Ilimi: Al'ummar Kayarda a Karamar Hukumar Lere sun bukaci gwamnati da gyara musu makarantar sakandire da ke bukatar agajin gaggawa

Ilimi dai abune mai muhimmacin gaske ga rayuwar mutanen dake cikin ko wacce irin al'umma, Wanda da ilimi ne ake tafiyar da komai a rayuwar, rashin ilimi kuwa yana haifar da gagarumin Marsala cikin Al'umma

Kayarda


Shugaban Matasan Karamar Hukumar (LELOGYP), Kwamared Mubarak Ibrahim yayi kira ga shuwagabanni kan halin da  Makarantar Kayarda, wanda  take cikin garin Kayarda, a Gundumar Kayarda dake Karamar Hukumar Lere

Yayi kiran ne a wata budaddiyar wasika da ya aikewa wakilin The Voice Online Nigeria, a Kaduna.

Ya bayyana cewa halin da government Secondary school Kayarda take ciki, a yanzu haka bama maganar kujerun Makarantar ake yi ba, hatta gine ginen Makarantar yana cikin matsnancin hali na rugujewa, sakamakon rashin kulawa Gwamnati tayi alkawari kala, Kala, ta bakin 'yan majalisun mu na Dattijai da na Walkilan tarayya, dana Jaha amma haryanzu babu abinda ya canza. 


“Dan haka zamuyi amfani da damar da muke dashi muyi Kira ga gwamnati da ta duba halin da wannan makaranta take ciki domin ceto yan uwan mu 'Dalibai, sabida daga Malamai har 'Dalibai baza su samu, nutsuwa ba matukar akace akwai tsoro azukatan su, wani irin tsoro nake nufi?  shine, zafin Rana, tsoron dukan Ruwa/ko rushewar ginin makaranta. Rashin kujerun zama masu kyau, duk cikin abinda na lissafa sune abinda wannan makaranta ke bukata.” 



“Sabida haka idan akayi la'akari da abubuwan dana lissafa wannan makaranta tana bukatar dauki na gaggawa.” Inji Mubarak. 

Ya kara da cewa, “Maigirma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufa'I, Sanatan mu na shiya ta dayar jihar Kaduna, Suleiman Abdu Kwari, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltan Karamar Hukumar Lere, Hon. Ahmed Munir, Shugaban Karamar Hukumar Lere, Hon. Abubakar Buba, 'Yan Majalisun mu na Jiha na Lere ta Gabas da ta Yamma, Hon. Abdullahi Idris Marafa da Hon. Bashir Idris Gatari, Amatsayin mu na kungiyar matasa mun isar da koken al'umar Kayarda wanda suma 'yan asalin Karamar Hukumar Lere ne, a duba wannan matsala domin kawo karshen ta.”



Sannan zamu chigaba da binciko irin wadannan matsalolin domin kai koke wajen da ya dace dan ganin anyi Abinda ya kamata. 


A nashi jawabin, Wani Mazaunin Kayarda Usman Isa Ladan Bamauje, ya bayyana hakan a shafinsa na saka zumunta, yace "Samun muhallin gudanar da ingantattun kayan koyar da karatu yana da muhimmacin sosai ga dalibai domin hakan zai sa Caliban su sami cikakken natsuwa da har za su fahimci darasin da ake koya masu."


Ya kara da cewa "Wannan makarantar kauyuka da dama anan suke karatun su kamar: Galma, Unguwan sarki, Kwana, Kamfa, Kakun kurama, Tashan Kayarda, Goron dutse  dama sauran kauyuka da damage wanda a wannan makarantar suke karatu."



"Amfanin Ilmi basai an lissafa ba mun sani kuma bamu zo duniya domin mu huta ba, muyi aiki tukuru domin mubarwa masu zuwa su cigaba suma." Inji shi.


Masu karatu Wani irin k uke dashi?

Zaku iya kawo koken ku kuma domin isar da ita inda ya dace.


Post a Comment

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post