Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki mutum miliyan ɗaya don gudanar daaikin ƙidaya

 Hukumar kidaya ta Najeriya wato NPC ta ce gwamnatin tarayya za ta ɗauki ƴan yan Najeriya miliyan daya aiki domin gudanar da kidayar jama’a da zai gudana a shekarar 2023.



Hukumar ta ba da tabbacin cewa, an samar da kyakkyawan tsarin yadda za'a gudanar da ƙidayar don hana ƴan siyasa da masu mummunar aniya yin amfani da wannan dama.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa kwamishinan hukumar mai kula da jihar Ekiti Mista Deji Ajayi ya bayyana hakan a Ado Ekiti, jiya, a wani taron manema labarai kan kidayar gwaji da za a gudanar a jihar.

A yayin da yake bayyana mahimmancin kidayar jama’a ga gina kasa, Ajayi ya ce kungiyoyi masu zaman kansu za su yi amfani da kididdigar yawan jama’a wajen tsara yadda za a dauki matasan Najeriya aiki ta hanyar sanin adadin yawan jama’a.

Ya kara da cewa, Gwamnati za ta kuma yi amfani da irin wannan kididdiga don tsara yadda za a taimaka wa matasanmu, da dalibanmu da kuma biyan bukatun lsauran jama'ar ƙasa.

1 Comments

You can ask a question about something you don't understand about our website via comment or you can send us a story through this email thevoice24ng@gmail.com. You can contact us Directly using Contact Us page.

Previous Post Next Post