Wani Malamin lissafin Mr. Isah ya yi ma wata daliba Hauwa'u Salihu 'yar shekara 15 dalibar aji biyu na babbar Sakandire watau SS2 a makarantar Rochas Foundation da ke Zaria, dukan da har yayi sanadiyyar samun matsala a kashin bayarta Malam Isa ya yi wa Hauwa’u bulala da babbar sanda (Gora) a baya wanda hakan ya yi sanadin lalacewar Kashin bayanta.

 Jaridar Harvest Nig ta tattaro cewa, “Halin da ya haifar da mummunanan rauni, wanda yanzu haka tana jinya da ta yi wanda iyayenta suka kashe kimanin naira miliyan daya, wani kwararrun likitoci a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABUTH SHIKA) ya gano cewa Hauwa’u ta sami matsala a kashin bayanta wanda yake hadarin lalacewa sakamakon dukan da malamin lissafin ya yi mata.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugabar makarantar Malama Rabi Ibrahim ta musanta faruwar lamarin yayin da a matakin farko ta bayar da gudunmawar naira dubu goma ga iyayen Hauwa'u a lokacin da ta kai ziyara.