tareda Izinin likita ba musamman magungunan olsa da sunan zai warkar maka da olsa, da kuma amfani da magunguna na gargajiya wanda ba'asan kansu ba wannan ma na haifar da rashin warkewar olsa.


Shawara ga masu dauke cutar olsa:

1. A kauracewa wadannan Abinci:

- Abinci mai yaji

- Abinci mai daci

- Abinci Mai sami

- Abinci masu Gas

- Abinci masu dauke da Acid kakar tumaturi.

2. A daina amfani da hayaki ko wacce iri ko tabar sigari, wiwi ko shisha sabida suna daga cikin Abubuwan da suke haddasa olsa Kuma suna sananta olsa.

3.  Adaina amfani magungunan dauke ciwo irinsu Aspirin, Ibuprofen, cataflam, Naproxen, Feldene, da sauransu.

4. A rage shan giya domin yawan shan giya yana daya  daga  cikin abubuwan  da suke kawo olsa Kuma suke tsananta ciwon Olsa.

5. A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da ake da kwawato akai kafin amfani.

6. A yawaita amfani da kayan lambu musamman kabeji (cabbage) yana taimaka wajen dakile ciwon olsa.

7. Sai Kuma zuwa ganin likita domin Tabbatar da cutar da Kuma bada magani.

Ya ka ke shan maganin olsa?

Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post